Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1

Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane: Matukar muhimmanci sai […]

Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1
Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1

Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:

Matukar muhimmanci sai Rediyo – Ali Sarki

Alhaji Ali Sarkin Baburawan Potiskum: “A ganina Rediyo shi ya fi matukar muhimmanci ga al’umma fiye da Waya, don waya kan amfanar da mai ita ne kawai. Alal hakika ma, ai in ana batun Rediyo dangane da amfaninsa ga al’umma babu hadinsa da waya, don ita waya ai ba kowane mutum ne ma kan iya mallakar ta ba kuma ko da mutum ya mallake ta ma ai shi kadai za ta fi amfana. Duk da cewa kusan dukkan abubuwa da yawa ma akan iya samun su ta cikin waya, to amma ai sai wanda yake da ilminta, sabanin Rediyo wanda ko ba ka da ilmi za ka iya kama tasha ka kuma ji abin da ake fada.