Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu da suka tayar da ƙura

Da wuya a yi wata guda ba tare da Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da wani sabon tsari ko mataki da ya haifar da ce-ce-ku-ce, a wani lokaci har da zanga-zanga a Nijeriya ba

Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu da suka tayar da ƙura

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi ƙaurin suna wajen ɓullo da tsare-tsare masu cike da ruɗani da jawo ce-ce-ku ce a tsakanin ’yan Nijeriya.

Tun a jawabinsa na farko a wurin karɓar rantsuwar fara aiki ya fara tayar da ƙura. Ba a yi minti 10 da rantsar da shi ba ya yi sanarwarsa ta farko da ta girgiza ’yan Nijeriya kuma har yanzu suna magana a kanta.

Daga tun lokacin da ya yi sanarwar soke biyan tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayun 2023 yanzu ’yan ƙasar na maganganu kan tasirinta, tare da ɗora mata laifin matsalolin tattalin arziƙin da suka yi wa ƙasar ɗaurin huhun goro.

Bugu da ƙari, da wuya a yi watanni ba tare da wani sabon mataki ko tsarin gwamnati ya haifar da ce-ce-ku-ce, da wani lokaci ke kaiwa ga zanga­zanga ko zazzafar muhawara da dai sauransu ba. A halin yanzu ma ƙasar ta yi makonni da ɗaukar zafi kan ƙuduronin Dokar Haraji da shugaban ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa, baya ga wasu tsare-tsare da gwamnatinsa ta ɗauka da ’yan ƙasar ke nuna wa yatsa.

Duk da haka, wasu daga cikin waɗannan dokoki da tsare-tsare ko matakai, suna daga alƙawuran yaƙin neman zaɓe da ya ɗauka a 2023.

Ga wasu daga cikin matakai da tsare-tsaren shugaban da suka haddasa muhawara ko kakkausan suka:

Janye tallafin mai

Janye tallafin man fetur ne tsarin Shugaba Tinubu na farko da ya ke ci gaba da gwara kan masana da ’yan ƙasa ke ganin babu abin da ya janyo sai wahala, saboda ta sa farashin litar fetur ninkuwa aƙalla sau 10 daga N190 zuwa 1,200 wanda hakan ya tilasta yawancin masu ababen hawa komawa hawa shiga na haya.

Ba iya ce-ce-ku-ce ku ce ba, har yajin aiki ƙungiyar ƙwadago ta shiga don menan ya lashe amansa amma ya ce sam, amma ya yi alƙawarin ɓullo da wasu tsare-tsare da ya ce za su rage raɗadin janye tallafin.

Sai dai har ya zuwa yanzu ’yan ƙasar na kukan cewa ba su gani a ƙasa ba. Hasali ma, suna danganta matsalar hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwanni da janye tallafin da aka yi. Akwai kuma waɗanda suka gwammace ya riƙe tallafin da ya yi alƙawari ya dawo da na man.

Ƙarin mafi ƙarancin albashi

Wani abin da ya tayar da ƙura shi ne batun ƙarin mafi ƙarancin albashi inda ƙungiyar ƙwadago ta dage cewa tunda gwamnatin ta janye tallafin ma to dole yi wa ma’aikata ƙarin albashi daidai da yadda farashin kaya suka tashi, inda suka sharɗanta ƙarin mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N600,000 amma gwamnatin ta ƙi, daga ƙarshe aka daidaita a kan Naira dubu 72,000.

An daɗe ana kwan-gaba-kwan-baya kan lamarin, inda ƙungiyar ƙwadago ke zargin gwamnati da yaudara kain da karshe su sasanta.

Sai dai har yanzu akwai jihohin da ba su fara aiwatar da wannan ƙari ba, har sai da ƙungiyar kwadago ta shiga yajin aiki — haka ma kamfanoni masu zaman kansu.

Mayar da sassan Bankin CBN Legas

Surutai sun biyo bayan mayar da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Legas, inda musamman a Arewa ake zargin gwamnati da ƙoƙarin ɗauke Babban Birnin Tarayya zuwa Legas. Masu wannan zargi na ganin babu dalilin mayar da sassan Legas, domin tun farko a can hedikwatarsa take kafin aka dawo da ita Abuja, sabon birnin tarayya a zamain mulkin soja na Ibrahim Badamasi Babangida.

Bayan ƙurar da lamarin ya tayar gwamnatin ta yi bayanin cewa an yi haka ne saboda sauƙaƙa aiki da rashe kuɗaɗen da ake ba ma’aikatan sashen domin tafiye-tafiye a duk mako ko wata zuwa Legas, inda aka fi buƙatar aikinsu.

Bankin ya kuma ƙaryata zargin da cewa zai mayar da hedikwatarsa Legas. Amma dai har yanzu dai bankin na Abuja.

Rancen kuɗin karatu ga ɗalibai

An ɓullo da sabon shirin ne don taimaka wa ɗalibai musamman marasa galihu su ci gaba da karatunsu zuwa duk matakin da suke so.

Sai dai shi ma ya zo da nasa ƙalubalen, ciki kuwa har da sharuddan da aka gindaya wa waɗanda za su ci moriyar, da takaita shi ga daliban jami’o’in gwamnati da kuma yadda kusan za a ce tun bayan sanya wa dokar hannu har yanzu, ɗaliban da suka amfana ba su taka kara sun karya ba.

Akwai kuma masu tunanin ’ya’yan masu uwa gindin murhu ne kawai za su amfana, amma dai bisa abin da ya bayyana bayan fara ba wa daliban kuɗaɗen, wanann zargi ba shi da makama.

Soke tsarin ‘cashless’

Watsi dag gwamnatin ta yi da tsarin soke tsoffin takardun kudi da kuma taƙaita amfani da takardun kuɗi ya faranta ran ’yan Nijeriya, saboda irin baƙar wahala da aka sha lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ta ɓullo da tsarin tare da canja takardun N200 da N500 da kuma N1,000, wanda har bore mutane suka yi a bankuna domin ganin tsohuwar gwamnati ta tsoke dokar amma ta ƙi.

Wasu gwamnoni sun kai ƙara babban kotun tarayya inda ta yanke hukuncin dakatar da dokar, kuma gwamnatin Tinubu ta bi hukuncin kotun aka ci gaba da amfani da sabbin da kuma tsaffin takardun kuɗaɗen a tare.

Ƙwace aikin titin Abuja-Kaduna

Aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna da gwamnati ta yi daga hannun kamfanin Julius Berger bai yi wa wasu daɗi ba a yayin da wasu kuma ke ganin hakan shi ne mafita. Ministan Aiyuka Daɓid Umahi ya ce an ƙwace aikin ne saboda tafiyar hawauniyar da kamfanin ke yi na tsawon shekaru da kuma neman ƙarin kuɗi sama na Naira tiriliyan ɗaya.

Gwamnatin Buhari ce ta bayar da aikin a wa’adinsa na farko, amma har ya aikin bai kammalu ba, hasali ma, an dakatar da aikin bayan kamfanin ya nemi ƙarin kuɗi da kuma matsalar tsaro.

Duk da cewa an kammala ɓangaren aikin da ya tashi daga Kaduna zuwa Kano, ɓangaren Abuja zuwa Kaduna wanda shi ne mafi gajarta, ya gagara, kuma shi ne a makonnin baya ministan ya ƙwace zai bai wa wani kamfani.

Al’ummar Arewa dai ba su ji daɗin tsaikon aikin ba, kuma har yanzu akwai masu ganin da wuya a kammala a zangon farko na Tinubu.

Màikatar kiwon Dabbobi

An ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar ce da mufin kawo inganta harkar kiwon dabbobi domin cin maroiyarsa ta fannin tattalin arziki da kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya.

Ministan ma’aikatar na farko, Idi Muktar Maiha, a kwanakin baya ya bayyana irin ɗimbin alfanu da ke tattare da ma’aikatar, inda ya yi alƙawarin magance mafi yawan matsaloli da ke addabar makiyaya da manoma musamman a yankin arewa.

A baya wasu sassan ƙasar nan sun nuna baƙar adawarsu ga shirin gwamantin Buhari na shirin (RUGA) da cewa bai kamata ta shiga ciki ba tunda kiwo kasuwanci ne.

Yanzu dai da alamar ma’aikatar dabobin ta asmu karɓuwa kuma ana sa ran za ta taimaka taimaka wajen tsugunar da makiyaya a koya masu yadda ake kiwo na zamani.

Yanke wutar lantarkin Nijar

Barazanar yaƙi da rufe iyaka da kuma yanke wutar lantarki da Nijeriya ke ba wa Jamhuriyar Nijar da Tinubu ya bayan sojojin Nijar sun yi wa shugaban ƙasarsu Mohammed Bazoum juyin mulki ya haifar da zazzafar muhawara.

Bayan sojojin sun ƙi bin umarnin Ƙungiyar ECOWAS na dawo da Bazoum kan kujerarsa ne, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Tinubu da ke jagoranta ƙungiyar ya yi barazanar yin amfani da ƙarfin soji wajen dawo da Bazoum, ya kuma yanke wutar ƙasar tare da rufe iyakarta da Nijeriya da nufin tilasta wa sojojin bin umarnin ECOWAS.

Hakan ya matuƙar kaɗa hantar manyan Arewa domin ’yan yankin sun ɗauki kansu ’yan uwan Nijar saboda al’adunsu da yare da addini da auratayya sun haɗa su.

A ƙarshe malaman Musulunci daga Nijeriya suka shiga tsakanin wajen ganin ba a yi yaƙin ba a yayin da ’yan Arewa ke zargin Tinubu da neman kai hari domin raba zumuncinsu, zargin da gwamnati ta musanta.

’Yancin ƙananan hukumomi

An kwashe shekaru gwamnatoci na ƙoƙarin ba wa ƙananan hukumomi ’yancinsu musamman na samun kuɗaɗensu kai-tsaye daga Asusun Gwamnatin Tarayya ba tare ad nasara ba, sai a zamanin Tinubu.

Amma hakan bai yi wa gwamnoni daɗi ba, kasantuwar dama su ke amshe kuɗaɗen ƙananan hukumomi, don haka suka kai ƙara amma suka sha kaye a Kotun Ƙoli, lamarin da ya matukar faranta ran ’yan ƙasa da dama.

Ganin cewa Kotun Ƙolin na shirin mayar da zaɓen ƙananan hukumomi hannun Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), gwamnoni suka yi rige­rigen gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a wasu jihohi, inda ake zargin sunyi ɗauki-ɗauran yaransu ne domin su ci gaba da yin yadda suka ga dama da kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Kudirin dokar Haraji

Wannan batu na ci gaba da ɗaukar hankali duk kuwa da cewa Majalisar Dattawa ta tura shi ga kwamiti da zai yi nazari tare da gyara duk wani sashe da ke da buƙatar gyara.

Wanann doka ta sha kakkausn suka daga Arewa da kuma zargin shirin cutar da yankin.

Tun daga lokacin da Tinubu ya miƙa ƙudirin ga Majalisar ake ta ce-ce-ku-ce- inda gwamnoni da sarakuna da ’yan majalisar dokoki na ƙasa daga Arewa da ke ganin dokar za ta cutar da yankin, zargin da gwamnatin tarayya ta ce ba gaskiya ba ne.

Rage ’yan rakiyar shugaban ƙasa

’Yan Najeriya sun yi ta surutai kan yawan tawagar da ke raka shugaban kasa musamman a tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje. Wannan lamari ya fi ƙamari a lokacin wani taron kasashen waje da ’yan Nijeriya suka ga jerin sunayen wakilan ƙasar sun haura 100, alhali tana fama da matsalar tattalin arziki da tulin bashi.

A sakamakon kakkausan, shugaban ƙasar ya sanar da zaftare yawan ’yan rakiyarsa da na ministoci zuwa motoci hudu. Sai dai kuma zuwa yanzu dai babu alamar ana amfani umarnin.

