Tsakanin talakawa da masu mulki: Malamai ku ji tsoron Allah
A yau, Malam Nasir Abbas Babi (08033186727), bulala ya dauka, ya shauda ta ga wasu karkatattun malaman addini da ke wuce gona da iri wajen haddasa fitina cikin al’umma, sannan ya yi musu nasiha da su ji tsoron Allah. Ga abin da yake cewa: Sha’anin Najeriya, to sai dai mu ce Allah Ya gyara amma […]
A yau, Malam Nasir Abbas Babi (08033186727), bulala ya dauka, ya shauda ta ga wasu karkatattun malaman addini da ke wuce gona da iri wajen haddasa fitina cikin al’umma, sannan ya yi musu nasiha da su ji tsoron Allah. Ga abin da yake cewa:
Sha’anin Najeriya, to sai dai mu ce Allah Ya gyara amma fa duk inda ni nake zato, da kuma inda kai kake zato lallai abin ya wuce nan. Ana cewa ’yan boko zalla na dagula al’amura, yanzu kuma lamari ya dawo hatta malamanmu na addini da muke girmamawa, muke darajjanta su, sun zamto gaba-gaba cikin masu dagule al’amura! To ina mafita ke nan?
Idan muka yi la’akari da addinin Kiristanci da tsarinsa, muka yi la’akari da addinin Musulunci da tsarinsa, sai mu ga cewa babu addini daya wanda annabinsa ke horo da tashin hankali da kuma neman tayar da zaune tsaye. To me ya sa ake ta hasarar rayuka a karkashin inuwar wadannan addinai? Saboda malaman addinan biyu mafi yawansu sun saki hanyar koyarwar addinan, suna amfani da iliminsu domin nema wa kansu girma da daraja.
’Yan siyasa ne ke da alhaki wajen rura wutar kabilanci da addinanci a cikin wannan kasa ko shakka babu amma malamanmu suna aikin me har suka bari wannan lamari ya girma haka? Ashe ba aikinsu ne su fadakar da mu a kowane lungu da sako domin mu fahimci gaskiyar kowane lamari da kan iya kawo cikas a cikin addini ba? Akwai malaman da suke iya kokarinsu, Allah Ya saka musu da alheri. Sai dai Hausawa suka ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi.
Inda matsalar take da girma shi ne, malaman ba su kare muradin addini, ba su kuma kare muradun talakawa ko na shugabanni. Sun mayar da abin kasuwanci ne. Duk inda za a samu abin sakawa a cikin aljihu, shi ne muradinsu, ko kuma duk inda za a samu daukaka a idanuwan talakawa, ko kuma samun shiga wajen masu mulki. Amma da wuya kake samun malami na Allah da yake wa’azinsa saboda neman yardar Allah kadai ba tare da ya surka wa’azinsa da neman yardar mutane ba.
Duk malami na Allah, ba za ka same shi yana ta sukar lamirin wasu mutane ko wasu kungiyoyi ko wata jama’a a wurin wa’azinsa ba. Sai dai ka same shi yana horo da alheri da kuma hani da aikata sharri! Idan wata matsala ta bijiro wa al’umma, sai ya ankarar da al’umma a kanta. To sai a irin wannan yanayin za ka samu ya kama sunan wata kungiya ko wasu mutane yana jan hankalin al’umma a kan aibi ko musibar da ke iya samuwar su sanadiyar wata kungiya ko wasu jama’a. Amma shi ma sai idan yana da hujjoji kwarara.
Amma ka samu malami na kirkirar karya ko kuma hawa dokin ra’ayi yana ingiza al’umma da kalaman da kan iya sanya su yin bore wa gwamnati ko wani mutum da bai san hawa ba bai san sauka ba, wannan ba daidai ba ne. Kuma akan samu wannan matsalar ne idan malami ya yi kokarin yin katsalandan cikin harkar da bai san kanta ba, bai kuma san yadda take tafiya ba.
Malami mai wa’azi, ya kamata ne ya tofa albarkacin baki a kan abin da yake da cikakken sani a kansa, ba a kan wani labari da aka kawo masa ba kawai, ko kuma abin da son zuciyarsa ya saka masa. Malamin da yake zaune a Jihar Adamawa misali, ina ruwansa da abin da ya shafi siyasar Jihar Kebbi, Zamfara ko Sakkwato? Siyasa fa! Ai ko wace jiha akwai malamai a cikinta (’yan cuwa-cuwa da kuma na Allah), Don haka idan cuwa-cuwar yake so ya yi, ya tsaya a jiharsa mana. Idan kuma kira yake yi zuwa ga hanyar Allah, ya tsaya a jiharsa mana. Yadda yake na Allah, to akwai na Allah ko a jihata, kowa ya yi kokarin gyara yankinsa ba sai ya wuce gona da iri ba.
Amma tare da haka, idan al’amari bai hada da siyasa ba, misali abin da yake faruwa a Borno, Adamawa da Yobe da sauransu, wannan abu ne da ya shafi addini kai tsaye. Ba illa ba ce idan malamin addini ya dage wajen tofa albarkacin bakinsa ta hanyar kiran mutane su dage zuwa addu’a da fadakar da mutane a kan abin da yake ganin ya haifar da wannan matsalar da kuma abin da yake ganin shi ne mafita. To amma tare da haka, malami ya kamata ya yi taka-tsan-tsan don gudun kada ya janyo wata sabuwar musibar kuma.
Yanzu mu dauki misali daga kan Malam Sallau, ya dade yana bayanai masu zafi a kan mai sunan Sahabi, bayanai da kan iya harzuka mutane su dauki matakin kawar da shi (Mai sunan Sahabin) daga doron kasa, inda Allah Ya kiyaye dai shi ne, mutanen garin mai sunan Sahabi ba su yi gaggawar daukar al’amarin da hannunsu ba, har zuwa ranar da Allah Ya bayyana ikonSa. Aka zo aka bayyana gaskiyar lamarin.
Kowa ya san mutanen garin mai jar kalamsuwatun ba su daukar raini, kuma ba su sassautawa ga dukan wanda suka kama da hannu a cikin yaudarar al’umma. Yanzu ba domin Allah Ya tsare ba, da sun kai hari ga Mai sunan Sahabin suka kone gidansa, ko kuma suka ji masa da iyalansa rauni, kuma daga baya aka zo ta bayyana cewa abin da aka fada a kansa ba gaskiya ba ne, kuna ganin al’amari ya yi sha’awa ke nan?
Saboda haka ya zama wajibi malamanmu ku ji tsoron Allah. Dukan wasu bayanai da kan iya harzuka talakawa su yi wa gwamnati bore, ba daidai ba ne. Kowa dai ya san kalaman da shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya ke yi, abin haushi ne a ce malamin addini ne yake yin su. Kuma tabbas, kalamansa suna daga cikin kalamai na gaba-gaba da ke harzuka wutar kiyayya tsakanin Kirista da Musulmi a wannna kasa. Kuma wannan ba koyarwar Masihu Isah dan Maryam ba ce.
***