Tsakure daga littafin Kirarin Duniya 222
Wani mashahurin littafi da na yi kicibis da shi, shi ne littafi mai suna ‘Kirarin Duniya 222’ wanda mashahuran malamai, Malam Rabi’u Muhammad Zarruk da Malam Habib Alhassan suka rubuta, wanda kuma kamfanin wallafa na Ganuwa Publishers Limited, Zariya ya wallafa, wanda kuma ya fito a cikin shekarar 1982.Kamar yadda masana suka tantance, kirari na […]
Wani mashahurin littafi da na yi kicibis da shi, shi ne littafi mai suna ‘Kirarin Duniya 222’ wanda mashahuran malamai, Malam Rabi’u Muhammad Zarruk da Malam Habib Alhassan suka rubuta, wanda kuma kamfanin wallafa na Ganuwa Publishers Limited, Zariya ya wallafa, wanda kuma ya fito a cikin shekarar 1982.
Kamar yadda masana suka tantance, kirari na daya daga cikin wani ginshiki ko bangare da ke bayyana al’adar al’umma kuma yake adana tarihi da taimaka wa al’ummar wajen ci gaba, kamar kuma yadda yake taimakawa wajen nishadantarwa, ilimantarwa da fadakarwa.
Kamar yadda daya daga cikin marubutan littafin, Malam Habib Alhassan ya fada, a yayin da yake rubuta mukaddima a shafi na b na littafin; ya ce: “Sanin kowa ne, idan aka sami wata halitta, mai tsananin jaruntaka ko gwaninta ko mai yawan rikida, wacce ba ta iya tsayuwa a kan halinta da aka sani, akan shirya mata kirari na musamman, saboda ya nuna siffofinta da halayenta a fili, a karbi na karba, a guji na gudu. Tun tuni Hausawa suka shirya wa duniya irin wannan kirari, suna kuma amfani da shi wajen wasu matsalolinsu na yau da kullum. Sai dai saboda kulawarsu da irin wannan kirari, da kyakkyawar hardar da suka yi masa, ba su bukaci ma su rubuta shi ba. A ganina, ya fi kyau a tara shi a wuri daya a rubuce, saboda yara manyan gobe, ko kuma don gudun kada wata rana a wayi gari, a neme shi, a rasa shi sam.”
Lallai kam gaskiyar wannan bayani na sama ba ta kankaruwa, musamman idan mutum ya bibiyi kunshiyar littafin, wanda ke dauke da kirarin duniya guda dari biyu da ashirin da biyu cur. Dalili ke nan ma na ga ya kamata in dan tsakuro kadan daga cikinsa, domin maido mana da kaifiyyar tunanin kirkiro wasu kirare-kiraren ko kuma mu sake bincike domin zakulo wasu tsoffin kirarin da suka shafi wasu bangarori na rayuwarmu. Kada mu mance da cewa, magana fa jari ce, kuma kafa ce ta adana tarihi, ta fadakarwa, ilimantarwa da kuma nishadantarwa.
Shi kuwa daya marubucin da suka yi tarayya wajen rubuta littafin, watau Malam R. M. Zarruk, a yayin da yake rubuta gabatarwa ga littafin, a shafi na bii, ma’anoni ya tsakuro game da kirari, musamman ta fuskar wasu bangarori na rayuwa. Ga kadan daga abin da yake cewa:
“A fagen nishadi kam, a iya cewa babu wanda bai san matsayin kirari ba. Domin kirari shi ne gishirin kida da waka da sauran al’amuran da suka shafi bukukuwa. Shi ne kuma sinadarin take da zambo. Bayan haka, kirari nau’i ne na fasahar harshen Hausa. Duk abin da ya burge Bahaushe, ko wanda ya ba shi tsoro, ko ya iya gagarar sa, ko ya ba shi mamaki, to lallai za ka ji ya yi masa kirari. Saboda haka dabbobin daji, kamar su zaki da giwa da damisa da kura da sauransu, duk suna da kirari. Wani kirarin yana gwada karfin dabbar ne, ko fadanta, ko wasu halayenta na tsoratarwa.
“A muhimman abubuwa na kasar Hausa, kusan babu wanda ba shi da kirari. Garuruwa da sauran nau’o’i da mutane maza da mata, yara da manya, duk suna da irin nasu kirari. Ana yi wa namiji kirarin mazakuta. Mace, ana yi mata kirari game da halayenta na mata. Haka nan tsoho da yaro, duka akwai abin da ake fada game da su a cikin kirari. Da aure da haihuwa da mutuwa, duka babu wanda bai sami kirari ba. Kowane daya daga cikin wadannan abubuwa, in ka ji tarin kirare-kiraren da aka yi masa, zai ba ka mamaki. To, ka ji dalilin da ya sa aka ce kirari abin nishadi ne.
