Tsakaninmu da ’yan Jari-Hujja
Hakika harkar siyasa ta kankama a ’yan kwanakin nan, kuma jam’iyyun siyasa musamman manyan jam’iyyun nan biyu APC da PDP sun tashi gadan-gadan suna yakin neman zabe don ganin sun samu nasara a zaben badi da ke kara gabatowa. Kuma mun ji yadda wadanda ya kamata a ce sun zamo ’yan ba-ruwanmu a siyasar jam’iyya […]
Hakika harkar siyasa ta kankama a ’yan kwanakin nan, kuma jam’iyyun siyasa musamman manyan jam’iyyun nan biyu APC da PDP sun tashi gadan-gadan suna yakin neman zabe don ganin sun samu nasara a zaben badi da ke kara gabatowa.
Kuma mun ji yadda wadanda ya kamata a ce sun zamo ’yan ba-ruwanmu a siyasar jam’iyya suka dawo suna caccakar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa ta gaza don haka ba za su goya mata baya ba a matsayinsu na dattawan Arewa.
To amma ko kafin a je ko’ina wadansu daga cikin ’ya’yan wannan kungiya sun ce ba da yawunsu aka yi wannan magana ta juya wa Shugaba Buhari baya ba.
Ba ina kare Shugaba Buhari ba ne kawai da wannan rubutu, a’a ina kare makomar kasarmu ce wadda ’yan Jari-Hujja suka yi mata tsirara suka mayar da ita fanko suka nemi kai ta Lahira ta zamo babu ita kacokan.
’Yan Jari-Hujja da suka nemi ruguza kasar nan domin biyan bukatun kashin kansu suna daukar mutanen Najeriya tamkar ba mu san abin da muke yi ba ne.
Sun manta cewa muna rike da duk barnar da suka tafka tun daga 1988 zuwa shekarar 2015, inda suka yi wa kansu da abokansu gwanjon kasar nan.
Mutanen da suka rika dauki-daidai da dukiyar kasa suna mayarwa tasu wai su ne za su dawo suna cewa su ne za su iya gyara Najeriya. Ta ina za su gyara Najeriya, sai dai su karasa kashe ta a neme ta a rasa kamar yadda suka so ta auku har Amurka ta yi hasashen kasar za ta wargaje kafin shekarar 2015.
’Yan Jari-Hujja sun iske Najeriya da muhimman cibiyoyi kamar kamfanoni da masana’antu na gwamnati wadanda suke taimakawa wajen samar da dimbin ayyukan yi ga jama’a, amma suka kassara su suka yi wa kawunasu gwanjonsu da sunan sayar da hannun jarin gwamnati. Yau ina aka kwana bayan sayar da wadannan kamfanoni? Ai gwanda gwamnati ta rika asarar kudi wajen zubawa a wadancan kamfanoni da hukumomi tana samar da aikin yi da a sayar da su ga wadanda za su rufe su a rasa aikin yi, a karshe rashin aikin ya samar da dubban ’yan ta’addan da za a zo ana kashe biliyoyin Naira wajen yakarsu kamar yadda lamarin yake a yanzu. Yau ina Kamfanin Sadarwa na Kasa (NITEL) wanda bayanai suka nuna cewa shi kadai yana samar da kudin da ake iya biyan sojoji albashi? Ina Hukumar Aikewa da Sakonni? Ina Kamfanin Taki na Onne a Fatakwal da Kaduna? Ina kamfanonin harhadar motoci na Fijo da ke Kaduna da Fait a Kano da Styer a Bauchi da Boswaja a Legas da Anamco a Anambra? Ina Kamfanin Yin takardu na Oko-Ibuku a Jihar Ribas? Ina masaku da daruruwan kamfanonin ’yan kasuwa da ’yan Jari-Hujja wadanda akasarinsu ma’aikatan gwamnati ne da masu da rike da mukaman mulki suka durkusar?
A shekara uku na farkon gwamnatin PDP ta Obasanjo jaridar Weekly Trust ta taba buga wani rahoto da ke cewa sama da masana’antu 200 aka rufe a birnin Kano kawai.
Duk wannan bala’i masominsa muguwar hadama da babakere da mugunta na ’yan Jari-Hujja ne da yanzu suka zagayo suke neman su komo gadon mulki.
