Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 2
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:Waya ta fi amfani […]
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:
Waya ta fi amfani kwarai – Malam Nur
Malam Nur: “Ai idan ana batun muhimmanci a tsakanin wadanann abubuwa biyu, kowa ya san waya ta fi amfani. Domin mutum zai iya shafe kwanaki ba rediyo a tare da shi, amma waya fa? Ko cajin wayar ne ya dauke yanzu mutum zai shiga damuwa saboda irin muhimmancin da take da shi a gare shi. Waya ta sawwake harkokin sadarwa, cikin ’yan dakiku sai mutum ya yi magana da dan uwansa ko abokinsa da ke wata kasa daban.”