Tsarin da APC ta kawo na zaben ‘yan takara ya yi daidai – Dokta Nasirudeen

Wani dan takarar kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, Dokta Nasirudeen Usman ya yi amanna da tsarin da Shugaban Jam’iyyar ta kasa ya fitar wajen fitar da dan takara. Dokta Nasirudeen Usman, wanda shi Mataimakin Darakta Janar na Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya da […]

Tsarin da APC ta kawo na zaben ‘yan takara ya yi daidai – Dokta Nasirudeen
Tsarin da APC ta kawo na zaben ‘yan takara ya yi daidai – Dokta Nasirudeen

Wani dan takarar kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, Dokta Nasirudeen Usman ya yi amanna da tsarin da Shugaban Jam’iyyar ta kasa ya fitar wajen fitar da dan takara.

Dokta Nasirudeen Usman, wanda shi Mataimakin Darakta Janar na Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya da ke Kano ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce tsarin da uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta kawo, na yadda za a gudanar da zaben tsayar da ’yan takarar jam’iyyar a zaben da za a gudanar a badi, ya yi daidai. 

Ya ce tsarin da Jam’iyyar APC ta kawo na zaben ’yan takara, inda ta ce a zaben Shugaban kasa za ta yi zaben kato-bayan-kato ne, sannan wakilai su gudanar da sauran zabubbukan ya yi daidai.

Ya ce abin da ya sa uwar jam’iyya ta ce a bi tsarin amfani da wakilan jam’iyya a jihohi, ta lura da wasu matsaloli da za su iya tasowa a wasu jihohi, idan ba irin wannan zabe aka yi ba. Don haka aka bai wa kowace jiha zabi, ta je ta zabi tsarin zaben da take so, wanda ba zai kawo wata matsala ba. 

Dokta Nasirudeen Usman ya ce tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya, Jam’iyyar APC ce kawai ta bai wa ’ya’yanta irin wannan dama. Ya ce babu shakka wannan mataki da Jam’iyyar APC ta dauka zai karfafa mulkin dimokuradiyya a Najeriya. 

Dokta Nasirudeen ya ce ko mutum 100 ne za su fito su yi takara da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan kujerar shugabancin kasar nan, ba za su samu nasara ba, domin ’yan Najeriya sun ga irin kokarin da Shugaba Buhari yake yi wajen farfado da kasar nan. Don haka ba za su bar wannan dama da suka samu ba.

Ya ce idan Shugaba Buhari ya ci gaba da mulki nan da shekara 4 masu zuwa, zai dora kasar nan kan kyakkyawar turba tagari.