Kamfanin taki na Fatakwal wanda yanzu ya koma Indorama, bayanai sun nuna sai da aka kashe masa Dala miliyan 500, sannan aka sanya shi a kasuwa, kuma Alhaji Aliko Dangote ya taya shi a Dala miliyan 150, amma aka ki sayar masa aka sayar wa wadansu ‘mutanen waje’ a kan Dala miliyan 100! Na sa mutanen waje a cikin baka mai ruwa ne saboda ina da shakku kan cewa mutanen kasar waje ne, maimakon haka ina zargin an yi mana dodorido ne da su aka sayar wa kai.
Haka aka sayar da kamfanonin siminti na kasar nan da duk wata kadara ta gwamnati bisa alkawarin ’yan kasuwar za su inganta su fiye da gwamnati ta yadda kayan da suke samarwa za su yi araha, amma a karshe ina aka kwana?
Mun samu kanmu ne kawai gara jiya da yau, ma’ana gara gwamnati ta rika asarar kudin da take zubawa a wadancan kamfanoni da masana’antu da a ce ta zo tana kashe ninkinsu wajen magance matsalolin barayi da ’yan ta’adda da galibi rashin aikin yi ne, ya haifar da su!
’Yan Jari-Hujja sun kashe kasar nan murus, tunda sun bar gwamnati babu abin da take iya yi, sai daukar ma’aikata a ofisoshi, wadanda ma’aikatan da suke ciki sun fi karfinsu baya ga fatalwoyin ma’aikata da babu su babu alamarsu, sai dai zuke albashin da suke yi zuwa aljifan ’yan Jari-Hujja kananansu da manyansu.
Kai illar ’yan Jari-Hujja ta kai bayan sun kashe ma’aikatu da masana’antu da gangan don su yi wa kansu gwanjo, sai kuma suka dawo suna kafa kamfanonin ci-da-gumin talakawa, irin su kamfanonin tsaro da na shara da sauransu, inda za su kafa kamfani ba jarin kirki su nemi a rika ba su kwangilar harkar tsaro da shara a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a ba su kudi mai yawa su kuma su rika biyan ma’aikatan da suka dauka dan abin da bai taka kara ya karya ba!
Ana kuka gwamnatin Buhari ta gaza inganta tattalin arziki, amma an manta daukacin harkokin tattalin arzikin na hannun ’yan kasuwa ’yan Jari-Hujja ne wadanda suka saba a ba su Dalar Amurka su sayar su samu riba maimakon sayo na’urori da kayayyakin da za su dada inganta kayayyakin da muke samarwa. Wadannan ’yan Jari-Hujja fa sun yi wa kawunansu gwanjon kadarorin gwamnati ta yadda baya ga kamfanoni da masana’antun ’yan kasuwa da na gwamnati hatta gidajen da Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka gina ga ma’aikata tun zamanin Turawa sun sayar da su, sai dan abin da ba a rasa ba.
Shin irin wadannan mutane har suna da bakin da za su ce Buhari ya gaza? Shin sun dauka ’yan Najeriya sun mance wannan muguwar barna da suka yi wadda in da wata kasa ce da yanzu sai buzunta?
Don haka ’yan Najeriya ku sake bitar barnar da aka yi wa kasar nan daga 1988 da kuma na cikin shekara 16 na mulkin PDP. Kada ku sake a mayar da hannun agogo baya!
PDP ta samu damar da za ta mayar da Najeriya kasa mai karfin arziki da fada-a-ji a duniya, amma a karshe ta bar mulkin kasar nan albashi ma ya gagari sama da jihohi 30 daga cikin 36, balle maganar fansho. Wannan ya karfafa samuwar mabarnata da suke gudanar da ayyukan ta’addanci kama daga Boko Haram da barayin shanu da na mutane da sauransu. Don haka babbar matsalarmu ita ce ta ’yan Jari-Hujja kuma ya kamata mu tabbatar ba su sake mayar da mu gidan jiya ba.
Alhaji Adamu Shuwa Damboa
Dan kasuwa kuma dan siyasa ne da ke Mpape, Yankin Bwari, Birnin Tarayya, Abuja
08055945695, 08033515344