Tsakanin malami da manomi, wa ya fi amfani ga al’umma?2
Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane […]
Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Manomi ya fi malami alfanu ga jama’a – Nafisa Ahmad
Nafisa Ahmad: “Gaskiya manomi ya fi malami, domin sai manomi ya yi noma sannan malami zai sami abincin da zai ci kuma sai al’umma sun ci abinci sannan za su sami ikon zuwa neman ilimi. Saboda haka idan babu abinci babu yadda za a sami ilimi da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ingantacciyar lafiya a tsakanin al’ummar duniya baki daya.”