Ƙarin albashin alƙalai

A watan Augusta ne shugaban ƙasa ya miƙa buƙatar ƙara albashin alƙalai da kashi 300 ga Majalisar Tarayya wadda kuma ta amince ba tare da ɓata lokaci ba, lamarin da shi ma ya janyo surutai a wajen ’yan ƙasa, inda suka ce ya wuce misali idan aka yi la’akari da albashin sauran ma’aikatan gwamnati da kuma mafi ƙarancin albashi.

Titin Legas zuwa Calaba

Aikin da Tinubu ya bayar na gina katafaren titin Legas-Kalaba-Sakkwato ya jawo surutai, musamman ganin cewa ba a taɓa ba a da aikin hanya da ya kai shi tsada ba, alhali gwamnatin tana kukan rashin kuɗaɗe ga kuma bashi.

A watan Okctoba ne Ministan Ayyuka Daɓid Umahi ya sanar da cewa za a kammala ɓangaren farko na aikin titin Laƙas zuwa Calaba mai nisan kilomita 700 a watan Mayun 2025.

Umahi ya ce za a kwashe kusan shekaru biyar zuwa 10 kafin a maido da kudaden da aka kashe a aikin, wanda kamfanin Hitech Construction ya fara tun a watan Maris.

Tsarin rabon CNG

Batun tsarin amfani da gas ɗin CNG a ababen hawa har yanzu ’yan Najeriya na cewa ba sun inda aka dosa ba, domin kuwa baya ga tsadar sauya ababen hawa daga shan fetur zuwa CNG, tun daga lokacin da aka kaddamar da fara amfani da CNG bayan an janye yallafin feturs har yanzu masu amfani da shi ba su taka kara sun karya ba. Wuraren da aka buɗe domin rika canza wa masu ababen hawa da ke da bukatar CNG ba su da yawa, a wasu johihin ma babu, sannan har yanzu masu ababen hawa ba su gama amincewa su koma amfani da CNG ba.

Bambanta masu amfani da wutar lantarki

Tsarin rukunin Band A da B da C na wutar lantarki ya jawo zazzafar muhawa, inda musamman Sanata Ali Mohammed Ndume ya yi uwa ya yi makarɓiya cewa harmatacce ne domin ba shi da muhalli a kundin tsarin mulki.

Tsarin ya yi tanadi bayar da wuta na aƙalla awa 20 ga waɗanda ke Band A, tare da kara musu kuɗin wutar, su kuma ragowar aka bar su a yadda suke.

Ana kuma sukan tsarin da cewa ya fifita unguwannin masu kuɗi, kuma duk da sukan tsadar, an rage kudin wutar. Kazalika, har yanzu matsalar karancin wutar lantarki ga kuma ƙarin kudin wuta da aka yi sunan nan aka kuka da su.

Tallafin janye tallafin fetur

Aƙalla Naira biliyan 5 gwamnatin tarayya ta ba wa kowace jiha a matsayin tallafin rage wa mutanen ta raɗaɗin janye tallafi fetur. Wasu jihohin har ya zuwa yanzu sun kasa yin bayanin yadda suka raba kuɗaɗen da kayayyakin duk kuwa da cewa sun ce wai sun sayi shinkafa ne suka bai wa talakawa.

Ma fi yawan talakawa sun ce ba su ga komai ba dangane da shinkafa da aka cewa za a saya a raba masu, wasu kuma sun ce bai fi mudu hudu aka raba masu ba.

Digiri ɗam Kwatano

Bayan wani ɗan jaridar mai bin cike kwakwaf ya gno cewa akasarin shaidar kataun digirin da ’yan Najeriya ke yi akwatano ba su inganci, Ma’aikatar Ilimi ta sanar cewa sai an tantance duk masu amfani da digiri ƙasar Jamhuriyar Benin, domin ware waɗanda Nijeriya ba ta amince da ingancinsu ba.

A yanzu haka an fara korar wasu ma’aikatan da suke am amfani da takardun digirin jami’o’in da abin ya shafa wajen neman aiki.

 

 

 

 

 

 

 

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja