Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 4

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Jarida ta fi tasiri – Muhammad SanusiMuhammad Sanusi Umar: “Ra’ayina game da wannan […]

Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 4
Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 4

Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:

Jarida ta fi tasiri – Muhammad Sanusi
Muhammad Sanusi Umar: “Ra’ayina game da wannan batun ya karkata a kan jarida, ta fi isar da sako da kuma wayar wa jama’a kai fiye da yadda kake tsammani. Dalilaina sun hada da, na farko dai ita jarida ana amfani da kalmomi masu sauki wurin gina jimlolin da mutanen da suke karatu za su fahimta cikin sauki. Sannan ita jarida kana iya ajiye ta domin kafa hujja game da duk abin da ake gardama game da wani al’amari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Bayan haka, mutane na iya bitar jaridun da suka ga labaran da suka rasa koda na watanni nawa ne, sabanin radiyon da a duk lokacin da ka yi asarar sauraron duk wani labara ko shirye-shirye, magana ta kare, don kuwa ba kowa zai iya sayaen wayar da zai iya shiga yanar gizo don sauraron labarai da shirye-shiryen da yake sha’awa ba.”