Tsantsar jahilci ne zai sa uwa kawalcin ’ya’yanta ga ’yan bindiga

Ra’ayoyin jama’a kan wata mata da ke kai wa ’yan bindiga ’ya’yanta suna lalata da su.

Tsantsar jahilci ne zai sa uwa kawalcin ’ya’yanta ga ’yan bindiga

Gidajen karuwai

Ra’ayoyin jama’a sun bambanta kan abin da ya sa wata mata da aka kama take yin kawalcin ’ya’yanta ga ’yan bindiga suna lalata da su.

A ranar Lahadi ne Aminiya ta fitar da bidiyon yadda wata matar aure ke safarar ’ya’yan cikinta zuwa cikin daji inda ’yan bindiga suke lalata da su suna biyan su.

Bayan wallafa bidiyon matar tana jawabi da kanta a shafin Aminiya na sada zumunta ne jama’a suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan danyen aikin da matar ta yi.

Wasu daga ciki na ganin bakin talauci ne ke jefa mutane a irin wannan danyen aiki, akwai kuma masu ganin tsantsar jahilci da rashin sani kimar kai shi ke sa masu irin wannan danyen aiki fadawa cikin wannan halaka.

A tsokacinsa kan wannan tabargaza da matar ta yi, Rabiu Muhammad ya bayyana cewa, “Wallahi talauci ne da yunwa da rashin tauhidi da rashin dogaro ga Allah” ne ya sanya ta a wannan mugun aiki.

A take kuma aka samu wadansu suka goya masa baya tare da karfafa cewa har da ma tsantsar jahilci da rashin imani a cikin abun da ta yi.

Shi kuma Bashir Ilyas Maishuni, cewa ya yi, “Akwai babban aiki a kan jami’an tsaronmu duba da yadda mutanen da ba a tunanin za su samu wata alaka ta kai tsaye da irin wadannan mutane amma sai ga shi an same su da hannu dumu-dumu ba tare da jin tsoron Allah ba.”

Ya kara da cewa, “Dole ne jama’a su farka su tashi tsaye domin daukar kakkyawan mataki a kai.

“Da yawa daga cikin garuruwan da ake wannan abubuwan sun san [masu garkuwan] kuma wasu ma ’yan uwansu ne, kuma sun kasa tona masu asiri.”

Har ila yau ya ce, “Wasu sukan ki tona asirin [ne] saboda ana ba su kasonsu na irin kudin da ake samu ko kuma saboda suna tsoro abin da zai iya biyo baya.”

Ko a ranar 21 ga watan Disambar 2021, Rundunar ’Yan Sanda ta musamman (IRT) ta kama wani saurayi da budurwa da ake zargi da yi wa ’yan bindiga da ke Dajin Galadimawa kawalcin mata.

Matsalar ’yan bindiga a Arewacin Najeriya dai ta ki ci, ta ki cinyewa duk da irin kiraye-kiraye da ake yi wa hukumomin tsaro ta kowane bangare da kuma kokarinsu na magance matsalar.