Tsarin babbar manhajar Android (7)

Matashiya A makon da ya gabata mai karatu ya fahimci yadda babbar manhajar Android, ta amfani da tsarin “Actibity Manager,” ke taimaka wa mai waya wajen mu’amala da masarrafa ko manhajar da yake budewa don amfani da su.  Duk da cewa na samu sakonni da dama daga masu karatu kan wasu daga cikin dabi’un Android […]

Tsarin babbar manhajar Android (7)

Yadda ake samar da bayanai a Tsarin Babban Manhajar AndroidMatashiya

A makon da ya gabata mai karatu ya fahimci yadda babbar manhajar Android, ta amfani da tsarin “Actibity Manager,” ke taimaka wa mai waya wajen mu’amala da masarrafa ko manhajar da yake budewa don amfani da su.  Duk da cewa na samu sakonni da dama daga masu karatu kan wasu daga cikin dabi’un Android da jama’a ke korafi kansu, zan dakatar da bayani kan dalilan da suka sa haka ke faruwa.  A yau cikin dacewar Ubangiji za mu ga yadda ake gina manhajojin da ake amfai da su a babbar manhajar Android ne.  kada mai karatu ya rikice.  
A baya na yi bayani ne kan manufar gina babbar manhajar Android.  Wannan a fili yake.  Ma’ana na yi magana ne kan manufofin da kungiyar Open Handset Alliance ya kiyaye wajen gina manhajar.  A karo na biyu kuma na yi bayani kan tsarin gina manhajojin da mai waya ke amfani da su a kan Android, wanda ya kunshi bayani kan tsare-tsaren da ke cikin manhajojin, da dabi’unsu.  Wannan bayanin ne ma ya kawo mu kan tsarin “Actibity Manager” da sauransu.  Bayanin yau, wanda nake sa ran ya zama na kusa da karshe, kan yadda ake gina manhajojin da ake amfani da su ne a kan Android, da matakan da ake bi kafin yin hakan, da kayayyakin aiki da ake bukata kafin fara hakan, sannan da aiwatar da ginin, a aikace.  Ban ce wadannan bayanai za su takaitu cikin kasida guda ba.  Amma dai, bari mu gwada mu gani.

Gina Manhajojin Android a Aikace
Dukkan manhajojin da mai amfani da wayar Android ke saukarwa daga Cibiyar Play Store ko Google Play, mutane ne suka tsara su, suka gina su, sannan suke watso su wajen, kyauta.  Ta yiwu mai karatu ya kalli abin ya ga kamar da wuya ya iya.  Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Kana iya gina manhajar Android kai ma ka loda a wannan cibiya, da harshen Hausa.  Ba wani abu ba ne mai wahala.  Idan ma da wahala, to duk bai wuce rashin sanin matakai da hanyoyin gudanarwa ba.

Masu Ginawa
Masu gina wadannan manhajoji dai sun kasu kashi kashi ne, dangane da kwarewa na ilimi nake nufi.  Akwai wadanda su daman can aikinsu kenan gina manhajojin kwamfuta, tun kafin zuwan Android.  Da wannan babbar manhaja ta samu, sai suka kalli tsari da kintsinta, suka kalli dabarun gina manhajar kwamfuta da aka yi amfani da su wajen gina ta, daga nan suka kama gina manhajojin da za su iya gudanuwa a kanta.  Kashi na biyu su ne wadanda suka koyi abin matakin farko zuwa kurya, a ilimance, a aikace.  Dukkan wadannan biyun ana kiransu “Android Debelopers.”

Hanyoyin Ginawa
Dangane da gina manhajojin Android a aikace, akwai hanyoyi guda biyu, ko uku.  Haryar farko ita ce ta amfani da gundarin ilimin gina manhajojin kwamfuta, wato “Application Programming Language,” don gina masarrafan.  Wannan ita ce hanyar da kwararrun masana a wannan fanni suke bi wajen gina manhajar Android.  Bayani kan nau’ukan ilimomi ko dabarun yin hakan kuwa na nan tafe in Allah Ya so.  Hanya ta biyu kuma ita ce ta yin amfani da manhaja ta musamman, don gina manhajar Android.  Wannan ita ce hanyar da galibi wadanda ke da sha’awar gina manhajar Android ke amfani da ita a farko; ko don sha’awar yin hakan kadai, ko kuma don “farawa” da “gwadawa.”  Wannan hanya ta biyu babu wata kwarewa ta musamman tare da ita, domin cikin ‘yan mintuna kana iya gina manhajar Android ba tare da gumi ba.  Sannan manhajar da za ta taimaka maka wajen yin hakan ma kyauta z a ka same ta a Intanet.  
Galibin manhajojin Android na littafai (kamar Kur’anai da Hadisai ko littafan ilimi, ko album na hotuna da muke gani a cibiyar Play Store) duk da ire-iren wadannan manhajoji ake gina su.
Hanya ta uku ita ce yin amfani da hanyoyi biyun farko da suka gabata, don tsarawa, da ginawa da kuma kayatar da manhajar Android.  Ba dukkan kwararru ke amfani da wannan hanya ba.  Galibi wadanda ke amfani da hanya ta biyu ne ke neman kwarewa wajen hada dabarun guda biyu.  Akwai hanya ta karshe, wacce ta shafi karance-karance kan yadda ake gina manhajar Android a aikace, ta hanyar littattafan da aka rubuta, da hotunan bidiyo da masana a wannan fanni suka tsara ko ake samun kyauta a Intanet.  Wannan hanya tana da inganci matuka, domin hanya ce mafi sauki da za ta kai dalibi zuwa hanyar farko, wato hanyar da masana ke amfani da ita.  Ta fi hanya ta biyu inganci, domin duk abin da ka karanta kuma ka aikata, ya zauna a kwakwalwarka kenan.
Duk da haka, abin da ya fi mahimmanci dai shi ne manhajar ta zama mai inganci.  Ba kuma abin da ke taimakawa wajen yin hakan illa kwarewa da hazakar mai gina manhajar.

Ilimin Ginawa
Gina manhajar da za ta iya wanzuwa da gudanuwa a kan babbar manhajar Android yana bukatar ilimi matuka, da lokaci, da kuma sadaukar da kai.  Duk da nace ba abu ba ne mai wahala.  Akwai nau’ukan ilimi da dabarun gina manhaja da ake amfani da su wajen yin wannan aiki masu dimbin yawa.  Amma wanda ya fi shahara shi ne dabarun gina manhajar kwamfuta mai suna JAbA.  Bayan shi akwai wasu kanana irin su Python.  Amma dai JAbA ya fi shahara.  Saboda saukin mu’amala da yake dauke da shi, sannan tsari ne mai iya wanzuwa a kowace irin kwamfuta ko madauki na sadarwa mai amfani da manhaja – Windows ko Linud ko Mac.
Idan kana son koyon yadda ake gina manhajar Android ta amfani da wannan ilimi na JAbA kuwa, dole ne ya zama kana da sanayya kan wannan ilimi iya gwargwado; ko da kuwa a matakin farko ne.  Sai kuma dabarar hade bayanai waje daya mai suna Edtensible Markup Language, ko dML a gajarce.  Nau’in ilimi ne mai matukar muhimmanci a tsari da fannin sadarwa na zamani.  Idan ka budo manhajar da ke gudanuwa a kan Android, za ka samu tana dauke ne da siffa na zahiri da ta kunshi shafin farko, da shafi na biyu har zuwa yadda aka tsara, sannan da hanyoyin mu’mala da manhajar na zahiri, wato Menus da Toolbars da Windows misali.  Duk wadannan siffofi na zahiri ana tsara su ne da wannan ilimi na hade bayanai mai suna Edtensible Markup Language.  Kwatankwacin wannan ilimi kamar kwarangwal ne da kafinta ke yi wanda ake kira rafta, kafin ya fara dora fallen kwano a saman gini.  Ko kwarangwal din kofofi da tagogin sabon gida, kafin a zo a dora hakikanin marafan kofofi da tagogin.  Wannan ilimi yana da matukar mahimmanci da tasiri sosai a wannan fage.  
Idan ka bude hakikanin jakar bayanan da ke dauke da wata manhaja ta Android, za ka tarar tana dauke ne da manyan bangarori guda biyu; bangaren siffofinta na asali wanda aka tsara da ilimi dML, sai kuma bangaren da ke lura da tsara bayanai da kyale-kyalen da manhajar ke dauke da su, wanda aka tsara a dabarun gina manhaja (ko dai ya zama JAbA ko wani ilimi daban).
Idan kai kwararre ne a wannan fanni, ba sai na gaya maka hanyoyin da za ka bi ba.  Amma idan irina ne kai, to, kana da hanyoyi biyu.  Ko da ka je makaranta a koya maka (akwai makarantun karantar da yadda ake gina manhajojin wayar salula a Najeriya), ka biya abin sadaka, ko kuma ka zauna ka bata hankalin dare, don koya wa kanka ta hanyar karanta littattafan da aka rubuta a wannan fanni, ko hotunan bidiyo, don ganin yadda ake abin a aikace.
Idan ka zabi zuwa makaranta, a nan sai dai ka ji da kudin makaranta, wanda galibi daga Naira dubu hamsin (N50,000) ne zuwa sama.  Za a koya maka cikin kasa da watanni uku, idan kana bukata.  Wannan karantarwa da za a maka ya hada da kwatanta ilimin ne a aikace.  Amma wannan ba zai sa ka kware ba nan take, sai ka yi ta maimaita abin a aikace.  Kada ka mance, da babu makoyi, da gwanaye sun kare.
Idan kuma ka zabi zama da kanka ne don koyo, wannan ma abin maraba ne.  Sai dai dole ne ka tarbiyyantar da kanka.  Koyon ilimi ba tare da malami ba, aiki ne ja, in ji mutan garin dan Ja a Katsina.  To, akwai littattafai da dama.  Wadannan littattafai an rubuta su ne a lokuta daban-daban, ta amfani da mazubin tubulin gina manhajar Android daban-daban.  Ga kadan daga cikinsu nan (idan mai karatu na bukata yana iya tuntubata sai mu shirya yadda zan turo masa):
