Tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta (8)
Ga wadanda suka saba bibiyar wannan shafi a kodayaushe, kasidu kan Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta, wato fannin da a harshen Turancin ilimin kimiyya ake kira Genetics, sun faro ne tun cikin shekarar da ta gabata. Idan ba a mance ba, mun gabatar da kasidu har zuwa kashi na 7 da suka yi magana […]
Ga wadanda suka saba bibiyar wannan shafi a kodayaushe, kasidu kan Tsarin Gadon dabi’u da Siffofin Halitta, wato fannin da a harshen Turancin ilimin kimiyya ake kira Genetics, sun faro ne tun cikin shekarar da ta gabata. Idan ba a mance ba, mun gabatar da kasidu har zuwa kashi na 7 da suka yi magana kan tsarin jirkita siffofin da dabi’un halittar shuke-shuke da kayayyakin abinci da ake shukawa.
Mun kawo ma’ana da asalin wannan fanni da har yanzu a duniya ake ta muhawara wajen fa’ida ko rashin fa’idarsa, musamman a bangaren lafiyar jiki da muhalli. Wannan muhawara ce da za ta dauki tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin masana masu goyon bayan tsarin da kuma kwararru da ke ganin wannan babu abin da zai jawo wa duniya illa matsala.
A yau, cikin yardar Allah, ga ci gaba da tattaunawa kan wannan fanni. Wannan zai zama kashi na 8 ke nan, ko kasida ta 8 daga cikin jerin kasidun da muka fara kawowa.
Zan yi kokarin jeranta su ba tare da yankewa na tsawon lokaci ba, don kauce wa mantuwa kan abin da kasidar baya ta yi magana a kai. Duk da cewa wannan shafi ne da ke tattaunawa kan jimillar fannin kimiyya da kere-kere, wanda hakan ke bukatar a rika cakuda kasidun kan fannoni daban-daban.
Fannin da za mu duba shi ne bangaren abin da ya shafi Nau’in dabi’ar Halitta na Zahiri (Phenotype). Idan mai karatu bai mance ba dai, a kasidar farko mun nuna cewa: Nau’in dabi’ar Halitta (Genotype) a kimiyyance shi ne nau’in dabi’u da siffofin halittar da ya kebance kowane dan Adam da zuriyarsa. Shi ya sa ma idan ana son jingina wani jariri ko ’ya’ya ko kokarin gano rashin alakarsu ga wanda ake alakanta su da shi, sai a yi musu gwajin Nau’in dabi’ar Halitta (Genotype Test). Hakan na faruwa ne saboda ba abu ba ne da za a iya gani a zahiri, kamar siffar jiki; wajen tsawo ko gajarta ko laushi ko gautsi. Wannan Nau’in dabi’ar Halitta (Genotype) da ke kebance mutane daga wadanda ba su ba, ita ce ke bayyana hakikanin yanayin siffa da dabi’ar mutum a zahiri. Wadannan dabi’u da siffar halitta ta zahiri, wadanda ke samo asali daga wancan Nau’in dabi’ar Halitta ta boye, ita ake kira ‘Phenotype’.
Wannan shi ne abin da kasidarmu ta wannan mako za ta duba, don tattaunawa kan yadda yake samuwa, da abin da ke haddasa shi, da kuma tsarin sauyawarsa.
Kalmar ‘Phenotype’
A fannin ilimin kimiyyar sinadaran halitta, kalmar ‘Phenotype’ ta samo asali ne daga wasu kalmomi guda biyu na harshen Girka (Greek). Kalmar farko ita ce kalmar ‘Phainein’, mai nufin “Nuna wani abu…” da kuma kalmar ‘Typos’ da ke nufin “A kamanta.” Wadannan kalmomi biyu ne aka gwama su don samar da kalmar ‘Phenotype’, wadda a harshen sinadaran kimiyyar halitta ke nufin: “Nau’in dabi’ar halitta ta zahiri.” Wannan kuwa ya hada da dukkan abubuwan da ke bayyana siffar halitta da ake iya gani a fili, da wadda za a iya gani idan aka bude wani bangare na jikin dan Adam. Ire-iren wadannan siffofi sun hada da: Yanayin girman jiki, da tsawon hannu, da launin fatar jiki, da gajarta ko tsawon gabobi, da launin idanu, da nau’in jini (Blood Group), da dabi’un mu’amala, da dabi’un zamantakewa, da yanayin fahimta, da yanayin hazaka, da kaifi ko dakushewar basira, da taushi ko laushin fatar jiki da dai sauransu, abin da za a iya gani a kusa ko a nesa.
Asali da Tarihi
Duk da cewa fannin ilmin halitta na daga cikin dadaddun nau’ukan ilmin kimiyya, bunkasar fannin Nau’in dabi’ar Halitta ta Zahiri bai samu ba, sai bayan bincike na musamman da wani masanin fannin mai suna Wilhem Johannsen, a shekarar 1911 ya gudanar. Wannan shi ne kwararre na farko da ya fara gudanar da bincike na musamman kan wannan fanni da yadda yake samuwa.
Ya gudanar da bincikensa ne kan tsarin gadon dabi’u da siffofin halitta tsakanin iyaye da zuriyarsu, da kuma yadda gadon ke kasancewa a aikace; wato boye da zahiri ke nan. Wajen tabbatar da yadda ’ya’ya ke gadon dabi’un halitta (wajen siffar tsawo da gajarta da dabi’un zuci da dabi’un halayya) ne ya gano cewa lallai akwai tasirin mahalli wajen samuwar wadannan abubuwa.
