Tsarin amfani da waya nau’in Blackberry

Daga cikin wayoyin salula na zamani masu tashe a yau, akwai wayoyi nau’in Blackberry da ake amfani da su.  Wayoyin salula nau’in Blackberry suna kan yaduwa a duniya a halin yanzu.  Kuma duk da cewa wayoyi ne na alfarma, kuma masu tsada da ba kowa ke iya mallakarsu ba, shafin Kimiyya da kere-kere ya ga […]

Tsarin amfani da waya nau’in Blackberry

On May 30, 2007, AT&T and Research In Motion announced retail availability of the BlackBerry Curve in the U.S. Packed with consumer-friendly features including a 2 megapixel camera, enhanced media player and high performance Web browser, the BlackBerry Curve goes on sale tomorrow for as low as $199.99. (PRNewsFoto/AT&T)

 Nau’in wayar BlackberryDaga cikin wayoyin salula na zamani masu tashe a yau, akwai wayoyi nau’in Blackberry da ake amfani da su.  Wayoyin salula nau’in Blackberry suna kan yaduwa a duniya a halin yanzu.  Kuma duk da cewa wayoyi ne na alfarma, kuma masu tsada da ba kowa ke iya mallakarsu ba, shafin Kimiyya da kere-kere ya ga dacewar gabatar da ’yan takaitattun bayanai ga masu karatu don fahimtar yadda tsari da kintsinsu yake.  Har wa yau, na tabbata da yawa cikinmu mun samu labarin cewa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates) ta toshe wasu daga cikin hanyoyin amfani da wannan waya mai matukar tasiri saboda wasu dalilai.  To me ya kawo haka?  Kuma wane irin tsari ne wannan nau’in wayar salula ke da shi da har zai sa wata kasa ta dauki mataki makamancin wannan?  Duk wadannan na cikin abubuwan da za mu karanta cikin wannan mako da makon da ke tafe in Allah Ya yarda.  Da farko dai, ga bayani nan kan ma’ana da samuwar wannan waya ta Blackberry.

Ma’ana da asali
Kalmar Blackberry, a Turancin Kimiyyar Sadarwa ta Zamani a yau, na ishara ne zuwa ga wani jerin wayoyin salula na musamman nau’in Smartphone, masu dauke da  masarrafar Imel da kamfanin Research in Motion (RIM) na kasar Kanada yake kerawa.  Wannan waya ta Blackberry na dauke ne da masarrafai na musamman da ake amfani da su ta hanyoyi na musamman, kuma a wani irin yanayi da ya sha bamban da sauran hanyoyin sadarwa.  Wasu cikin wadannan masarrafai dai sun hada da masarrafar Imel mai zaman kanta, wato Mobile E-mail da manhajar kalanda da masarrafar taskance bayanai da masarrafar allon rubutu na kamfanin Microsoft – irin su Microsoft Word da Edcel – da taskar adireshi da manhajar mu’amala da tsarin sadarwa ta wayar iska, wato Wireless Frekuency Radio (Wi-Fi) da masarrafar sauraro da shan kida da rariyar saduwa da Dandalin Facebook da MySpace da na Twitter.  Har wa yau akwai masarrafar gano bigire, wato Geographical Positioning System (GPS) da manyan ka’idojin da ke tafiyar da manhajar Imel: Post Office Protocol (POP) da Internet Message Application Protocol (IMAP), sai kuma manhajar hirar ga-ni-ga-ka, watau Instant Chat Messenger, mai taimakawa wajen gudanar da hira tsakanin mai wayar da duk wanda ke giza-gizan sadarwa ta duniya, irin su Yahoo Messenger, da Windows Libe Messenger da ICk da Google Libe Talk da sauransu.
Wannan waya ta musamman mai suna Blackberry, kamfanin Research in Motion da ke kasar Kanada ne ya fara kera ta a 1999.  Zubin farko da kamfanin ya fara kerawa su ne nau’in Blackberry Pearl, kuma shafukansu launin fari da baki ne, babu wasu launi-launi na daban, wato Monochrome ke nan.  Cikin shekarar 2002 ne ya fara kera na zamani masu dauke da manhajoji masu kayatarwa.  Kuma a haka kamfanin yake tafiya har zuwa yau; inda yake ta kera wasu nau’uka daban-daban masu dauke da abubuwa da dama. A kididdigar da masana kuma masu lura da tsari da tasirin tsarin sadarwa ta wayar salula a duniya suka bayar, bayan wayoyin salula masu dauke da manhajar Symbian OS da kamfanin Nokia ke kerawa, babu wata wayar salula da ta fi samun kasuwa a duniya irin Blackberry.

