Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma?
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane: Rediyo ya fi […]
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:
Rediyo ya fi muhimmanci
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Malam Saleh Bakwaro Damaturu: “A ganina Rediyo shi ya fi muhimmanci ga al’umma fiye da Waya, domin kuwa kowane lungu ka je za ka tarar da Rediyo. Kuma a gaskiya akan samu labarai ne da dumi-duminsu fiye da waya, ka ga ashe Rediyo hanyar sadarwa ce da ta fi kowce hanyar sadarwa kusanci ga al’umma; kasancewar da wuya ka je gida ba ka same shi ba. Don haka nake ganin Rediyo shi ya fi matukar muhimmanci ga al’umma fiye da Waya, wacce ba kowa ne kan iya mallakar ta ba.”