‘Tsananin so ya sa na yi wa budurwata wanka da ruwan batir’

Wani dalibi mai suna Alaci James Bako mai shekara 32 a duniya, wanda ya yi ta kokarin guje wa kamu bayan ya watsa wa budurwarsa ruwan batir ya zo hannu.Alaci James Bako wanda dalibi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a tsangayar kimiyyar siyasa ya ce tsananin son da yake wa budurwarsa mai […]

‘Tsananin so ya sa na yi wa budurwata wanka da ruwan batir’

 Kafin watsa wa Glady ruwan batirWani dalibi mai suna Alaci James Bako mai shekara 32 a duniya, wanda ya yi ta kokarin guje wa kamu bayan ya watsa wa budurwarsa ruwan batir ya zo hannu.
Alaci James Bako wanda dalibi ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a tsangayar kimiyyar siyasa ya ce tsananin son da yake wa budurwarsa mai suna Gladys Onwusoronyeh, wanda ita ma daliba ce a jami’ar ya sa ya watsa mata ruwan batir din.
Alaci James Bako ya shaida wa wakilinmu haka ne lokacin da jami’an tsaron jami’ar suka gabatar da shi ga Aminiya bayan kama shi.
Saurayin Alaci ya ce “Mun hadu da budurw ta Gladys Onuwusoronyeh a makaranta, kuma kodayaushe muna tare, kuma ina matukar sonta wanda idan ban ganta ba, ba na jin dadi. Ana cikin haka sai muka samu sabani sai na ga ta fara juya min baya, duk ta canja min. Na shiga damuwa, na rasa yadda zan yi da rayuwata, kusan duk na dimauce, karatuna ya fara zama wani iri duk na fara lalacewa. Sai na shiga tunanin yadda zan yi, daga nan sai zauciyata ta raya min cewa in kashe ta kawai in huta. To daga nan ne na yanke shawarar yi mata haka. Kuma na aikata mata ta zo, bayan na tanadi ruwan batir dina na boye bayan mun hadu kawai sai na watsa mata a fuska.”
Alaci Bako ya ce daga nan sai ya gudu, kuma duk abin duniya ya dame shi, ya rasa inda zai sa kansa, “Ina cikin tunani sai na gaya wa fastona cewa ga halin da nake ciki shi kuma ya ba ni shawara cewa in dai har tana nan, to in je in nemi gafararta ko na samu natsuwa, akwai ranar da na shigo mota na zo har Zariya domin in duba ta, amma sai na kasa sai na hau mota na koma, kuma ga shi yanzu na shiga hannu,” inji shi.
Aminiya ta waiwayi mahaifin dalibar Mista Christopher Onwusoroyeh inda ya ce farko ya yi bakin ciki ganin yadda yarinyata ta samu kanta a ciki; amma yanzu ya yi farin ciki, kuma ya gode wa Allah kuma yana yi wa shugabanin makarantar godiya, “Domin tun daga ranar da wannan abu ya faru suke ta dawainiya da mu har zuwa ranar da ’yata ta samu sauki, bayan zamanmu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, kuma sun dauke mu sun kai mu kasar Indiya inda aka je aka gyara wa yarinyata fuskarta domin da in dan ka dube ta, ta zama kamar kifi, yanzu kuwa ta kammala karatunta a yanzu haka tana Enugu tana yi kasa hidima,” inji shi.
Gladys Onwusoronyebudurwar da aka zuba wa ruwan batir, kwance a gadon asibitiYa ce sannan ba su zauna ba, har sai da suka kamo wanda ya aikata mata haka, don haka yana godiya, kuma ya ji dadi.
Shugaban tsaro na jami’ar Kanar AS Obuche (mai ritaya), ya ce a ranan 11/8/2011 da misalin karfe 8:30 na dare ne aka ce wata daliba mai suna Gladys Onwusoronyeh ta shiga wannan hali, “Kuma tun daga ranar muka fara daukar matakai daban-daban domin kamo wanda ya aikata hakan, amma Allah bai sa mun kama shi ba sai ranar Alhamis 15/8/2013, shekara biyu da kwana uku, kuma mun kama shi ne a garin Lakwaja cikin Jihar Kogi, don haka muka kira iyayen yarinya da ku don ku gan shi, kuma bayan mun gama bincike, za mu mika shi ga ’yan sanda,” inji shi.
Ya yaba wa shugabannin jami’ar a kan irin hadin kan da suke ba su wajan gudanar da aikinsu.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan