Tsakanin malami da manomi, wa ya fi amfani ga al’umma?6
Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane […]
Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Manomi ya fi amfani – Idris Inuwa
Idris Inuwa: “Ba abin da ya fi abinci tasiri, don sai an koshi koyo da koyarwar da kuma wasu lamurran za su samu muhalli. Haka in dai da koshin za a samu damar yin tafiya mai nisa don nemo ilimin a zo a karantar a kuma tafiyar da harkokin addinin. Samun manoma a al’umma zai ba da dammar samar da malaman addini da yawa, su yo caa zuwa gari don samun abinci da kuma ba da karatu. Da zarar an ce wuri ba abinci to koda da malaman, da sannu za su yi hijira zuwa inda za su samu abun lasawa. A haka nake ganin manomi ya fi malamin addini tasiri.”