Tsangwama: An dawo da ’yan Najeriya 270 gida daga Afirka ta Kudu
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin dawowa da ‘yan Najeriya gida lafiya.
Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta karɓi ’yan Najeriya 270 da suka dawo daga Afirka ta Kudu.
Waɗanda suka dawo sun shiga shirin komawa gida da kansu.
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sa-kai 2 a Filato
- ’Yan sanda sun ceto mutum 5 daga hannun ’yan bindiga a Zamfara
NEMA ta ce sun yi rajista tare da kammala dukkanin gwaje-gwaje da ake buƙata kafin su dawo.
Sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Alhamis.
Jami’an NEMA, sauran hukumomin gwamnati sun tarbi waɗanda suka dawo, tare da taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.
Gwamnati ta kuma shirya motocin da za su kai su zuwa wuraren da suka nufa a sassa daban-daban na ƙasar.
An kuma tanadi motar asibiti da ma’aikatan lafiya domin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda ke buƙatar kulawar lafiya nan take.
NEMA ta ce wannan shiri an tsara shi ne domin tabbatar da dawowar ’yan Najeriya daga ƙasashen waje tana kasancewa cikin aminci, tsari, da mutunci.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da abokan hulɗa domin tallafa wa rayuwar waɗanda suka dawo da kuma taimaka musu wajen yin rayuwa cikin sauƙi.