Tsarin 5G zai bunkasa amfani da Intanet – Dambatta

Babban Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya wakilci Nahiyar Afirka a daya daga cikin manyan tarurrukan duniya da ya gudana kwanan nan na Kungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU) a birnin Budapest na kasar Hungry. Shugaban Hukumar ya bayyana shirin da Nahiyar Afirka ta yi dangane da yin amfani da tsarin […]

Tsarin 5G zai bunkasa amfani da Intanet – Dambatta

Farfesa Umar Garba Dambatta Shugaban Hukumar NCC

Babban Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya wakilci Nahiyar Afirka a daya daga cikin manyan tarurrukan duniya da ya gudana kwanan nan na Kungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU) a birnin Budapest na kasar Hungry. Shugaban Hukumar ya bayyana shirin da Nahiyar Afirka ta yi dangane da yin amfani da tsarin kimiyyar 5G a nahiyar a taron. Ya gabatar da takarda mai taken: TSARIN 5G: TSARIN DA ZA A YI AMFANI DA SHI:

Kafin in fara bayar da gudunmawata a kan wannan maudu’i ya kamata mu duba yadda ake amfani da tsarin 5G. Akwai nau’o’i uku da suka hada da karfafa yin amfani da jadawalin wayar salula da karancin wanda ake dogara da shi da karancin manhaja da kuma tsarin manhajar alakar na’ura da na’ura.

Ina tsammanin wadannan su ne duniyar da muke nema a matsayin muhimman wuraren amfani da tsarin. Amma wanda kasashen Nahiyar Afirka za su yi amfani da shi cikin gaggawa shi ne tsarin karfafa yin amfani da Intanet ta manhajar wayar salula.

Dalili shi ne kasashen Afirka suna kokarin sanya kayayyakin aikin shiga Intanet don samar da manhajar shiga Intanet. Shi ya sa yin hakan zai karfafa mu wajen tabbatar da ganin mun sanya kayayyakin da suka zama wajibi.

Dangane da matsayin shirin da kasashen Afirka suke yi na yin amfani da tsarin 5G

Mene ne matsayin shirinmu?

Muna kokarin mu adana zangon yin amfani da Intanet. Musamman a Najeriya muna magana a kan nau’o’i uku na gigahaz; 26 da 38 da 48 GHz. Wadannan zanguna suna nan amma ba mu yi musu lasisi ba don wata manhaja.

Muna jiran kammala aiki a kan tsarin a tashar sadarwa ta kasa da kasa da ke kasar Masar sannan mu ga yadda za mu yi wa zangunan uku lasisi kamar yadda na fada.

“Daya daga cikin muhimman matakin da kasashen Afirka suke dauka shi ne magance sabuwar fargabar tashoshin da ke barazana ga tarbiyya da mu’amalar al’umma da ke da alaka da wannan kimiyya ta 5G.

Akwai fargabar sanya ido kuma saboda  tsarin da muke da shi a baya duk wani tsarin da muke amfani da shi mukan sanya shi a matsayin na gwaji. Haka ma tsarin kimiyyar 5G ba ta zama ta daban ba za mu gwada ta kuma shirye-shirye na tafe don yin wannan muhimmin gwaji. Baki daya, dalilin yin gwajin shi ne don mu gano kwalubalen da ke tattare da tsarin. Kalubalen tsaro da irin karfin sinadarin da zai rika sauka, za mu duba mu ga ko ya dace da tsarin sanya ido na kasa da kasa na sinadarin sadarwa da kuma tabbatar da duk wani abu da muke son ganowa da suka danganci harkokin cinikayya da ke da dangantaka da tsarin na 5G. Hakan yana gudana a Najeriya. Matakan da muke dauka yayin gwajin zai hada da hukumomin tsaro wadanda suke da ta cewa a kan harkokin tsaro a kan wannan sabuwar kimiyya yayin da aka fara yin amfani da tsarin. Muna so mu tabbatar da an dama da su a yayin gwajin don bayar da shawarar da ta dace kan abin da ya shafi tsaro da za mu yi amfani da su wajen tsarin sanya idon wadanda za su taimaka wajen yin amfani da tsarin idan aka fara samun kudin shiga daga gare shi.

Kasashen Afirka suna musayar bayanai da dabaru a kan abin da suke gani kasancewar tsarin 5G zai bunkasa yin amfani da yanar gizo a wayar salula a daidaikun kasashe tare da magance fargabar ’yan kasa ta hanyar yi musu bayanan da zai kwantar musu da hankula dangane da fargabar da suke da ita kan tsarin.

