Tsangayar Adabin Hausa ta gudanar da taron kara wa juna sani

A kwanakin baya ne (20-12-2014, kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa maza da mata su 35, inda aka nuna musu hanyoyi da dabarun kasuwancin zamani da ilmin na’ura mai kwakwalwa da kuma kalubalen da ke cikin gyaran wayar salula.  A yayin taron, wanda ya gudana a Gidan Mambayya, […]

Tsangayar Adabin Hausa ta gudanar da taron kara wa juna sani
Tsangayar Adabin Hausa ta gudanar da taron kara wa juna sani

A kwanakin baya ne (20-12-2014, kungiyar Tsangayar Adabin Hausa ta gabatar da taron sanin makamar aiki ga matasa maza da mata su 35, inda aka nuna musu hanyoyi da dabarun kasuwancin zamani da ilmin na’ura mai kwakwalwa da kuma kalubalen da ke cikin gyaran wayar salula. 

A yayin taron, wanda ya gudana a Gidan Mambayya, a birnin Kano, masana sun gabatar da takardu ga mahalarta. Malam Nasiru Wada Khalil, a takardarsa mai taken ‘Matakan Kafa Kasuwanci Da Samun Nasara’ ya zayyano hanyoyin da ake bi a samu nasara a kasuwancin zamani. Ya nuna muhimmancin bincike da jajircewa da tunanin kawo wani abu sabo a matsayin hanyoyin kai wa ga nasara.
Injiniya Yunusa Muhammad kuwa a tasa takardar mai taken ‘kalubalen Da Ke Cikin Sana’ar Gyaran Waya,’ ya lissafo ire-iren kalubalen da ke cikin sana’ar gyaran waya da irin fadi tashin da masu sana’ar ke shiga a yau da gobe. Sannan ya bukaci gwamnati ta samar da wani tallafi na musamman ga matasa, domin samun ingantaccen ilmin gyaran wayar ta salula.
Takardar da danladi Haruna ya gabatar mai taken, ‘Ilmin Kwamfuta A Takaice’, ta bayyana yadda na’urar kwamfuta ke aiki da abubuwan da ta kunsa da kuma takaitaccen bayani a kan fasahar intanet. A karshe ya fadi cewa, ilmin kwamfuta ya zama wajibi ga kowa da kowa a wannan zamani.
Mahalarta taron sun nuna jin dadinsu game da ayyukan wannan kungiya. Da dama daga cikinsu, sun bukaci a sake samun wata rana domin a maimaita musu irin wannnan taron.
Shugaban kungiyar, Rabi’u Muhammad Abu Hidaya, ya gode wa Allah da Ya ba su ikon gudanar da irin wannan taron a karo na uku. Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba kungiyar za ta sake lalubo wani bangare daga al’ummar Hausawa domin ta ba su horo na musamman bisa al’amuran ci gaban rayuwa.
Sannan a karshen taron, kungiyar ta karrama wasu fitattun mutane da ke bayar da gudunmawa a fannonin rayuwa daban-daba, wadanda suka hada da, Dokta Abdulkadir Koguna, Sardaunan Agadez da Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) da Aminu Alan Waka. Haka kuma akwai Hajiya Bilkisu Yusuf Ali da Hajiya Lami Sumayya Murtala.
A jawabinsa na godiya kuwa a madadin wadanda aka karrama, Sardaunan Agadaz, ya yaba wa wannan kungiya da ke hobasa wajen bullo da abubuwan ci gaba a kodayaushe, sannan ya yi alkawarin ba da hadin kansa a dukan abin da kungiyar ta sa a gaba.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa