Tsakanin rediyo da wayar tarho, wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 5
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane: Wayar tarho ta […]
Babu shakka a wannan zamani da muke ciki, rediyo da wayar tarho suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakon al’umma ta hanyoyi daban-daban. Abin tambaya a wannan muhawara, shin tsakanin wadannan na’urori wanne ya fi muhimmanci ga al’umma, tsakanin rediyo da wayar tarho? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mabambantan mutane:
Wayar tarho ta fi muhimmanci – Abubakar Musa
Abubakar Musa: A nawa ra’ayi dai Waya ta fi mahimmanci ga dan Adam fiye da Rediyo, domin yanzu ana wani zamani ne wanda sai ka ga damar sayen Rediyo za ka saya. Don idan ka lura, wayoyin salula da dama da ake yi yanzu suna da radiyo da zaka iya kunnawa ka ji labarai da sauransu, ba sai ka sayi radiyo ba. Haka kuma za ka iya aiko da sako da nisa da yin kira da dai sauransu. Saboda haka ni ban ga wani abin da za a ja a nan ba, waya ta fi Rediyo amfani ga rayuwar dan Adam a zamanin da muke ciki yau.”