“A fagen nazari kuwa, kirari wani rukuni ne na fasahar harshen Hausa da al’adun mutanenta. Ita kuma wannan fasaha ta harshe, ta baka ce ko rubutacciya ce, ita ake kira adabi. Watau idan an ce Adabin Hausa, an kira dukkan fasahar harshen Hausa ke nan. Adabin Hausa kuwa, da ma fanni ne guda, wanda ake tsayawa a yi nazarinsa a makaranta. Saboda haka, idan an yi nazarin kirari, kamar an dauki wani rukuni ne a cikin Adabin Hausa.
“Bayan haka, duk kirarin da aka yi wa duniya sako ne. Cikinsa akwai abubuwa da yawa. Akwai gargadi da nasiha da tsawatarwa da hattara da ban mamaki. Wadannan abubuwa kuwa, kowannensu makaranta ne, watau abin nazari ne.
“Jerin kirarin duniya, wanda aka zaba aka rubuta a wannan littafi, ba fa shi kadai ne kirari ba. Duk abin da aka dauka, muddin ya shafi rayuwar Hausawa, to, ana iya tara masa nasa kirarin. Don haka, ba abin mamaki ba ne, nan gaba ka ga an dauki garuruwan Hausa ko dabbobinsu, ko wani abu makamancin wadannan, an tara masa kirari. Fagen dai ba zai kare ba!
“Bayan haka, kirari abu ne ginanne, watau ba marubuta littafin ne suka kago shi ba. Haka suka jiwo shi a bakin Hausawa. Sai dai kuma, yayin da ake tara kirarin, duk wanda aka tashi dauka sai an ji karshensa. Alalmisali, idan aka ji wani ya ce: ‘Duniya uwar kare!’ ya yi shiru, ba za a hakura da wannan ba, sai an tambaye shi, an ji karshen kirarin, kana a rubuta kamar haka: ‘Duniya uwar kare, ba don ke ba da kare ya yi nika!”
Lallai kam, bayani ya gabata mai gamsarwa, saura da me, bari mu dan yi ninkaya cikin littafin domin tsinto kadan daga cikin kirare-kiraren duniya, kamar yadda marubutan suka rubuta su.
Ga wasu daga kirarin duniya: 1-Duniya masakin kunu, yaro yadi a hankali! 2-Duniya karyar sarki, ta dansamadu maganinki Allah! 3-Duniya limaminki ba a bi masa Sallah, ko an bi shi dole ake sakewa! 4-Duniya gururud dara, kowa ke cinikinki ba shi gane halinki! 5-Duniya katangar yashi, ana gini kina rushewa! 6-Duniya kwan dodo, kowa ya tarar ana nemanka! 7-“Duniya baltsangu” inji matar kwado, a bata ruwa a sha a yi tsarki! 8-Duniya kin fi sarka rikici, sarka takan rikice akan gyara ta! 9-Duniya makahon ciniki, cikin rashin sani ake kullawa. 10-Duniya tsohuwa mai zare da abawa, gwanar bartaka ta wane da wance! 11-Duniya kurunguzugudum, koginki ga ruwa ba gaba! 12-Duniya ohoro maganin sodoro, fate-fate sai an tona akan ci a sude! 13-Duniya kitson Barahaza, wani kwance wani tsaye, wani cure, wani ko kama da tsinin mashi! 14-Duniya makiyiya mai kama da kawanya, mai hankali yakan gane ta! 15-Duniya kure-makaryata, kowa ya ce babu sai kin ce masa akwai, in ya ce akwai, ki ce masa babu! 16-Duniya tukin sakwarar Ladi, in ta yi haka ta tuke, in ta yi haka ta kwashe, wata rana ko ta tuka ba ta kwashe ba! 17-Duniya walankelu-walankeluwa, sarkin kowa ta wankalazuke, in kin so mutum kina yi masa jakar baya! 18-Duniya rawar kunkuru da bushiya, ana fitar da kai ana nokewa! 19-Duniya ta Duna ba ki son mai son ki, jakar aro baka ki sabo! 20-Duniya ma-fiha, abin da ke cikinta jami’an, komai ka gani, wata rana ana rasa ganinsa. Galibin komai ka gani cikinta an yi kamarsa!”
Kadan ke nan daga kirare-kirare guda dari biyu da ashirin da biyu da ke cikin littafin, wanda haka ke nuna mana cewa lallai kam kirari darasi ne, ilimi ne, kamar kuma yadda ya kasance fadakarwa da nishadantarwa.