Tsarin hada-hadar kudi na tafi da-gidanka na Glo dchange ya bunkasa kasuwanci – Masu hada-hada

kungiyar Masu hada-hadar kudi na tafi-da-gidanka bisa shirin Glo dchange na Najeriya, ta yaba wa Kamfanin Gl;obacom saboda bullo da shirin sarrafa kudi ta hanyoyin sadarwa, al’amarin da suka bayyana a matsayin manufar inganta harkokin mu’amala da kudi ta cikin na’urorin sadarwa a Najeriya.daukacin ’ya’yan kungiyar masu hada-hadar aikewa da kudin, sun yi wannan yabon […]

Tsarin hada-hadar kudi na tafi da-gidanka na Glo dchange ya bunkasa kasuwanci – Masu hada-hada

kungiyar Masu hada-hadar kudi na tafi-da-gidanka bisa shirin Glo dchange na Najeriya, ta yaba wa Kamfanin Gl;obacom saboda bullo da shirin sarrafa kudi ta hanyoyin sadarwa, al’amarin da suka bayyana a matsayin manufar inganta harkokin mu’amala da kudi ta cikin na’urorin sadarwa a Najeriya.
daukacin ’ya’yan kungiyar masu hada-hadar aikewa da kudin, sun yi wannan yabon ne a dakunan taron horarwa daban-daban, wadanda suka hada da na Ibadan da Binin da Abuja da Fatakwal da Ikeja da Lekki a Jiahr Legas, cikin karshen makon da ya gabata, inda suka bayyana tsarin Glo dchange a matsayin al’amarin da ya inganta harkokin samun abin hannunsu, sannan ya bunkasa harkokin kasuwancinsu.
Mista Raphael Arokoyo na Kamfanin Real Imagination, wanda ya halarcin taron da aka gudanar a Ikeja ta Jihar Legas, cewa ya yi, “Wannan tsari ne na bunkasa tattalin arziki ga ’yan Najeriya,” inda ya yi nuni da kwarin gwiwarsa wajen ganin karbuwar tsarin aikewa da kudi na tafi-da-gidanka.
“Babu wata harkar kasuwanci da ba tattare da matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya. A lokacin da aka bullo da amfani da katin zarar kudi na ATM , an sha wuya kafin ya samu karbuwa, amma a yau, shirin ya samu karbuwa. Don haka, ina ganin idan Kamfanin sadarwa na Glo da sauran abokan huldarsa suka kafu kan manufa mai kyau, jakar kudin tafi da gidanta (mobile wallet) za ta zama hanya mafi inganci,” inji shi. Arokoyo, ya ce abin farin ciki a gare shi game da wannan tsari, shi ne, babu shinge, inda ya bayyana cewa, “jakar kudin tafi-da-gidanka na da saukin aiwatarwa, ba ta bukatar wani zurfin ilimi. Matukar mai amfani da tsarin ya iya amfani da wayar hannu, to zai iya gudanar da harkokin kasuwanci a wannan tsarin.”
Ya ce: “Ba a bukatar kudin jari don fara kasuwanci. Tallafin Glo da tambarin kasuwancinsa a jikin shaguna, zai sanya a takaita kashe kudi.”
Wata mai amfani da wannan tsari,  Misis Eucharia Ajaegbu, wadda ke da kantin sayar da kayan masarufi a unguwar Ojo-Alaba da ke Jihar Legas, ta ce tsarin Glo dchange wani ci gaba ne da aka yi amanna da shi, don “zai saukaka hada-hadar kasuwanci. Sannan ya bunkasa samun masu kananan sana’o’i. Ina son shirin, ina kuma fatan ganin ya ci gaba,” inji ta.
Misis Mercy Nanamani, wata malamar makaranta, kuma mai cinikin kayan masarufi a Ojo-Alabal, ta ce: “Tsarin Glo dchange ba ya bukatar kudin fara kasuwanci (wani jari mai yawa). Da zarar an samu tallafin glo sun yi zayyanar alamar kamfanin a kantuna, to ana samun saukin aiwatartawa, ba tare da wata damuwa ba. Ina da tabbacin cewa shirin zai bunkasa,” a cewarta.
