Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 4
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane: Rediyo ya fi […]
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:
Rediyo ya fi Waya muhimmanci – Hajiya Hafsat
Hajiya Hafsat Usman Liman: “A gaskiya duka biyu, wato Rediyo da Waya suna da mahimmanci sosai ga mutum amma idan ana maganar wanda ya fi amfani, to a gaskiya Rediyo ya fi amfani. Domin yau akwai wasu wurare da idan ka ta fi ba za ka iya amfani da waya ba don babu sabis amma za ka iya amfani da Rediyo a wajen. Kuma akwai mutane da dama da ba su iya amfani da waya ba amma sun iya amfani da radiyo, don yana da saukin gane yadda ake amfani da shi fiye da waya, kodayake ita ma Waya kamar yadda na fada a baya tana da nata amfani sosai ga mutum.”