Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 1

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Rediyo ya fi tasiri – Aminu MuhammadAminu Muhammed Harande Sabaru: “Ina ganin rediyo […]

Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 1
Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 1

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:

Rediyo ya fi tasiri – Aminu Muhammad
Aminu Muhammed Harande Sabaru: “Ina ganin rediyo ya fi jarida saurin isar da sako ga jama’a. Mutanen da suke zaune a kauyuka da birane suna samun saukin sauraro a kowane lokaci suka bude rediyo. Ita kuwa jarida, ba safai ake samun ta a wasu wurare ba amma za ka ga mutane da rediyo a hannayensu a irin wadannan wurare kuma sakon jarida ya tsaya ne kawai ga mutanen da suka iya karanta ta. Sai dai kuma jarida tana da amfanin isar da sako mai tsawo fiye da rediyo kuma za ka ajiye ta na tsawon lokaci a tare da kai.”