A jawabin wani mai shirin fantsama a hada-hadar shirin a Lekki, lokacin da aka bai wa mutane horo, Mista Osita Udoye, ya bayyana cewa da ya saurarin jawaban da aka gabatar, ya tabbatar “glo dchange na da kyau da samar da riba ga masu hada-hada.”
Shi ma Aled Muia, wani kwararren kan harkar aikewa da kudi ta na’urar tafi-da-gidanka a Kamfanin Globacom, ya bayyana wa mahalarta taron horarwa a birnin Binin, cewa, “dimbin mutane suka shiga cikin hada-hadar aikewa da kudi ta wayar tafi-da-gidanka, lokacin da aka bullo da shirin a kasar Kenya, wadanda a halin yanzu suka zamo hamshakan attajirai masu miliyoyi ta irin wadannan hanyoyi.”
“Abin da kawai ake bukata ga mutum ya zama jami’in aikewa da kudi na tsarin Glo dchange, shi ne ya samu dan karamin shago a gefen titin da ke unguwarku, sai kawai ka zama banki a al’ummarku, inda za ka rika zama don rajisatar abokan hulda, kana karbar kudi, kana kuma biyan masu karba, kamar yadda ake yi a banki,” inji shi.
Muia ya ce “yin rajistar zama jami’I, abin da kawai ake bukata ga mutum, shi ne ya dauki wayarsa ta hannu, ya aike da sakon tes na sunansa na farko/da na karshe/da birni/da jiha zuwa ga lambobi kamar haka 33003 ko 08150033003, ko kuma ya ziyarci kantin Gloworld mafi kusa ko shafukan sadarwar intanet na www.Gloworld.com/Mobilemoney.”
Bankuna da aka yi hadin gwiwa da su, sun bayyana a wuraren bayar da horo don yin rajistar jami’an. Mafi yawan wadanda suka halarci taron sun cika takardun shiga tsarin aikewa da kudi na tafi-da-gidanka, da kuma kungiyar jami’an hada-hadar Glo dchange Network. A cewar Shugaban sashen Hada-hadar Kasuwancin tafi-da-gidakan a kamfanin Globacom, Mista Esaie Diei, jami’an hada-hadar aikewa da kudi a tsarin Glo dchange, na da rubi biyu na sana’arsu, inda za su kasance masu dillancin katin waya na glo. Wannan tsari na Glo dchange tare da hadin gwiwar masu hada-hadar aikewa da kudi bisa tsarin tafi-da-gidanka, zai kasance wani ala’amari karbabbe a rayuwar ’yan Najeriya ta yau da kullum, saboda zai rika kusanta su da hanyoyin hada-hadar sarrafa kudi cikin sauki a unguwanninsu.
Tsarin aikewa da kudi na Glo dchange na da saukin aiwatarwa, kuma ga kariyar tsaron dukiya da ake gudanarwa a cibiyoyin hada-hadar kudi daban-daban, inda ake amfani da wayar hannu a matsayin asusun zuba kudi ko wurin fitarwa ko aikewa da su, har ma da biyan kudin wutar lantarki. Wannan tsari dai Kamfanin Globacom ne ya kaddamar da shi, tare da hadin gwiwar cibiyoyin hada-hadar sarrafa kudi na tafi-da-gidanka, don bai wa ’yan Najeriya damar amfani da wayoyin hannunsu, wajen aikewa ko karbar kudi, ko sayen katin waya ko kayan bukatun yau da kullum ko biyan ladar kwadago da kudin wutar lantarki da ruwan famfo da katin tashahohin talabijin na tauraron dan Adam a sassan kasar nan daban-daban.