Tsare mutanenmu a Zariya ya saba wa yarjejeniyarmu da gwamnati – Shugaban Darul Islam
Shugaban ’yan Darul Islam ta kasa Malam Bashir Abdullahi Sulaiman ya ce tsare mutanensu 10 ’yan sanda suka yi a garin Zariya yin karan-tsaye ne ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a tsakanin Gwamnatin Tarayya da Darul Islam shekara bakwai da suka gabata.Shugaban ya shaida wa Aminiya a Kano cewa, tabbas mutanen da aka […]
Shugaban ’yan Darul Islam ta kasa Malam Bashir Abdullahi Sulaiman ya ce tsare mutanensu 10 ’yan sanda suka yi a garin Zariya yin karan-tsaye ne ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a tsakanin Gwamnatin Tarayya da Darul Islam shekara bakwai da suka gabata.
Shugaban ya shaida wa Aminiya a Kano cewa, tabbas mutanen da aka tsare a Zariya ba ’yan Boko Haram ba ne, ya ce mutanen Darul Islam ne. Malamin ya ce, a tsawon shekara 16 da wata bakwai da kafuwar Darul Islam a Najeriya, ba inda aka taba samunsu da laifi ko zargin tashin hankali hasali ma inji shugaban a kullum su suke jaddada alfanun zaman lafiya ga zamantakewar al’umma.
Shugaban ya kara da cewa tunda aka tashe su daga mazaunin Darul Islam a shekarar 2009, suka kudiri aniyar bin yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsu da gwamnati sau da kafa. “Gaskiya mun dade muna fuskantar tsangwama daga hukumomin tsaro, amma mun yi dubi da yanayin da kasa ta tsinci kanta a cikin ’yan shekarun baya, muka yi wa hukumomin uzuri. Kuma lokacin da na samu labarin an tsare mana mutum takwas a Zariya, na tura wani mutum don ya binciko mana laifin da suka yi. To amma sai muka ji shiru, na sake tura wani sai kawai muka ji labarin wai an kama ’yan Boko Haram mutum goma a Zariya. Wannan a gaskiya ya saba wa yarjejeniyar da muka kulla tsakaninmu da Gwamnatin Tarayya a kan zaman lafiya. An je inda suke zaune an kuma tabbatar da cewa suna zaune a wannan wuri kimanin shekara bakwai, wato tun lokacin da aka tashe mu a shekarar 2009, ba wani tashin hankali tsakaninsu da jama’a,” inji Shugaban.
Shugaban ya ce tunda aka taso su daga inda suke, wadansu daga cikin ’ya’yan kungiyar ke fuskantar tsangwama a akasarin wuraren da suka koma; ya ce ana ta yada jita-jita marasa dadi a kan ’yan kungiyar wanda hakan ya sa hukumomin tsaro ke yawaita takura musu. “Mutanen nan da aka tsare, a fa masallaci aka kame su suna gudanar da ibadarsu ba a kuma kama su da komai ba na nau’in makami. Shin tsarin yarjejeniyar da muka shafe shekara bakwai, muna bi sau da kafa ta rushe ne? Idan har wadansu daga cikinmu sun aikata wani laifi, sai a sanar da ni a matsayina na shugaba. To amma ba a yi haka ba. Ina amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki wadannan bayin Allah domin tabbatar da adalci da kuma mutunta yarjejeniyar da aka kulla shekara bakwai baya,” inji Shugaban na Darul Islam.