Littafin farko mai take: “Android Application Debelopment Cookbook: 93 Recipes for Building Winning Apps,” wanda Wei-Meng Lee ya rubuta, yana dauke ne da hanyoyi da dabarun gina nau’uka ko bangarorin manhajar Android guda 93!  Littafi ne mai kayatarwa ainun, kuma ya yi amfani ne da zubin JAbA na 6, “Jaba bersion 6.”  Sai littafin shahararren marubuci Jason Ostranda mai suna: “Android User Interface Fundamentals,” mai shafuka  337.  Littafin na koya wa mai karatu ne yadda zai gina fuska da shafuka da hanyoyin mu’amala a manhajar Android, wato “idon gari.”  Wannan wani bangare ne mai mahimmanci a ilimin gina manhajar Android, domin shi ne bangaren da mai waya ke mu’amala da shi.  Sai littafi na gaba mai taken:  “User Interface Design for Android Apps,” wanda Ryan Cohen da Tao Wang suka rubuta.  Littafi ne na hadin gwiwa, kuma, kamar wanda ya gabace shi, yana karantar da yadda ake tsara hanyoyin mu’amala da manhajar ne.  Shafukan littafin ba su shige 173 ba; babu yawa.  Sannan akwai hotuna da gamsassun bayanai masu nuna wa mai karatu yadda zai dabbaka abin da ake koya masa.
A bangaren masu koyo na fari kuwa, akwai littafin shahararren masani Masumi Nakamura da abokinsa Marko Gargenta, mai take: “Learning Android.”  Littafi ne da ke koyar da yadda ake gina manhajar Android daga farko zuwa karshe, ta hanya mai sauki, da hotuna da bayanai.  A cikin littafin, marubutan sun kwatanta yadda mai karatu zai iya gina manhajar Dandalin Abota mai amfani da tsari irin na “Twitter,” wajen musayar ra’ayi tsakaninsa da abokansa.  Idan ka bi wannan littafi, za ka iya gina taka manhajar, har ma ka yi gogayya da abokanka a yanar gizo.  Shafukan littafin ba yawa; dari biyu da ashirin da takwas (228) ne kacal!  Sai littafi mai take: “Jaba Programming for Android Debelopers for Dummies.”  Wannan littafi ne da aka rubuta shi musamman don karantar da wadanda suka kware a fannin gina manhajar kwamfuta ta amfani da tsarin JAbA, don su iya gina manhajar Android cikin sauki.  Littafin na dauke da darasi na musamman kan ilimin JAbA a gajarce, sai kuma darasi mai zurfi kan yadda ake gina manhajar Android.  Wannan littafi ya zo ne don a kashe tsuntsaye biyu da dutse daya.   Marubuci Barry Burd ne ya rubuta littafin, kuma shafukansa 458 ne.
A nasa bangaren, Wallace Jackson ya rubuta littafin: “Pro Android Graphics,” don karantar da yadda ake tsara hotuna, da bidiyo, da kuma sauti a manhajar Android.  Babbar magana.  A cikin littafin, wanda shafukansa ba su wuce 605 ba, ya nuna a aikace yadda ake tsara wadannan abubuwa cikin sauki (ga wanda ya sadaukar da kansa).  Littafi ne mai dadin karatu ga wanda yake sha’awa kuma yake iya jure tsawon lokacin karatu.  Yana fitar da wannan littafi kuma sai ga wani mai taken: “Pro Android Flash,”  wanda marubuta Stepehn Chin, da Dean Iberson, da Oswarld Campesato da kuma Paul Tirani suka rubuta.  Littafin na karantar da yadda ake shigar da tsarin Flash ne, wanda wani tubali ne na musamman wajen mu’amala da bidiyo a wayoyin salula.  Shafukan littafin 463 ne.  
Wadannan kadan ne daga cikin littattafan da ake kan rubutawa don karantar da yadda ake gina manhaja da masarrafar da za a iya amfani da ita kan babbar manhajar Android, cikin sauki da kayatarwa.  Abin da ya rage wa mai karatu kawai shi ne ya sa sha’awar abin cikin zuciyarsa, sannan ya sadaukar da lokacinsa don cimma burinsa.  Allah Ya sa mu dace, amin.