Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako?
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Rediyo ya fi jarida muhimmanci – Maikudi AuduMaikudi Audu Yola: “Rediyo ya fi […]
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:
Rediyo ya fi jarida muhimmanci
– Maikudi Audu
Maikudi Audu Yola: “Rediyo ya fi jarida isar da sako domin jarida ba kowa ne ya iya karanta ta ba. Amma rediyo ga sji nan a hannun mutane a cikin birane da kauyuka na kasashen duniya daban-daban suna sauraron labarai da dumi-duminsu. Shi ma wanda bai iya karatu ba yana sauraron rediyo. Saboda haka nake ganin rediyo ya fi jarida tasirin isar da sako ga jama’a.”