Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 2
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Rediyo ya fi tasiri – Shehu UmarShehu Umar Gusau: “Ni a rayina, rediyo […]
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:
Rediyo ya fi tasiri – Shehu Umar
Shehu Umar Gusau: “Ni a rayina, rediyo ya fi jarida isar da sako saboda ita jarida sai wanda ya yi karatu zai iya amfani da ita kuma babu yadda za a yi mutumin kauye ya sami duk wani sakon da ake so ya samu cikin lokaci komai muhimmancinsa, in dai ta hanyar jarida ne ake so ya sami sakon. Don haka rediyo ya fi jarida isar da sako ko wayar da kan mutane ko mu ce jama’a”