Tsalle daya ake yi a shiga uku

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da korar ma’aikata sama da dubu hudu daga kananan hukumomi ashirin da uku da ke Jihar a matsayin abin da ta kira gyararrakin da za su bayar da damar gudanar da harkokin kananan hukumomin ba tare da wata tangarda ba. Tun farkon hawan Gwamnatin Nasir el-Rufa’i ne ake ta dauki-ba-dadi […]

Tsalle daya ake yi a shiga uku

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da korar ma’aikata sama da dubu hudu daga kananan hukumomi ashirin da uku da ke Jihar a matsayin abin da ta kira gyararrakin da za su bayar da damar gudanar da harkokin kananan hukumomin ba tare da wata tangarda ba. Tun farkon hawan Gwamnatin Nasir el-Rufa’i ne ake ta dauki-ba-dadi da ma’aikatan kananan hukumomin da aka ce sun yi yawa, kuma da yawa daga cikinsu wai ba su da aikin yi, haka nan ake musu gata suna karbar  albashin awuf. A cewar gwamnatin yin haka zai sa a samu wadatattun kudin inganta ayyukan kiwon lafiya da gudanar da makarantu da kuma yin wasu ayyukan da suka kamata don kyautata halayyar zamantakewar al’ummomin yankunan karkara. 

To amma ai an ce idan mafadin magana ba shi da kan-gado ai  mai saurarensa ba gaula ne ba, yakan iya fahimtar abubuwan da aka fada, ya kuma tantance gaskiya don  ya yi aiki da ita, ya kuma yi watsi da karairayin da ke ciki. Mutanen Jihar Kaduna na cewa batun gyararrakin da Gwamna Nasir ke cewa su ne dalilansa na raba dubban ma’aikatan kananan hukumomi da abincinsu gyara ce irin  ta gangar Azbinawa, wacce bayan an yi sai kuma a dauko lauje a nemi  kadawa da ita don a tabbatar ta gyaru. Ina amfanin gyaran da zai sa jama’a  da yawa zubar da hawaye,  a gidaje da yawa kuma ana kururuwa kamar an yi mutuwa, birane da kauyuka  ana manufar waccan gyaran da kuma sakamakon bakar wahalar da ta haifar?

Gwamnati ta ce wai ba korar wadancan ma’aikatan aka yi ba, ritaya ce aka yi wa fiye da dubu uku daga cikinsu, wadanda za a biya su fansho da giratuti, aka kuma sallami sama da dubu guda da za a ba albashin wata guda a yi ban-kwan da su. A’aha! Ba cinya ba kafar baya !!  Wanda duk aka tilastawa yin ritaya alhali lokacinsa na yin haka bai kai ba, ana iya  cewa ke nan  ba kora da hali aka yi mar ba? Shi kuma wanda aka sallama haka nan zikau-mikau, wane laifi ya aikata aka kuma bi bahasi aka tabbatar da cewa hakan ya cancanci a sallame shi?

To an ji cewa za a biya wadancan mutane hakkokinsu gaba daya, kuma kacokan a karshen watan Fabrairun sabuwar Shekara, sai a tabbatar an yi hakan don kada ta kai su ga tagayyara, ba su ga tsuntsu ba su ga tarko, ga kuma nauyin iyali jibge a kawunansu babu yadda za su iya saukewa. Kafin a kai ga hakan kuma wajibi ne a  biya su dukkan hakkokinsu  da suka jibanci albashi da alawus-alawus din su na watanni uku, sa’annan a tabbatar ba a jinkirta biyansu giratutinsu ba,  a kuma hanzarta sanya su cikin masu karbar albashin fansho kowane wata. Idan  aka yi la’akari da yawan mutanen da suka yi shekaru sama da ashirin, wasu ma kusan talatin suna aiki,  ai da ba a gaggauta korarsu ba a lokacin da ake cewa an yi haka ne don samun wadatattun kudin inganta ayyukan kananan hukumomi, domin kuwa kudin sallama da na giratutin da za a biya su zai kusan kaiwa Naira miliyan dubu tara. Wannan na ma’aikatan kananan hukumomi ne kadai. Ina kuma a ce an hada da na malaman makarantun firamare? To, da wanne gwamnati ko kuma kananan hukumomin  za su ji da shi, biyan giratuti da kudin sallamar ma’aikatan da aka rage, ko kuwa yin amfani da kudin don aiwatar da muhimman ayyukan ciyar da yankunan  kananan hukumomin gaba? 

