Tsananin sanyi na kashe mutane a Afghanistan

Sakamakon zubar dusar kankara da tsanantar sanyi a Jihar Logar da ke Afghanistan, an bayar da rahoton rasuwar mutum biyar da ke zaune a wani sansanin masu neman mafaka. Kakakin Fadar Gwamnan Logar, Didar Ahmad Labang ya fada wa manema labarai cewa, an shafe tsawon kwanaki ana ta ruwan dusar kankara a jihar wanda hakan […]

Tsananin sanyi na kashe mutane a Afghanistan
Tsananin sanyi na kashe mutane a Afghanistan

Sakamakon zubar dusar kankara da tsanantar sanyi a Jihar Logar da ke Afghanistan, an bayar da rahoton rasuwar mutum biyar da ke zaune a wani sansanin masu neman mafaka.

Kakakin Fadar Gwamnan Logar, Didar Ahmad Labang ya fada wa manema labarai cewa, an shafe tsawon kwanaki ana ta ruwan dusar kankara a jihar wanda hakan ya janyo tsananin sanyi.

Labang ya ce muni tare da tsanantar sanyin ne suka haddasa rasuwar mutum biyar da ke zaune a sansanin masu neman mafaka na tsakiyar Logar.

Ya ce sakamakon sanyin an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a gundumomi da dama na Jihar Logar.