Tsakanin yanayin hunturu da zafi, wanne ya fi takura mutane?

Yanayin hunturu, lokaci ne na sanyi da muku-muku, a yayin da lokacin zafi kuwa ya kasance na zufa, inda iska kan kuntata. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan yanayi na hunturu da zafi, wane ne ya fi takurawa ga mutane? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: […]

Tsakanin yanayin hunturu da zafi, wanne ya fi takura mutane?
Tsakanin yanayin hunturu da zafi, wanne ya fi takura mutane?

Yanayin hunturu, lokaci ne na sanyi da muku-muku, a yayin da lokacin zafi kuwa ya kasance na zufa, inda iska kan kuntata. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan yanayi na hunturu da zafi, wane ne ya fi takurawa ga mutane? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

An fi samun lafiya a lokacin hunturu – Ibrahim Balali

Hamza Aliyu, a Bauchi

Ibrahim Ahmad Balali Mula: “Maganar gaskiya shi ne, sanyi ya fi dadin sha’ani fiye da lokacin zafi. Misali, idan za ka kashe Naira dari biyu ne a lokacin sanyi, to a lokacin zafi sai ka kashe sama da Naira dari biyar wajen sayen man janareto. Idan mutum ya yi tsam da ransa zai fahimci cewa sanyi yana da magani, za ka iya kwanciya ka rufu da gwado ba tare da wata matsala ba.
“A matsayina na mai saida bakin mai, babu lokacin da muke samun kasuwa sai lokacin zafi. An fi ciniki fiye da lokacin sanyi. Saboda haka da yawa daga cikin mutane sun fi samun koshin lafiya a hunturu. Amma duk da haka akwai wadanda sun fi jin dadi a lokacin sanyi, mata da kananan yara ba su kaunar zafi a rayuwarsu, domin a lokacin ne wasu cututtuka suke kunno kai a tsakanin al’umma.”

Sanyi ya fi kuntata wa mutane – Sani Muhammadu

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Sani Muhammadu Zedom: “Na fi son zafi saboda walwala fiye da lokacin sanyi. Lokacin sanyi ba a hira kodayaushe, mutane na daki kuma ga yawan gobara saboda amfani da wuta kuma yara na yawan konewa saboda jin dumi. Don haka sanyi ya fi kuntata wa al’umma fiye da lokacin zafi, saboda haka zafi ya fi dadi a ganina.”

Yanayin zafi ya fi kuntata wa jama’a – Shu’aibu Abubakar

Hussaini Isah, a Jos

Alhaji Shu’aibu Abubakar: ‘’Ni a ganina yanayin zafi ya fi yanayin sanyi kuntata wa jama’a, domin idan aka dubi wuraren da suke da zafi, suna neman abubuwan sanyi don su sami sauki kuma shi yanayin sanyi yakan boye cututtuka. Amma da yanayin zafi ya zo sai ka ji cututtuka sun barke. Don haka ni a ganina yanayin zafi ya fi yanayin sanyi kuntata wa jama’a.”

Zafi ya fi takura wa mutane – Zakariyya Goje

Hamza Aliyu, a Bauchi

Zakariya Umar Goje: “A matsayina na jami’in kiwon lafiya, wanda yake hada-hadar saida magunguna, babu lokacin da al’umma suke dandana kudarsu kamar lokacin zafi. A lokacin zafi an fi kamuwa da cututtukan amai da gudawa da zazzabin cizon sauro. Bayan haka, kashi 85 cikin 100 na ’yan Najeriya sun fi son lokacin sanyi fiye da lokacin zafi. Misali, ni da nake saida magunguna babu lokacin da muke samun kasuwa sai a lokacin zafi, cututtuka da dama sun fi tashi a lokacin. Wadanda Allah Ya albarkace su da injinan janareto, sun fi kashe kudi a lokacin zafi.
“Kuma idan ka duba sosai, da zarar an fara zafi sai ka ga yanayin cin abinci na mutane ya canza sannan idan ka tambayi mafi yawan al’umma za su tabbatar maka da wannan magana tawa. Kamar yadda na fada maka a baya, a lokacin zafi idan ka zo nan shagon za ka samu dimbin mutane suna layin karbar magunguna ba dare ba rana.”

Na fi sha’awar sanyi fiye da zafi – Nasiru Adamu

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Nasiru Adamu Samaru: “Zafi na kuntata wa al’umma fiye da sanyi, domin ka ga dai dole ka bar kofa a bude kuma ga sauro ga shi ba barci ga kuma yawan ciwon sankarau, ga ciwon kyanda da ke kama kananan yara kuma ga kwalara. Mutane ba su son zama a gida sai yawan fira. Lokacin sanyi kuwa kowa na daki tare da iyalinsa, don haka sanyi ya fi dadi.”

Sanyi ya fi dadi ga jama’a – Salisu Ibrahim

Hussaini Isah, a Jos

Alhaji Salisu Ibrahim: ‘’A gaskiya yanayin zafi ya fi uzura wa jama’a saboda a lokacin yanayin sanyi ana amfani da abubuwan da suke kare sanyi kamar rigunan sanyi. Amma a lokacin yanayin zafi jama’a sukan rasa yadda za su yi, cututtuka suna kama jama’a. Amma a lokacin yanayin sanyi za ka ga cututtuka sun kwanta. Don haka yanayin zafi ya fi uzura wa jama’a.”