Shin ko kasashen Afirka sun shirya nan da shekara 2020 na amfani da tsarin 5G, wannan wani abu ne da ba zan iya amsawa ba nan take amma na san yanayin shirinmu shi ne na samun adana zangon tsarin a wasu kasashe masu yawa ana ta gwaji a wasu kasashen Afirika kuma kasar Najeriya ta shirya tsaf don yin gwaji.

Kan rashin hadari da batun tsaro da masu ruwa-da-tsaki suka nuna

“Muna bukatar samun dabara kan yawan karfin lantarkin da tsarin ke tattare da shi, na’urar da muke son yin amfani da ita musamman idan aka yi la’akari da yawan karfin lantarkin yin amfani da tsarin 5G ke janyowa. Ina maganar miliyoyin na’urorin a yanki kilomita daya zuwa kilomita daya kuma mafiyawan wadannan abubuwa na’urori ne da ake amfani da su a gidaje. Ina tunanin za a nuna damuwa dangane da ko babu hadari dangane da shi.

Wadanda suka kirkiro wannan kimiyya suna cewa ba wani hadari amma masu sanya ido suna cewa ya kamata a duba don a baiwa masu amfani da shi tabbacin ba shi da wani hadari.

Haka nake cewa dangane da magance farfabar da aka nuna dangane da tsaro da kunshin data da kuma sirrin masu amfani da shi. Kuma hakan za a iya tantancewa kawai ta hanyar gwaji. Shi ya sa kasashe masu yawa suke cewa suna son yin gwaji kuma suna son hukumomin tsaro da ke cikin tsarin su tabbatar  mun sanya ido kan irin hadari tare da gamsar da mutanenmu cewa wannan kimiyya ba ta da hadari kuma ba ta hadarin sanya jama’a ga kamuwa da wata guba.

Gudunmawar na’urori da kayan aikin samar da tsarin 5G

Ba tare da kayayyakin aiki masu inganci ba yin amfani da tsarin 5G zai zama mafarki. Saboda haka muna bukatar dabaru. A Najeriya mun kasa kasar zuwa yankuna bakwai kowane yanki an warewa kamfanin sanya na’urori don kai wa tare da kafa na’urorin samar da yanar gizo.

Mun sanya tsari na kasuwancin zangon yanar gizo ba za ka tsaya kan wani tsarin da ba ya amfani ba. Ko dai ka sayar da zangon ko ka bayar haya ko kuma ka bai wa wani kamfani.

“Hakan ya janyo wajen tabbatar da yin amfani da wannan muhimmin abu.  Idan aka yi la’akari da mutane  miliyan uku da digo bakwai da ba su yin amfani da kimiyar zamani a duniya, daya daga cikin uku na wadannan kaso na zaune a nahiyar Afirka. Ainihin kalubalen kan hada wadannan jama’a na kasashen Afirka karancin kayayyakin aiki. Har sai mun magance wannan kalubale ba za mu ga yanayin yana bunkasa ba ta yadda zai bai wa mutanenmu damar yin amfani ba kai wa ga tsarin 5G ba har ma da wasu tsare-tsare wadanda za mu iya samu.

“Wani vangaren da za iya mayar da hankali shi ne janyo zuba jari. Ba wata gwamnati a Afirka da za ta ita yi ita kadai. Gwamnatoci a kasashen Afirka suna mayar da hankali kan samar da kayayyakin more rayuwa. Kamfanonin sadarwa suna bukatar sanya jari kayayyakin da ake bukata da kudin da za a kashe na kawo sabbin kayayyaki don bunkasa tsarin. Hanyar da Kungiyar ITU ta bayar da shawara shi ne ya kamata a yi hakan ta hanyar amfani da tsarin PPP wanda muka sani, inda masu zuba jari za su shigo za su zuba jari a cikin kasar, inda vangaren masu zaman kansu a kasar za su samar da kudin tallafi don bunkasa tsarin.

“Ina tunanin hakan zai zama wata mafita musamman a kasashen da kasuwa take kamar kasar Najeriya inda ake da yawan mutane miliyan 200, kasuwar tana nan ta na jira a ci moriyarta don samar da tsari da samun riba kan jarin da aka sanya. Saboda haka muna kokari wajen bunkasa __Nahiyar Afirka zuwa mataki na gaba dole mu yi amfani da tsarin da ya dace wanda zai bunkasa saka jari a vangarenmu.”