Tsarin gadon dabi’u da Siffofin Halitta (1)

Gabatarwa Al-Fazaaree, daya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi), wata rana ya dawo gida sai ya samu matarsa ta haifa masa jariri baki sitik! Nan take hankalinsa ya tashi. Domin Balarabe ne shi, farin Balarabe kuwa, haka ma matarsa. Amma ta yaya aka yi ta […]

Tsarin gadon dabi’u da Siffofin Halitta (1)

Gabatarwa

Al-Fazaaree, daya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi), wata rana ya dawo gida sai ya samu matarsa ta haifa masa jariri baki sitik! Nan take hankalinsa ya tashi. Domin Balarabe ne shi, farin Balarabe kuwa, haka ma matarsa. Amma ta yaya aka yi ta haifa masa jariri baki sitik? Nan take ya nannade wannan jariri a zanen goyo, ya kama hanya sai wajen Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi).  Yana zuwa ya tarar da shi cikin sahabbansa kamar galibin lokuta. Yana isowa wajensa bayan ya yi masa sallama, sai ya nuna wa Manzon Allah wannan jariri, ya ce: “Dubi abin da ta haifa mini.” Sai Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya fahimci inda ya dosa nan take. Sai ya ce masa: “Kana da rakuma?” Sai ya ce: “Eh, ina da su.” Sai Manzon Allah ya sake ce masa: “Mene ne launinsu”  Sai ya ce: “Jajaye ne.” Sai Manzon Allah ya sake ce masa: “Babu wani mai launin baki-baki daga cikinsu?” Sai wannan Balarabe ya ce: “Akwai,” sai Manzon Allah ya sake tambayarsa: “Daga ina ya samo wannan launi (bayan iyayensa jajaye ne)?” Sai Al-Fazaaree ya ce: “Watakila wata jijiyar (dabi’ar) halitta ce ta jawo (daga kakanninsa).”  Sai Manzon Allah ya ce: “Haka shi ma wannan, ta yiwu wata jijiya ce ta jawo (daga kakanninsa)”

Wata rana Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yana zaune sai ga wani daga cikin mutanen Madina ya riko matarsa, rike da jariri baki sitik su ma, a kidime. Suna zuwa wajensa sai mutumin ya ce: “Ga abin da ta haifa.” Sai matar ta yi caraf ta ce: “Na rantse da Wanda Ya aiko ka da gaskiya, a matsayin cikakkiyar budurwa ya aure ni, kuma ban taba shigo da wani gidansa ya haye kan tabarmarsa ba.” Fadin haka ke da wuya sai Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya nuna cewa lallai abin da ta fada gaskiya ne. Domin daga ita har shi suna da dabi’un halitta wajen casa’in da tara ga kowanne, kuma kowanne daga cikinsu na yaduwa cikin jikinta ne a lokacin saduwa, yana rokon Allah da Ya sa jaririn da za a haifa ya zo da kama irin tasa.

Ummu Sulaim ita ce mahaifiyar Anas dan Maalik (Allah Ya kara musu yarda). Wata rana ta shigo inda Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yake zaune tare da sahabbansa, sai ta ce: “Ya Manzon Allah, hakika Allah ba Ya kunyar bayyana gaskiya.  Shin, wanka ya wajaba ga mace idan ta yi mafarki (ana saduwa da ita)?” Sai Manzon Allah nan take ya ce mata: “Na’ma, muddin ta ga ruwa.” (Ma’ana ruwan maniyya ke nan). Nan take sai Nana A’isha ta ce: “Shin mace ma tana fitar da wani ruwa ne?” Sai Manzon Allah ya ji, kuma ya ba ta amsa da cewa: “Kayya, A’isha! Ta yaya ake samun kamanceceniya to, (tsakanin jariri da iyayensa)?”

Daidai lokacin da Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya shigo garin Madina lokacin Hijira, sai Abdullahi Ibn Salaam, daya daga cikin manyan Malaman Yahudawan Madina ya je ya same shi, ya ce masa: “Na zo ne in tambaye ka kan wasu abubuwa guda uku, wadanda babu wanda ya sansu sai Annabi…”  Daga cikin tambayoyin da ya masa akwai neman sanin dalilin da ke sa jariri ke yin kama da mahaifinsa ko mahaifiyarsa? Sai Manzon Allah ya amsa masa cewa: “Idan ruwan (maniyyin) namiji ya riga na mace, to, (jaririn) zai yi kama da mahaifinsa. Idan kuma ruwan (maniyyin) macen ne ya riga na namijin, to, (jaririn) zai yi kama da mahaifiyarsa.” Daga nan sai Abdullahi Ibn Salaam ya ce: “Na shaida hakika babu abin bautawa a bisa cancanta face Allah, kuma lallai kai Manzon Allah ne.”

Daga cikin nau’ukan ilimin kimiyyar halitta da rai a duniyar yau, akwai fannin da ke bincike kan dalilan samun kamanceceniya tsakanin ’ya’ya da iyayensu ko kakanninsu, na kusa ne ko na nesa. Da kuma kamanceceniya ta dabi’ar jiki da dabi’ar tunani da dabi’ar juriya ko ragwanci da dabi’ar kirar jiki da dabi’ar tsawo da gajarta da dabi’ar zati ko mutuntaka da dabi’ar sanyi ko zafin zuciya da dabi’ar karfi ko kudurar zuciya da dabi’ar taushi ko kaushin hali da yanayi da dabi’ar bambancin launin fata ko launin gashin kai ko yanayin farata da dai sauransu. Har wa yau, me ya sa wadansu ’ya’ya ke gadon cututtuka daga iyayensu? Me ya sa wadansu ke yin kama da dangin iyayensu ba da asalin iyayensu ba? Me ya sa ake haifan ’ya’ya masu dauke da cututtukan da iyayensu ba su da su? Me ya sa musamman a yau likitoci da ma malaman addinin Musulunci ke shawartar samari da ’yan mata masu niyyar aure da su je don gudanar da binciken jini da kwayoyin halittar jikinsu kafin su yi aure? Me ya sa jaririn da ake haifa wani ke zuwa namiji, wani kuma mace? Dukan wadannan nau’ukan al’amuran halitta ana binciken yanayinsu ne a karkashin wani sabon fannin ilimin likitanci mai suna “Genetics” ko “Heredity” ko kuma “Genetic Inheritance”, a Turancin kimiyyar halitta da rai.

Hadisin farko da ke sama Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi, tare da sauran malaman Sunan, wato Abu Daud da Tirmizi da Nasaa’i da Ibn Majah. Hadisi ne ingantacce. Hadisi na biyu kuma mursal ne, ba Hadisi ba ne ingantacce, amma ma’anar da ke cikinsa daya ce da wadda ke cikin Hadisin da ya gabace shi. Wato Hadisin farko ya karfafe shi wajen ma’ana ke nan. Hadisi na uku ingantacce ne, domin Muslim ne ya ruwaito shi. Sai Hadisi na hudu, wato Hadisin Abdullahi Ibn Salaam, shi ma ingantacce ne, domin Buhari ne ya ruwaito shi. Dukan al’amuran halitta da ke dunkule cikin wadannan hadisai da suka zo a sama, abubuwa ne masu ban mamaki da suka faru, wadanda a lokacin faruwarsu babu wanda zai iya gudanar da wani bincike a likitance don gano sababin faruwarsu, sai dai kawai a yi imani.  Amma a yau Allah Ya kawo mu lokaci da zamani mai cike da yalwa wajen samuwar kayayyaki da fasahar binciken kimiyya da likitanci, cikin sauki. Ganin irin tasirin da wannan tsarin bincike ke yi a sauran kasashen Turai na yau, musamman kasar Amurka, ya sa na ga dacewar gudanar da bincike na musamman don kosar da masu karatu, da yardar Allah, dangane da wannan sabon fannin bincike. Duk da cewa dadadden ilimi ne, amma malaman kimiyyar zamani ba su fara gudanar da bincike a cikinsa ba sai a 1981.

Wannan kasida za ta gudanar da bincike ne kan asali da dalilan da ke haddasa wadancan al’amura. Da farko bayanai za su zo kan ma’anonin kalmomin Turanci masu alaka da wannan bincike, wadanda mai karatu zai yi ta cin karo da su a halin karatunsa. Sannan bayanai kan “kwayar Halitta” ko “Tubalin Halitta”, watau “Cell” su biyo baya. A nan ne za mu fahimci tsarin wannan sinadari mai matukar muhimmanci da yanayinsa da muhallinsa, da adadinsa da kuma abubuwan da ke kunshe a cikinsa, musamman irin su “Tantanin kwayar Halitta” ko ganuwarta, wato “Cell Membrane” da “Ruwan Rayuwa” wato “Cytoplasm” da kuma “Asalin Sinadarin Halitta” wato “Nucleus.”  A cikin sinadarin halitta ne al’amuran da suka shafi bincikenmu suke kunshe.  

Abu na farko shi ne “Madarar Bayanan dabi’ar Halitta” wato “DNA” ko “Deodyribonucleic Acid” a warware. Sai kuma babbar kundi wato “Ma’adanar Bayanan dabi’ar Halitta” ko “Chromosome” a Turance. Bayan mun yi bayani kan wannan babban kundi, sai mu zarce kan sauran abubuwan da ke da alaka da wannan babban kundi mai dauke da dukan bayanai kan dabi’un da ’ya’ya ke gadonsu daga iyayensu, irin su “dabi’ar Halitta” wato “Gene.” Da “dabi’ar Halitta ta Musamman” wato “Allele.” Sai kuma “Kebantacciyar dabi’ar Halitta” wato “Trait” ko “Genetic Trait,” wadda ita kuma ta kasu kashi biyu ne; akwai “dabi’a Mafi Rinjaye” wato “Dominant Trait” da kuma “dabi’a Nakasasshiya” wato “Recessibe Trait.”  

Wadannan su ne damuwarmu cikin binciken baki daya. Kuma fannin gudanar da bincike a kansu shi ake kira “Genetics.” “Nau’in dabi’ar Halittar” mutum kuma shi ake kira “Genotype.” Wannan wani abu ne da ba a iya gani, kamar yadda bayanai za su nuna mana nan kusa. Amma “Nau’in dabi’ar Halitta na Zahiri” (irin su kama da launin jiki da launin idanu da tsawo da sauransu) shi ake kira “Phenotype.” “Gadon dabi’ar Halitta” daga iyaye ko kakanni kuma shi ake kira “Heredity” ko “Genetic Inheritance.” dan Adam ba ya rayuwa sai da matsaloli na abin da ya shafi lafiyar jiki. Wannan ka’ida ce gamammiya da Allah Ya sunnanta wa dan Adam, hatta kan abin da ya shafi “Gadon dabi’ar Halitta” akwai shi. Idan aka samu matsala wajen gadon wata dabi’a ta halitta, har abin ya yi mummanan tasiri ga rayuwar mai gadon, a kimiyyance an samu abin da ake kira “Genetic Disorder” ke nan. To, shi dan Adam a duk lokacin da ya samu kansa cikin matsala, duk tsawon zamani, sai ya yi kokarin neman magani; ta hanyar halal ko ta hanyar haram. Ya danganci irin tarbiyya ko lalurar da ya samu kansa a ciki. Don haka, “Fannin Ilimin Magance Tangardar dabi’ar Halitta” shi ake kira “Genetic Engineering.”  A karshe wannan kasida za ta dubi hukuncin halacci ko haramci a Musulunci, dangane da abin da ya shafi tsarin da Malaman Kimiyyar Likitanci ke bi a yau, wajen gyara dabi’ar halittar da ta samu tangarda, sanadiyyar nakasu daga dayan iyayen mai gado.

Wadannan su ne shahararrun kalmomin da mai karatu zai ta cin karo da su. A sashen da ke tafe da cikakken bayani zai zo kan kowannensu, don a fahimci abin da kowanne yake nufi.