Bayan shi, masana da dama sun ci gaba da bincike don fadadawa tare da inganta wannan fanni ta hanyar binciken kwakwaf don kokarin tabbatar da wannan ka’ida ta ilimi.
Daga cikin shahararrun kwararru da aka sansu a wannan fanni akwai Richard Dawkins, wanda kwararren masanin ilmin kimiyya ne kuma marubuci. Dawkins dan kasar Ingila ne. Ya rubuta littattafai da dama kan fannin ilmin gadon dabi’u da siffofin halitta (Genetics).
Littafin da aka fi sanin Dawkins da shi shi ne wanda ya rubuta kan wannan fanni, mai suna: ‘The Edtended Genotype’. A cikin wannan littafi, Dawkins ya nuna cewa, a yayin da ake bayanin tasirin mahalli wajen haddasa sauye-sauye ga halittar dan Adam, ana takaituwa ne ga dabi’a ta zahiri, kuma ga wani mutum shi kadai. Wannan, a cewar Dawkins, nakasu ne ga wannan fanni, kuma shi ya sa ya rubuta wancan littafi don tabbatar da wannan kuskure. Dawkins ya kawo misalai masu gamsarwa da ke nuna yadda Nau’in dabi’ar Halitta ta Zahiri (Phenotype) ke samuwa ga wata halitta ta hanyar bayyana wata dabi’a da wata halitta daban ta yi, a inda ko mahallin da wannan halitta take. Wannan littafi dai ya samu karbuwa matuka, kuma kundi ne na musamman ga duk wanda ke son karin bayani a wannan fanni na ilimi.
Madogara
Malaman fannin Nau’in dabi’ar Halitta ta Zahiri sun nuna cewa wannan fanni na dogaro ga abubuwa guda uku ne. Abu na farko shi ne habaka ko bunkasar halitta ta zahiri. Wannan shi suke kira da suna ‘Debelopment’. Abu na biyu kuma shi ne madaukan jiki (musamman na cikin jiki), wadanda suka hadu suka samar da dan Adam. Wadannan sun hada da sinadaran jiki da sauran makamantarsu. Wannan bangare shi suke kira ‘Morphology’. Kalmar ‘Morphology’ tana da ma’anoni a fannonin ilimi guda biyu; da fannin ilimin harshe da magana (Linguistics). Sai fannin ilimin halitta (Biology).
Bayananmu sun ta’allaka ne ga bangaren ilmin halitta. Sai a kiyaye, kada mai karatu da ya kware a fannin ilimin harsuna ya ga wannan kalma da wannan ma’ana ya dauka akwai shirme cikin abin da ake magana a kai.
Sai bangare na uku, wato bangaren da ke lura da yanayin dabi’ar zamantakewa da dabi’ar halayya. Wannan shi kuma ana la’akari da shi ne wajen yanayin mu’amala tsakanin mutane. Ma’ana ba abu ba ne da a zahirin jikin mutum za ka gani, idan ba saninsa ka yi ba. Amma kuma yana bayyana idan bukatar hakan ta taso. Misali, idan mutum mai saurin fushi ne, ba kowa ke iya ganewa ba don ya gan shi a karon farko, ko ya hange shi daga nesa. Abin nufi, don kawai ka ga mutum, ba za ka iya cewa ga dabi’arsa ba kai tsaye, muddin ba saninsa ka yi ba. Wannan bangare shi suke kira ‘Behabiour’. Wadannan su ne bangarorin da wannan fanni na Nau’in dabi’ar Halitta ta Zahiri ke dogaro da su wajen tabbatar da hakikaninsa.
Tsarin Tabbatuwa
Don samun cikakkiyar fahimta kan ma’anar wannan fanni, zai dace mai karatu ya fahimci cewa, bangaren Nau’in dabi’ar halitta ta zahiri, kamar yadda muke gani, ba komai ba ne face “Fassarar” bayanan da ke cikin dabi’ar halittar kowane dan Adam (Genes). Idan mai karatu bai mance ba, mun yi bayani a baya cewa asalin bayanan da ke samar da hakikanin halittar mutum, kamar yadda ake haifarsa, suna kunshe ne gaba dayansu a cikin kwayar halitta (Cell). Wannan kwayar halitta na dauke ne da bangarori da dama. Daga cikin bangarorin akwai Ma’adanar Bayanan dabi’ar Halitta (Chromosome) ke nan.
Kowace kwayar halitta (Cell) na dauke ne da tagwayen “Ma’adanar Bayanan dabi’ar Halitta” (Chromosome) guda 23. Wannan ke nuna cewa a cikin jikin kowane dan Adam za a samu guda 46 ke nan (23 d 2 = 46). Dukkan wadannan ma’adanar bayanan dabi’ar halitta iri daya ne na jikin mutum daya, duk da yake kowane dan Adam nashi sun sha bamban da na waninsa. Kowane dayan tagwayen “Ma’adanar Bayanan dabi’a” kuma yana dauke ne da zaren “Madarar Bayanan dabi’ar Halitta” da ake kira “Deodyribonucleic Acid” ko “DNA” a takaice. Wannan zare a siffar sarka yake, mai harde da juna. Kuma a jikin layin wannan sakakken zare ne ake da “Kwayoyin dabi’ar Halittar” kowane dan Adam. Wadannan kwayoyin dabi’un halitta su ake kira “Genes”. Kowane dan Adam yana kebantuwa ne da kwayoyin dabi’un halitta daban da suka sha bamban da na wani, wadanda ya gado su daga wajen iyayensa ko kakanninsa ko kakannin kakanninsa, har dai abin ya kai ga Annabi Adamu da Hauwa’u, amincin Allah ya tabbata a gare su.
Za mu ci gaba