Idan aka yi la’akari da kyau za a fahimci cewa tun hawan Gwamnatin Nasir el-Rufa’i kananan hukumomi ke ta kanfar kudi, hakan ne kuma dalilan da ta bayar na korar hakimai da dagatai don a rage wa kananan hukumomi nauyin biyan su albashi. Yanzu kuma ga shi nan an rage ma’aikata bisa wannan dalilin. To amma ai a zamanin gwamnatin da ta shude kananan hukumomin ba su kasa biyan albashin  ma’aikatun masarautu da na ma’aikatansu ba, domin gwamnatin Jihar ta jam’iyyar PDP na  sakar musu dukkan kudinsu na kason arzikin kasa da ake aiko masu da su ta hannun gwamnatin jihar. A yanzu ma ba an daina aiko musu da kudin ne ba, Gwamnatin el-Rufa’i ce ake zargin cewa ba ta fitar musu da nasu rabon da ake gwamawa da nata idan gwamnatin tarayya ta tashi aikowa.  Ai ga alamu nan birjik da ke nuna haka, domin kuwa babu wasu ayyukan da kananan hukumomi ke aiwatarwa a yankunan karkara saboda rashin kudi, ko a manyan birane ma gwamnatin jiha ce ke aiwatar da irin ayyukan da ya kamata a ce kananan hukumomi ne ke yi ba ita ba. 

Ta ko ina dai aka dubi wannan al’amari na yanayin da kananan hukumomin Jihar Kaduna suka kasance a ciki sai a fahimci cewa Gwamnatin el-Rufa’i ta yi musu dabaibayi  har ba su iya rawar gaban hantsi, ta kuma daddaure masu hannuwa  ba su iya tabuka komai, ta ki sakar musu mara balle su fitsare, ta kuma doddode masu bakuna ba su iya yin kuka game da yadda ake takura musu, kana kuma ta makanta su ba su iya gane gaskiya su kuma yi aiki da ita.  A takaice dai abin da hakan ke nunawa shi ne  kananan hukumomin Jihar Kaduna ba su iya cin gashin kansu, domin  gwamnati ta tauye musu hakkokinsu, ta mayar da dukiyarsu nata da karfi da yaji, sai yadda ta ga dama za ta sarrafa, kuma sau da yawa ba bisa kyakkyawan tafarkin da zai amfani jama’ar yankunan karkara ba.

Jama’ar yankunan na sane da haka, suna kuma jin takaicin irin farfagandar da ake cika su da ita daga kafafen yada labarai game da ayyukan gaibun da ake cewa ana shimfida musu, domin suna kusa da shugabannin kananan hukumomin da ake nannada musu wadanda su ma  ‘yancinsu tauyayye ne, ba su iya tabuka komai saboda dukiyarsu ba ta isa gare su, gwamnatin jiha ta danne. Wannan ne ya sa fatara da mayata suka yi kamari a yankunan karkara, inda  marasa sana’a ko wani  aikin yi suka fi yawaita, domin daga noman damina ko  farautar zomo ba kuma wani abin yi. To yanzu kuma ga shi nan  korar da aka yi wa dubun-dubatan malaman makarantun firamare da  daruruwan ma’aiktan kananan hukumomi za su kara tsananta wadannan matsaloli a kowace karamar hukuma.

Ba shakka dabarar  korar ma’aikata da zimmar samun kudin inganta ayyukan kananan hukumomi ba ta yi ba, domin kuwa  wata matsala ce da aka haddasa da gangan ake neman kawarwa, amma a sakamakon haka kuma ana janyo wasu matsalolin da ba za a samu mafita ba daga gare su cikin sauki.  Tsalle daya ake yi a shiga uku, ga shi nan kuma Gwamnatin el-Rufa’i ta yi, bisa ga dukkan alamu  za ta yi dubu saba’in ba ta fito ba.    

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara