Tsarin karba-karba ya kawo tangarda wajen zaban Ooni
Zuriyar gidan sarautar Geisi a masarautar Ife, sun ce su ne suka cancanci fito da sabon Ooni na Ife domin layi ya zo kansu kamar yadda tsarin karba-karba a tsakanin gidajen sarautu 4 ya tanadar. Sun ce Ooni na karshe da ya fito daga gidan sarautar ta Geisi, Oba Derin Ologbenla, ya yi mulki ne […]
Zuriyar gidan sarautar Geisi a masarautar Ife, sun ce su ne suka cancanci fito da sabon Ooni na Ife domin layi ya zo kansu kamar yadda tsarin karba-karba a tsakanin gidajen sarautu 4 ya tanadar.
Sun ce Ooni na karshe da ya fito daga gidan sarautar ta Geisi, Oba Derin Ologbenla, ya yi mulki ne a tsakanin shekarun 1880 zuwa 1894. Saboda haka yanzu lokaci ya yi da gidan sarautar Geisi, zai fito da Yarima da zai yi mulki a matsayin sabon Ooni na Ife.
Mai magana da yawun gidan sarautar Geisi, Yarima Kunle Adelowo, ya yi wannan ikirari ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Osogbo. Yariman ya ce, dokar gwamnatin jiha ta shekarun 1977 da 1980 a kan nadin sabon Ooni na Ife, sun amince da gidajen sarautu 4 na Osinkola da Ogboru da Geisi da Lafogido su kasance gidajen da za su rinka fito da sabon Ooni.
Ya ce gidan sarautar Osinkola ne ya fito da Oba Adesoji Aderemi da ya yi mulki na tsawon shekaru 50 da Oba Okunade Sijuwade daga gidan sarautar Ogboru ya gaje shi.
Wani dattijo mai shekaru fiye da 80 mai suna Pa O. Oyekanmi, dake zaune a masarautar Ife ya roki masu zaben sabon sarkin kada su yarda ‘yan siyasa su tsoma musu baki a cikin al’amarin nada sabon Ooni na Ife domin al’amari ne da bai shafe su ba.
“Muddin kuka kyale ‘yan siyasa suka yi amfani da ku wajen tsoma baki a cikin wannan muhimmin al’amari to kuwa martabar masarautar Ife a idanun duniya zai gushe domin kara bata al’amarin za su yi ba gyara ba. Kamata ya yi a kyale masu zaben sabon Ooni na Ife su gudanar da aikin su kamar yadda al’adun zaben sabon sarki da aka yi gadonsu kaka da kakkani suka tanadar”. Pa O. Oyekanmi ya ce.