Tsakanin maza da mata Wa ya fi taurin bashi?
Masu iya magana suna cewa bashi hanji ne, akwai shi a cikin kowa. Abin tambaya a filinmu na wannan makon shi ne, shin tsakanin jinsin maza da na mata, wa ya fi taurin bashi? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma daban-daban: Maza sun fi mata taurin bashi – Salihu Abubakar Hamza […]
Masu iya magana suna cewa bashi hanji ne, akwai shi a cikin kowa. Abin tambaya a filinmu na wannan makon shi ne, shin tsakanin jinsin maza da na mata, wa ya fi taurin bashi? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga bakunan al’umma daban-daban:
Maza sun fi mata taurin bashi – Salihu Abubakar
Hamza Aliyu, a Bauchi
Alhaji Salihu Ahmed Abubakar: “Abinda zan fada game da wannan tambaya shi ne, gaskiyar magana maza sun fi mata taurin bashi, domin akwai dimbin mutane wadanda suke karbar bashi ba da niyyar biya ba kuma wasu suna da kudin da za su biya amma saboda mugunta da son zuciya sai su ki biya a kan lokaci. Bayan haka, sama da kasha 85 cikin 100 na wadanda suka fi cin bashi a duniya maza ne sannan kuma akwai masu karbar bashi da niyyar gurgunta mutum. Muna fatar Allah Ya shiryi masu taurin bashi a duk inda suke a fadin duniya, domin cin bashi ba da niyyar biya ba fitina ce babba a tsakanin wannan al’umma. Ina ba da shawara ga masu taurin bashi da a fahimci cewa Allah ba Ya yafe hakkin wani sai mai hakkin ya yafe sannan kuma duk wanda ya ki biyan bashi da gangan zai biyar ranar gobe kimaya da ayyukansa masu kyau.”
Mata sun fi maza taurin bashi – A’ishatu Hamza
Hamza Aliyu, a Bauchi
Hajiya A’ishatu Khamis Hamza: “Fahimtata game da wannan muhawara shi ne, gaskiyar magana mata sun fi maza taurin bashi. Akwai wasu daga cikin maza wadanda sukan karbi bashi amma da zarar sun samu kudi za su yi iya bakin kokarinsu wajen biya, domin Hausawa sun ce don tuwon gobe ake wanke tukunya. Akwai dimbin mata da suka ci bashi a wajena domin ina sayar da yadin hijabi na mata amma matan da nake bi bashi sun fi maza yawa, akwai wadanda suna da halin da za su biya amma saboda wasu dalilai sun ki biya kuma kowa ya san cewa suna da kudin a aljihunsu.
“Don haka duk inda ka kewaya a Najeriya, za ka samu cewa mata sun fi maza taurin bashi, domin kusan dukkan abubuwan mata yana gudana ne a kan bashi. Bashin da ya fi kowanne wahalar fita a wannan lokaci shi ne kananan kudade kamar dubu biyu da makamantansu. Sannan kuma ina ba da shawari ga al’umma duk wanda ya karbi bashi da ya yi iya bakin kokarinsa wajen biya domin akwai ranar hisabi.”
Taurin bashi sai mata – Hajiya Suwaiba
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
Hajiya Suwaiba Bala Haruna: “Ra’ayina game da wannan batu shi ne, mata sun fi maza taurin bashi duk da kasancewata mace na tabbata mata sun fi taurin bashi. Mace takan je wurin mace ta karbi bashi girma da arziki amma daga baya sai an ji tsanakinsu saboda saba alkawarin biyan bashin. Namiji idan ya karbi bashin zai yi kokarin ya biya ka don ba ya son jama’a ma su san abin da ake ciki saboda haka zai yi kokarin ganin ya biya ba tare da asirinsa ya tonu ba, amma ita mace saboda takamar ita mace ce, da yawa sai ta ki biya saboda ta san babu abin da zai same ta, musamman ma idan ta karbi kudin ne daga wajen namiji. Ni kaina akwai wacce na taba ba bashi amma har yanzu ba ta gama biya na ba, hasalima sai da hukuma ta shiga tsakaninmu.”
Mata sun fi maza taurin bashi – dayyabu Bello
Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna
dayyabu Bello danfulani: “Ni dan kasuwa ne mai sayar da kayan tireda. Ra’ayina game da wanda ya fi taurin bashi a tsakanin maza da mata shi ne, mace ta fi namiji taurin bashi. Saboda idan ka duba da yawa daga cikin mata ba su aiki ko kuma wata sana’ar da za su yi, idan suka karbi bashi su biya. Hasalima, da wuya ka ga mace ta biya bashi a kan lokaci, don tana tinkahon cewa ita mace ce ba za a rika takura mata kamar yadda ake takura wa maza ba. Ni da matata duk muna sana’a amma mata ne suka fi karbar bashi sannan ba su biya a kan lokaci. Amma namiji ko da ya karbi bashi a wajenka a wasu lokuta idan bai biya ba, yakan same ka ya rika bayar da hakuri da kuma uzuri, amma mata wata ma sai dai kawai ta murtuke maka fuska, idan kun hadu wai don kada ka tambaye ta bashin da kake bin ta. Ban ce ba a samu a wajen maza ba, amma na matan ya fi yawa.”
Mata sun fi taurin bashi – Hajiya Amina
Halima A. Musa, a Abuja
Hajiya Amina Muhammad Abuja: “Mu ’yan kasuwa kin san mun fi kowa sanin sirrin mutane. Kina iya sayar wa mata da maza kaya, sai ki ga namijin ya biya mace ta yi kememe, kamar ba bashi a kanta, ta yi kwalliya kan bashi. Abin mamaki, za ki ga mace na da dubu goma amma za ta ci bashin dubu dari, sannan kuma idan ta samu dubu darin; maimakon ta biya sai dai ta kara cin wani bashin. A gaskiya mata sun fi taurin bashi.”
Maza sun fi taurin bashi – Muntari TBO
Halima A. Musa, a Abuja
Muntari Tbo Abuja: “Gaskiya maza sun fi taurin bashi. Kin ga mace Allah Ya yi ta mai tausayi ce, idan mace tana da kudin nan, in dai ba jaraba ta addabe ta ba, kin san akwai wasu abubuwa da ke sa mata su tafi neman bokaye, ta kasa biya. Namiji in ya yi wani rashin imani kan bashi, za ki ga namiji ana bin shi bashi, sai ya je Hajji da Umura, ya manta da biya. A zahiri maza sun fi taurin bashi.”