Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 3

Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:Wayar tarho ta fi […]

Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 3
Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 3

Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:
Wayar tarho ta fi muhimmanci – Hamza Wada

Hamza Wada Saharif: “Babu shakka wayar sadarwa ta fi muhimmanci ko amfani ga jama’a, musamamn a wannan zamani da muke ciki, idan an yi la’akari da yadda take biya wa mutane bukata cikin hanzari. Da waya mutum zai gudanar da harkokin kasuwancinsa cikin sauki ba tare da waya ba. Mun san rediyo na da nasa irin amfani.”