Manufa
Sabanin sauran wayoyin salula wadanda tun asali an kera su ne don aiwatar da sadarwar murya musamman (boice Communication), su wayoyin salula nau’in Blackberry an samar ko an kera su ne musamman don sauwake ayyukan ofis da kamfanoni da kuma mu’amala da fasahar Intanet dare da rana safe da yamma.  Wannan kuwa a fili yake, musamman idan mai karatu ya yi la’akari da irin manhajoji da kuma masarrafan da wayar ke dauke da su.
Idan kana dauke da waya nau’in Blackberry, wacce ke hade babu kwange tare da ita, to, sadarwa a gare ka ba wata matsala ba ce.  A kowane lokaci tana jone ne ta giza-gizan sadarwa ta duniya, wato Intanet.  Kana iya karba da aika sakonnin Imel a duk sa’adda ka ga dama.  Kana iya hira da duk wanda kake so a duniya muddin a jone yake da Intanet. Kai a takaice ma dai, kana iya tafiyar da ayyukan kamfaninka ko hukumar da kake yi wa aiki a duk inda kake. Da wannan nau’in wayar salula, ana gudanar da harkar kasuwanci da shugabanci da siyasa da addini da duk abin da ya shafi zamantakewa.  Kana zaune a gidanka ne, ko a cikin jirgi kake, ko a cikin mota, ko kwance kake, ko a kasuwa kake, ko a maraya kake, ko kuma a karkara; duk ba ka da matsala.  Bayan haka, wannan waya ce da idan ka caja batirinta, kana iya kwanaki masu tsawo ba ka bukaci na’urar caji ba. Domin dukkan manhajojin da ke cikinta ba su cin makamashi fiye da kima, balle har kuzarin batirinka ya gaza nan take.  A halin yanzu wannan waya na sahun kayayyakin sadarwa na tafi-da-gidanka masu canja tsarin rayuwa a duniya, wato Conbergent Debices.

Babbar Manhaja
Kamar yadda masu karatu suka sha karantawa a wannan shafi, kowace wayar salula na dauke ne da bangarori guda biyu; bangaren gangar jiki da kuma na ruhi. bangaren ruhi ne muke yi wa lakabi da “manhaja.” Domin manhajar ce ke tafiyar da wayar; daga kunnawa har zuwa kashewa – idan babu manhaja a tare da ita, to gwamma a jefar a bola, watakila yara su tsinta su rika wasa da ita.  To, wayoyin salula nau’in Blackberry na dauke ne da babbar manhaja (wato Operating System) mai suna Blackberry OS 6.0.  Wannan shi ne zubin manhajar na zamani. Wannan babbar manhaja tana da kuzari matuka, kuma idan kana da Blackberry tsohuwar ya yi wacce ke dauke da babbar manhajar baya, kana iya kara mata kuzari (wato Software Update) ta hanyar zuwa shafin kamfanin ta Intanet daga wayar, ko kuma ka yi amfani da manhajar shigar da masarrafai ta kwamfuta, wato Blackberry Desktop Manager wajen yin hakan.  
Bayan babbar manhaja, kowace wayar salula nau’in Blackberry na gudanuwa ne a saman masarrafar tafiyar da ruhin waya nau’in ARM.  Nau’in Blackberry na farko sun yi amfani ne da Intel-80386.  Daga baya kuma sa’adda kamfanin ya tashi kera Blackberry zubin 8000 Series, sai ya yi amfani da nau’in ARM dScale 624MHz, in ka kebe zubin Blackberry 8707 wacce aka dora ta a saman nau’in kualcomm 3250.  Wannan mizani ne na tsarin sadarwa mai taimaka wa injin kwamfuta ko wayar salula sauri da gaggawar karba da aiwatar da umarnin da aka ba ta, kuma shi ake kira Processor a Turancin kimiyyar sadarwar kwamfuta.