Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon amana?

Allah Ya halitta dan Adam zuwa jinsuna biyu, mace da namiji kuma su ne abokan huldar juna a rayuwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan jinsuna biyu, wa ya fi rikon amana a cikin mu’amalar rayuwa? Wakilanmu sun tuntubi mabambantan mutane domin jin ra’ayoyinsu kuma ga abin da suke cewa: Mata sun […]

Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon amana?
Tsakanin maza da mata, wa ya fi rikon amana?

Allah Ya halitta dan Adam zuwa jinsuna biyu, mace da namiji kuma su ne abokan huldar juna a rayuwa. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan jinsuna biyu, wa ya fi rikon amana a cikin mu’amalar rayuwa? Wakilanmu sun tuntubi mabambantan mutane domin jin ra’ayoyinsu kuma ga abin da suke cewa:

Mata sun fi rikon amana – Hajiya Binta Bazamfara

Musa Kutama, a Kalaba

Hajiya Binta Bazamfara: “Maza suna da rikon amana amma fa mata sun fi, domin mace tana zaune da namiji idan sun haihu da shi koma ba a haihu ba; duk halin da ya shiga na rayuwa mace ba za ta ki namijin ba. Amma wani namijin macen na shiga wani hali sai ka ga yana neman korar ta ko sake wani auren. Ka ga saboda alkawari mace ko yara nawa take da su babu wata wuya da za ta sanya ta tsallake ta bar su amma mazan fa? Rashin lafiya za ta iya kama namiji mace ta yi tsayin daka, ta yi jinya har ya warke amma wani namijin sai ya tarkata macen ya ce ta koma gidansu. Ka ga babu amana ke nan, don haka mata sun fi maza rike amana.”

Mata sun dara maza amana – Nasiru Anas

Musa Kutama, a Kalaba

Nasiru Anas bare-bare: “A gaskiya mata sun fi maza rikon amana, domin idan mace tana soyayya da mutum kafin ma a yi aure za ka iske babu wata matsala da kalubale da ba ta fuskanta, don dai a raba ta da mutum amma saboda amana da rike alkawari sai ka ga mace ta jure. Amma namiji kuwa ko yaya ya ji wahala ko matsi na rawuya sai ka ga yana neman ya yarfar da macen. Su mata suna da tausayi da juriya kan duk wani kalubale na rayuwa game da namiji. Na taba shiga tasku na soyayya wadda mace ta cika min alkawari amma a yanzu idan a ce namiji ne ya yi alkawari ko amana sai namijin gaske ne zai rike wannan amana tsakaninsa da mace.”

Maza sun fi rikon amana – Zubairu Sarki

danladi Ibrahim, a Minna

Zubairu Sarki Bello: “A ra’ayina, maza sun fi rikon amana. Dalilina kuwa shi ne, idan ka hadu da wanda yake son mace tsakani da Allah, yana nunawa ne kiri-kiri. Da wuya ka ga ya nemi wata. Ita kuwa mace ko da an yi aure ba ta nuna wasu dabi’unta sai bayan ta haihu sai ta fito da wasu halayenta wadanda tun farko ta boye. Wannan ya kan kai ga cin amana. Wasu daga cikin matan ba su da juriya da hakuri game da kwadayinsu na son abin duniya ta kowane hali. Wannan dabi’ar ce kan sa suna sake-sake a zukatansu. Koda sun yi aure, a zahiri suna gidanka, zuciyarsu tana can inda za su samu abin da suke so ba tare da la’akari da cewa sun yi aure ba.

Mata sun fi maza amana – Priscilla Dennis

danladi Ibrahim, a Minna

Priscilla Dennis: “Wannan al’amarin ba karamar magana ba ce. A ra’ayina mata suna kokari, kusan ma in ce su suka fi yawa idan aka yi maganar rikon amana. A nan, ba wai ina nufin cewa maza ba su da rikon amana ba ne, ana samun matan da ke cin amana, sai dai ba su kai maza ba. Akasarin laifukan da ake ganin cewa mata suna cin amana a kansu, kura-kurai ne wadanda mu ’yan Adam kan tafka daga lokaci zuwa lokaci. Muddin aka samu mace ta aikata ba za a yi mata uzuri ba sai a dauki matakai iri-iri a kanta ciki har da tsangwama. Shi kuwa namiji yana ganin cin amanar matarsa ta kowace fuska ’yancinsa ne, musamman idan ita take sonsa shi kuwa ba ya sonta har ta kai ga aure.”

Mata sun fi rikon amana – Yahanasu Sani

Lubabatu I. Garba, a Kano

Yahanasu Sani: “A ra’ayina, mata sun fi maza rikon amana, domin idan kika dauki harkar rashin lafiya. Mace takan iya zama da mijinta a kowane hali ya kasance kuma za ta zauna ta yi jinyarsa duk tsawon lokacin da zai dauka ba tare da nuna gajiyawa ba ko neman rabuwa ba. Amma idan mace ce ta sami rashin lafiya sai ka ga mijin ya tattara ta ya mayar da ita gidansu, wai a yi jinyarta a can. Idan kuma ya ga ta dauki wani lokaci ba ta warke ba sai dai ya yi wani auren abinsa.”

Mata suke da rikon amana- Ibrahim Hamisu

Lubabatu I. Garba, a Kano

Ibrahim Hamisu Kabara: Babu shakka mata sun fi maza rikon amana a zamantakewar aure. Dalilina shi ne, na sha ganin inda miji yake tafiya ya bar mace da ’ya’ya ba tare da sanin inda yake ba amma haka matar nan za ta zauna tana jiran zuwan mijin nan nata har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Wasu matan ma ba za su taba yarda su yi wani auren ba koda kuwa kotu ta amince mata da yin hakan.”