Tsakanin Rediyo da Jarida, wanne ya fi tasiri wajen fadakarwa da aika sako? 5
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Rediyo ya fi tasiri – Yahaya YusufYahaya Alhaji Yusuf: “Ra’ayina game da wannan […]
Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:
Rediyo ya fi tasiri – Yahaya Yusuf
Yahaya Alhaji Yusuf: “Ra’ayina game da wannan batun shi ne, radiyo ya fi isar da sako ga jama’a fiye da yadda kake tsammani. Dalilaina sun hada da cewa, jama’a musamman mazauna shiyyar Arewacin kasar nan sun fi mu’amala da radiyo don kuwa suna sauraronsa akalla sau uku a rana; inda suke sauraron labarai da al’amuran yau da kullum a harshe mai sauki, sabanin jaridar da ba kowa ya iya karatunta ba. Bayan haka ma jaridun ba su isa ko’ina balle a same su a karanta a lokacin da ake bukata. Kafin jarida ta iso wurinka ma labarin da kake bukata ya tsufa. Ana iya sauraron shirye-shirye ta yanar gizo. A nan mutum yana iya amfani da wayar hannu wadda aka yi wa tanadin haka, ko kuma ta na’urar kwamfuta kowace iri.”