Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 3

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Rediyo ya fi jarida tasiri – Habibu YahayaHabibu Yahaya Gusau: “Ni dai ra’ayina […]

Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 3
Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 3

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:

Rediyo ya fi jarida tasiri – Habibu Yahaya
Habibu Yahaya Gusau: “Ni dai ra’ayina shi ne, idan isar da sako ne ko wayar da kai, rediyo ya fi jarida; domin ita jarida sai wanda ya yi karatu zai iya karantawa ko ya fahimce ta, domin ko mai karatun sai ya kai shekaru bakwai zuwa sama sannan amma shi Rediyo ko wanda bai yi karatu ba, in dai yana jin magana ba kurma ba ne, zai ji kuma zai fahimta. Don haka duk sakon da ake so a isar ga mutane, musamman ma a ce ’yan kauye kuma cikin gaggawa, to rediyo ya fi sauri da wayar da kai cikin sauki.”