Tsarin ECOWAS na wahalar da manoma shinkafa a Najeriya  – Lokpobiri

Minista a Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Sanata Heineken Lokpobiri, ya bayyana kokarin Gwamnatin Tarayya wajen rage shigo da shinkafa daga kasashen waje da cewa yana fuskantar matsala musamman daga Jamhuriyyar Benin sakamakon tsarin Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS). “Kalubalen da muke fuskanta daga kasashe makwabta shi ne, saboda tsarin da […]

Tsarin ECOWAS na wahalar da manoma shinkafa a Najeriya  – Lokpobiri

Minista a Ma’aikatar Gona da Raya Karkara Sanata Heineken Lokpobiri, ya bayyana kokarin Gwamnatin Tarayya wajen rage shigo da shinkafa daga kasashen waje da cewa yana fuskantar matsala musamman daga Jamhuriyyar Benin sakamakon tsarin Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma, (ECOWAS).

“Kalubalen da muke fuskanta daga kasashe makwabta shi ne, saboda tsarin da Kungiyar ECOWAS ta fitar, jama’ar kowace kasa na kawo irin shinkafarsu ce zuwa yankunansu, ana sarrafa shinkafar da zuba ta a cikin buhu sannan a shigo da ita zuwa Najeriya. Dalili a nan shi ne, a tsarin Kungiyar ECOWAS kayan da aka sarrafa a kowace kasa za su samu damar shiga kowace kasuwa a yankin,” inji shi.                                                                                                                                              “Ta wannan tsari manoman shinkafa na kasar Thailand za su iya kai shinkafarsu zuwa Jamhuriyar Benin da shinkafar da suka cashe ta sai su shirya ta a cikin buhu, duk da yake a cikin kasar Benin aka kammala sarrafa shinkafar daga bisani sai a fara safarar ta zuwa Najeriya, wanda hakan yana dakile damar da ’yan kasar Benin suke da ita wajen noman shinkafa a kasarsu, sannan su amfana daga kasuwannin Najeriya. Dalilin haka ya sa muka saka Gwamnatin Benin a harkar har zuwa matakin Shugaban Kasa,” inji shi.

Ya kara da cewa “A kan harkar shigowa da shinkafa daga kasashen waje ya sa Shugaba Muhammadu ya gayyaci Shugaban Jamhuriyyar Benin don tattaunawa kan yadda za a dakile safarar shinkafa kasancewar kasar na makwabtaka da Najeriya.”

A jawabin wakiliyar Asusun Habaka Ayyukan Noma ta Majalisar  Dinkin Duniya (IFAD) a Najeriya, Misis Ndine Gbossa, ta ce, shugabannin IFAD sun amince da karin Dala miliyan 89 ga Najeriya don bunkasa harkokin noma shinkafa da rogo da kasar nan ke shirin samar musu da  Dala miliyan 228.

Misis Ndine ta kara da cewa, akwai karin gudunmawar kudi da aka ware asusun matasan yankin Neja Delta na Dalar Amurka miliyan 60 domin magance ayyukan fasa bututu a yankin.