Tsarin iyali da takaita haihuwa munanan abubuwa ne
Akwai wani abokina da yake goyon bayan tsarin iyali da takaita haihuwa, yana da ’ya’ya biyu, mace da namiji. A kwanan nan ne dan nasa guda mai shekara 23 ya mutu, saura ’yarsa daya ke nan. A matsayin ta’aziyyata, na kuduri aniyar bijiro da wata lacca da na taba gabatarwa shekaru biyu da suka gabata, […]
Akwai wani abokina da yake goyon bayan tsarin iyali da takaita haihuwa, yana da ’ya’ya biyu, mace da namiji. A kwanan nan ne dan nasa guda mai shekara 23 ya mutu, saura ’yarsa daya ke nan. A matsayin ta’aziyyata, na kuduri aniyar bijiro da wata lacca da na taba gabatarwa shekaru biyu da suka gabata, a wani taron matasan Kiristoci maza da mata. A cikin laccar, na yi bayani ne dalla-dalla game da munin da ke tattare da tsarin iyali da takaita haihuwa.
A zamanin da, babu wani abu tsarin iyali ko takaita haihuwa, domin kuwa mutane suna tsoron Allah, don haka suna bin umurninSa na cewa a hayayyafa, a cika duniya da al’umma. Haka kuma mutane a lokacin sun yi imani da Allah cewa Shi ne mai ciyarwa da shayarwa, Shi ne mai kariya da daukaka ’ya’yan da ya ba su. Saboda wannan imani da suke da shi, ba su yin wani kokari ko shisshigin tsara iyali ko takaita haihuwa.
Sun dauki misali daga Annabi Yakuba, Shugaban Isra’ilawa, wanda Allah Ya ba ’ya’ya 12 daga matansa biyu da kwara-kwarai biyu. A misali, da a ce ya tsara iyali, ya takaita haihuwa zuwa ’ya’ya biyu ko uku, kamar yadda a yanzu ake yi; da bai samu damar haihuwar dansa na hudu ba, wato Yahuza, wanda daga bisani ya zama Shugaban Isra’ilawa. Haka kuma da bai samu damar haihuwar dansa na 11 ba, wato Annabi Yusuf – mutumin da ya zama abin kauna a duniya, ya kasance mai gaskiya da amana. Mutumin da ya zama dan lelen babansa amma ya gamu da jarabawa, lokacin da ’yan uwansa saboda kishi suka jefa shi a tsohuwar rijiya. Bai mutu ba amma bayan ya tsira kuma aka sayar da shi ga bauta, daga bisani kuma ya shiga tarko da makircin mata, wanda ya jaza aka daure shi a jarun ba da hakki ba. Bayan dukkan wannan jarabawa, ya zo ya zama hamshakin mai mulkin daular da ta fi kowace daula ta lokacinta shahara a duniya.
Idan da a zamanin da an yi tsarin iyali da takaita haihuwa, da kila ba mu ji duriyar wasu shahararrun mutane ba da duniyar nan ta samar. Mutane masu tarihi kamar Annabi Musa da Isa (AS) da sauransu da dama da suka yi wa al’umma hidima ta fuskar siyasa, addini, kasuwanci da kere-kere, da mai yiwuwa ba a samar da su ba, idan da iyayensu sun yi tsarin iyali ko sun takaita haihuwa. Da ba su zo duniya ba kuwa, lallai da al’umma sun yi asarar dinbim gudunmowarsu.
Kamar yadda tarihi ya tabbatar a cikin baibul, yadda Fir’auna ya ba da ummurnin cewa duk da namijin da aka haifa, a halaka shi a zamaninsa, a rika barin ’ya’ya mata. Wannan hukunci ya sanya maza suka kaurace wa matansu na aure, saboda suna ganin cewa babu dalilin da zai sanya su rika haihuwa ana kashewa. Daga bisani mahaifin Musa ya canja tunani, ya dawo wa matarsa suka samu nasarar haihuwar Musa, wanda Allah cikin ikonSa ya raya shi, ba tare da Fir’anuna ya samu nasarar halaka shi ba. Yanzu da a ce mahaifin Musa bai canja ra’ayi ba, anya za a same shi? Amma sai ga shi ya kasance daya daga cikin mashahuran manzannin Allah. Ya yi gagarumar hidima ga al’umma.
Daga dukkan tarihe-tarihen da muka samu, za mu fahimta da cewa ba bisa kuskure ake halittar yara ba. Allah Yana halittar yara ne bisa yadda ya tsara, yadda ya kadarta. A lokacin da magidanci ya ce ba zai haihu ba, zai tsara iyali, wato zai takaita haihuwa, to ya sani yana fada ne da tsarin Allah, ma’ana Ya yi wa Allah laifi ke nan. Duk wani mutum da zai zo duniyar nan, yana da irin nasa amfanin ga kansa da kuma al’ummar da ya fito cikinta, don haka ba daidai ba ne iyaye su ce za su hana shi zuwa duniya. Duk wani mutun da Allah Ya yi nufin halitta ko kuma ya ma halitta, yana da dalilinsa na yin haka. Domin kuwa Allah ba ya halittar banza. Kowa yana da amfani irin nasa, wanda shi kadai zai iya aiwatar da shi, ba wani ba.
Akwai wani lokaci can da na shiga cikin wata jarabawar rayuwa, sai wani wasu abokaina suka same ni da shawarar cewa wai ya kamata in zubar da cikin da matata take dauke da shi a lokacin. Sun fada mini haka ne wai ta la’akari da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta. Wai idan ta zubar da cikin, wannan zai rage mana wahala, sannan kuma ya hana yaron da za a haifa fadawa cikin matsala. Ni kuwa na yi watsi da muguwar shawararsu. A kullum na kalli yaron nan da na haifa, nakan lura da irin baiwar da Allah Ya ba shi, wadda ke sanya ni farin ciki. Kuma ina da yakinin cewa zai daukaka a rayuwa. Ina godiya ga Allah da ya ba ni ikon daurewa har aka haife shi kuma da ya ba ni ikon bijire wa gurguwar shawarar abokai.
Kamar yadda ana sha fadi a mukalolina a can baya, takaita haihuwa abu ne marar kyau, domin kuwa kisan kai ne. Takaita haihuwa tana haifar da illa ga al’umma da iyali, kuma tana jaza kuna da ciwo ga ita kanta matar da ke dauke da cikin. Haka kuma, idan aka ce ma zubar da cikin za a yi, yana iya haddasa matar ta mutu. Don haka, haihuwa baiwa ce kuma kyauta ce ga iyaye da al’umma gaba daya, a yayin da takaita haihuwa illa ce ga al’umma.