Tsarabar Azumin Ramadana (2)

WAJABCIN ZAKKAR KONO1.Zakkar kono wajibi ce akan kowanne daya daga cikin Musulmi, babba, Namiji ko Mace, da, ko Bawa.An samo Daga dan Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) Ya ce “ya wajabta Zakkar kono daga Ramadana Sa’a”I daga dabino, sa’i daga Sha’ir, akan Bawa ko da, Mace ko Namiji, karami, […]

Tsarabar Azumin Ramadana (2)
Tsarabar Azumin Ramadana (2)

WAJABCIN ZAKKAR KONO
1.Zakkar kono wajibi ce akan kowanne daya daga cikin Musulmi, babba, Namiji ko Mace, da, ko Bawa.
An samo Daga dan Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce, “Manzon Allah (S.A.W) Ya ce “ya wajabta Zakkar kono daga Ramadana Sa’a”I daga dabino, sa’i daga Sha’ir, akan Bawa ko da, Mace ko Namiji, karami, ko babba, daga Musulmi”.
Malamai sunyi dai-daita akansa
2. Hikimar shar’antata: Domin ta kasance tsarkaka ce, daga mai AZUMI, daga abinda ya Auku gareshi, na daga yasassar Magana,ko Fasikanci, kuma domin Taimakawa ga talakawa da masu Uzuri.
3. Gwargwadon ta: Sa’i daga Alkama, ko Sha’ir, ko Zabibi ko Dabino,ko Shinkafa, ko Cukwi (wato Nono busashe, ko maka Mancinsa, wanda ya ya sance abincin mutanen garin.
4. Lokacin fitar da ita: mafificin lokacin fitar da ita shi ne, kafin Sallar Idi, ya inganta a fitar da zakkar kafin Sallah da kwana daya ko kwana biyu, amma ba ya halatta a Jinkirta zuwa bayan Sallar Idi, domin fitar da ita bayan sallah, to ta zama wata Sadaka daga cikin sadakoki.
5. Rabonta: ana rabata ga Talakawa, da Miskinai, da masu aiki akanta, da wurin ‘yantar da wuya, da wanda ake rarrashin zukatansu, da masu bashi, da cikin daukaka kalmar Allah, da dan tafarki: (wato matafiyin da bashi da abinda zai kai shi garinsa)
Duba fikihussunna Jiz’i na 1 ( 412)
 
Sallar Idi Biyu Acikin Masallaci
Manzon Allah (S.A.W) Ya kasance Ya na fita ranar Sallar Azumi da Sallar Layya Zuwa Masallaci, farkon abinda Yake farawa da shi Sallah. Imam Bukhari Ruwaito shi
Manzon Allah (S.A.W) Ya ce: kabbara cikin Sallar Azumi, bakwai a ta farko. biyar a ta karshe, da karatu a bayan dukkansu biyun.
Wannan Hadisin Mai kyaune  Abu Dawuda ya ruwaito shi.
Manzon Allah (S.A.W) Ya Umarci mu da mu fita dasu cikin Sallar shan ruwa da Sallar Layya: ‘yantatu, da masu haila, da Mata ma’abota Aure to amma masu haila sai su kauracewa Sallah, zasu halarci alhairi, da Addu’oin Musulmi, sai nace ya Manzon Allah (S.A.W) dayan mu bata da jalbaba? Sai Ya ce “Yar uwarta ta sanya mata”
malamai sun dai-daita akansa
Annabi Ya kasance idan Ya wayan gari ranar Sallar Azumi, sai Ya ci dabino, kuma yana cinsu ne a wutiri.
Bukhari ya ruwaito shi.
(Shi wutiri yana daukar adadi kamar haka (1,3,5,7,9)
ABUBUWAN DA AKA AMFANA DA SU DAGA WAdANNAN HADISAI
1. Sallar Idi guda biyu Sha’rantacciya ce, kuma raka’a biyu ne, mai kabbara a cikin raka’ar farko sau bakwai, da kabbara biyar a ta biyu, sannan ya karanta fatiha, da abinda ya sawaka gareshi.
2. Sallar Idi tana kasancewa ne a Masallacin Idi, shi ne wani wuri kusa da Madina ya kasance Manzo (S.A.W) yana fita zuwa gare shi, don Sallar Idi biyu, Yara, da Mata, da ‘Yan Mata, hadda Mata masu Uzurin haila.
Hafiz ya ce cikin Fathul Bari: “Kuma cikinsa akwai fita zuwa Masallaci, Idi baya kasan cewa acikin Masallaci, sai bisa larura”
3.Yana karfafa kabbara a daran Idin karamar Sallah, yana karewa ne da karewar Sallar Idi Allah Madaukakin Sarki Ya ce;
Kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan ya shiryarda ku, kuma tsammaninku, za ku gode.
Suratul Bakara 185
BIDI’O’IN CIKIN IDI
1.Ziyarar kaburbura: Ibadar Ziyarar kabari bata cikin ranakun Idi, wanda babu wani dalili na ke~atata da ranar Idi.
2. Cakuda: Mata da Maza suna cakuda cikin Makabarta, Manzon Allah (S.A.W) Ya ce “Ban bar wata fitina ba a bayana wanda take cutar da Maza ba, kamar Mata”
 Malamai sun dace akansa
3. Karatun alkur’ani: hani yazo akan karatunsa a cikin Makabarta, Saboda Manzo (S.A.W) Ya ce “kada ku mayar da gidajen ku kamar Makabarta, lalle gidan da ake karanta Suratul bakara shaidan yana gudun sa”.
Muslim ne a ruwaito shi
 4.  Kuma lokacin da Manzon Allah ya tsaya a kan kabarin SahabbanSa, sai Ya ce musa “ku nemi gafara ga [an Uwanku, kuma ku rokar masa tabbatuwa domin yanzu ana tambayan sa ne”
Wannan Hadisin Ingantacce ne Hakim ne ya ruwaito shi
Kuma Manzon (S.A.W) Ya sanar da SahabbanSa, idan suka shiga Makabarta su ce: “Aminci ya tabbata a gareku Ma’abota gidan nan daga Muminai, da Musulmai, kuma mu ma in Allah Ya so zamu Iskeku, muna rokon Allah Da mu da Ku lafiya” (ai daga azaba).
Muslim ne ya ruwaito shi
Daga Littafin
SIYAMU RAMADANA: Fada’iluhu, Adabuhu, Ahkamuhu, {iyamuhu. Na Jameel Zainun
Makarantar Darul Hadis, Al-khairiyyah Makatul-Mukaramah.
 Nata’ala Sambo Babi (NASABA) 08063673656, 08096967800

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya