Tsantsanta bauta ta sa wani mutum ya yanke ’ya’yan marainansa a Binuwe

Zan so a ce kowane mutum zai kasance kamar ni.

Tsantsanta bauta ta sa wani mutum ya yanke ’ya’yan marainansa a Binuwe

Anongo

An samu wani mutumin Jihar Binuwe mai suna Terhemen Anongo da yanke ’ya’yan marainansa biyu don gudun duniya da kuma kauce wa fadawa halaka.

Terhemen Anongo mai shekaru 44, wanda aka fi sani da ‘Doc K’ ko ‘Bob Korna’ a yankin Gboko na Jihar Binuwe, ya ce a yanzu rayuwa ta fi masa dadi bayan wannan hukunci da ya yanke.

A wata hira da ya yi da wakilinmu a Makurdi, babban birnin Jihar Binuwe, Anongo ya ce ba haka siddan ya yanke ’ya’yan marainansa ba sai dai ya yi hakan ne domin ya yi nesa-nesa da sha’awar ’ya’ya mata wanda hakan zai ba shi damar tsantsanta bauta ga Ubangijinsa ba tare da wani abu ya dauke masa hankali ba.

Tun a watan Maris na bara ne labarin Anongo ya bulla, a lokacin da ya yanke daya daga ’ya’yan marainansa da kansa wanda a sanadiyar haka ya kusa rasa ransa.

Sai dai bayanai sun ce da yake yana da kwanaki a gaba, wasu kwararrun likitoci da suka yi masa rubdugu wajen fahimtar halin bukata da yake ciki suka ceto ransa ta hanyar yi masa tiyata bayan ya yi asarar jini mai tarin yawa.

A ranar Litinin ta makon da ya gabata ce Anongo ya yanke dan marainansa na biyun, inda ya sake nanata cewa hakan zai ba shi damar tsantsanta bauta ga Ubangijinsa ba tare da mata sun dauke masa hankali ba.

Tarihi dai ya nuna cewa, tun a aji na biyar Anongo ya yi watsi da karatun likitanci da yake yi a Jami’ar Ibadan inda ya koma mai tura baro a yankin na Gboko.

“Na shiga Jami’ar Ibadan a shekarar 1996, kuma a shekarar 2000 har na ci jarrabawar da za mu tafi Asibitin Koyarwa na Jamiar domin karbar horo a kan makamar aiki, sai na yanke shawarar watsi da karatun saboda matsananciyar damuwa da nake fama da ita.

“A lokacin na daina sha’awar karatun gaba daya, sai dai kuma daga baya na yi kokarin komawa karatun amma mahukuntan jami’ar suka ce da ni ai ta faru ta kare.

“Na yanke dan marainan nawa na farko a ranar 10 ga watan Janairun 2021, sai dai an samu tangarda domin kuwa kwayoyin cututtuka sun shiga jikina, amma hakan bai hana na ci gaba da gudanar da harkokina ba har zuwa lokacin da na warke kuma yanzu garau nake don babu abin da ke damu na.

“A wancan lokaci ina aiki ne a wani Kamfanin Sufuri da ake kira Flight, amma sai suka sauya tsare-tsarensu na gudanarwa, wanda hakan ya sanya na ajiye musu aikinsu.

“A halin yanzu ina rayuwa ta cikin annashuwa da jin dadi kasancewar ina abokai masu kirki da suka rika kula da ni, akwai yan uwana mata da suka rika aiko min da abun alheri lokaci bayan lokaci.

“Na ajiye kayan abinci da dama a gidana, kuma duk lokacin da nake da wata bukata na kan tashi na girka da kaina. Na kuma rika biyan mutanen da suka kula da ni asibiti.

Dangane da dalilan da suka sanya ya yanke ’ya’yan marainansa, Anongo ya ce kasancewarsa mutumin da ya fito daga gidan da ake riko da addini, babu abin da ya sa a gaba sai riko da addinin nan da kuma ganin ya samu sakamako mai kyau a karatuttukansa.

“Akwai wata rana a kan hanyar komawa gida bayan na taso daga makaranta a Makurdi, sai na gamu da mutumin kirki mai suna Gbile Akanri, sai ya yi min daawar cewa na yi riko da Ubangiji da muhimmancin gaske.

“Sai dai ni mutum ne mai matukar son ya tsantsanta bauta ga Ubangiji amma kuma ina fama da matsalar sha’awa mai karfin gaske, kuma ba zan iya magancewa kaina wannan sha’awa mai karfi ba.

“Toh, akwai lokacin da karatu ya kai ni nassin kissar yadda Almajiran Yessu suka yi masa tambaya a kan sharadin mutum ko zai iya sakin matarsa, sai ya ce musu babu wani sharadi face mutum zai fada zina muddin ya saki matarsa.

“Wannan nassi da na karanta shi ya haska min na fahimci daga jikin namiji aka fitar da mace, saboda haka duk wani namiji ba zai iya rayuwa ba tare da mace a tare da shi ba.

“Saboda haka kamar yadda ya zo a cikin nassin da Littafi Mai Tsarki (Bible) ya kawo, Manzo Bulus ya ce babu wanda zai ki jikinsa, duk wanda ya ki matarsa kamar ya ki jikinsa ne, domin a hade suke da juna.

“Na karanta tarihin mabiya addinin Kirista na farko-farko, kuma na gano cewa akwai wani mutum a wancan zamanin da ake kira Oregon a Armateus da yanke ’ya’yan marainansa don gudun kada a rika zarginsa na mufurci da kowacce irin siga.

“Ni a karan kaina ba ni da raayin yin aure, amma kuma ban dauki aure a matsayin wani abu mara kyau ba.

“Dalilin da ba zan yi aure ba kuwa shi ne ina daya daga cikin almajiran Manzo Bulus, wanda ya ayyana cewa abu ne mai kyau a yi aure, amma kuma mafi kyau shi ne mutum ya zauna ba tare da ya yi aure ba don hakan shi zai ba shi damar tsantsanta bauta ga Ubangiiji ya kuma sadaukar da komai na shi dari bisa dari zuwa ga bauta,” a cewar Anongo.

Dok K wanda ya fito daga Karamar Hukumar Tarka a Jihar Binuwe, ya ce ya so a ce kowane mutum zai kasance kamar shi, inda ya bayyana wa wakilinmu cewa da zarar ya warke daga tiyatar cire dan marainan nasa, zai kuma bude shagon sayar da kayayyakin masarufi sannan kuma ya rika yi wa mutane wa’azi kan muhimmancin tarewa a fadar Ubangiji.