‘Tsarin Bahaushe a Legas na da ban haushi’

Bahaushe a Legas na da ban haushi, duba da yadda ake zama irin na ’yan marina, kowa da tasa alkiblar.

‘Tsarin Bahaushe a Legas na da ban haushi’

Alhaji Sa’adu Gulma lokacin da yake yi wa Shugabannin Kungiyar Atto jawabi

Shugaban Kungiyar Ci Gaban ’Yan Arewa Mazauna Legas da ke yankin Iddo a Unguwar Atto a Jihar Legas, Alhaji Bala Muhammad wanda shi ne Daraktan Agaji na Kungiyar Izalatil Bidi’a wa Ikamatus Sunnah a jihar, ya bayyana cewa tsarin Bahaushe a Legas na da ban haushi, duba da yadda ake zama irin na ’yan marina, kowa da tasa alkiblar.

“Irin tsarin da muke kai a yanzu babu yadda za mu iya asassa wani abu ya yi tasiri domin an rarrabu kowacce unguwa muna da Sarki biyu, mun dade abin na damunmu, mun rasa yadda za mu yi, wannan ne ya sa muka yi kokari muka kafa kungiya domin magance wannan matsala ta yadda za mu samu hadin kai mu samu ci gaba,” inji shi.

Shugaban kungiyar ya shaida hakan ne a sa’ilin da ya jagoranci shugabannin kungiyar inda suka ziyarci Shugaban Kungiyar ‘Yan Arewa mazauna Legas a karkashin inuwar Jam’iyar APC Alhaji Sa’adu Dandare Gulma a ofishinsa da ke Kasuwar Shanu ta Abbatuwa a karshen makon jiya.

Ya jinjina wa Alhaji Sa’adu Dandare Gulma a kokarin da yake na hade kan ’yan Arewa mazauna Legas, abin da ya ce lamari ne mai matukar wahala duba da irin tsarin Bahaushe a Jihar ta Legas.

“Domin babu abin da ya kai yunkurin hada kan ’yan Arewa a Legas wahala, kanmu baya haduwa sai idan akwai matsala, amma da zarar ana zaune lafiya kowa ta kansa yake, babu tsarin kungiya, kuma in ba za mu yi komi a kungiyance ba, to ba za mu kai ga gacci ba, don haka ya ce aiki ya samu shugaban, domin dole ne ya tashi tsaye ya yi da gaske kuma dole ne ya yi hakuri ya zamo mai juriya, ya kuma ba shi tabbacin goyon bayan kungiyar, inda ya yi fatar Allah Ya dafa masa,” cewar Muhammad.

A nasa bangaren Alhaji Sa’adu Dandare Gulma yabawa ya yi ga shugabannin kungiyar Atto da suka ziyarce shi ya ce, kungiyar tana sahun gaba a cikin kungiyoyin ’yan Arewa mazauna Legas wacce ke da kyawawan tsare-tsare na taimakon kai da kai da taimakon marasa karfi da marayu da gajiyayyu, ya ce yunkurin da yake na samun hadin kan ’yan Arewa mazauna Legas aiki ne jah, amma sun dauko tsari mai kyau na neman goyon bayan wadanda suka shirya don ba da gudunmawa a tafiyar.

“Muna kokarin bibiyar sarakunan gargajiya da shugabannin kasuwanninmu wadanda daman suma fatarsu ne a tafi tare a tsira tare, shi daman mai yi ake kira a tafi tare, kokarin da muke mu samu goyon bayan koda kashi 75 cikin 100 ne in Allah Ya tabbatar mana da wannan bukatarmu ta biya,” inji shi.

Gulma ya ce, babbar matsalar Bahaushe a Kurmi shi ne son kai ko kuma son zuciya, domin muhimmancin ’yan Arewa a siyasance a Jihar Legas ne ya sa aka ba su mukamin Kwamishina a gwamnatin Legas, “a Legas ne kadai Bahaushe yake da wannan tagomashi a Kudu amma matsalar ita ce, ana amfana da wannan tagomashin?

Shin wakilci ne namu na ’yan Arewa ko kuma dauki-dora ne?” a cewarsa.

A karshe ya jaddada cewa, lokaci ya yi da ’yan Arewa za su daina zama kara zube, lokaci ya yi da za su farka daga barci da suke; su tashi su hada kai domin ci gabansu a zamantakewar da suke yi a Legas.