Tsarin Ma’adanar Bayanai a kimiyyance (2)
A makon jiya, mai karatu ya samu mukaddima kan yadda dan Adam ya fara wayar da kansa sanadiyyar kalubalen rayuwa da yake samu yau da gobe, cikin abin da ya shafi tsarin adanawa da taskance bayanai; daga taskance su a kwakwalwarsa zuwa taskance su cikin ababen da ke muhallinsa. A karshe dai, sabanin lokutan baya, a […]
A makon jiya, mai karatu ya samu mukaddima kan yadda dan Adam ya fara wayar da kansa sanadiyyar kalubalen rayuwa da yake samu yau da gobe, cikin abin da ya shafi tsarin adanawa da taskance bayanai; daga taskance su a kwakwalwarsa zuwa taskance su cikin ababen da ke muhallinsa. A karshe dai, sabanin lokutan baya, a wannan zamani dan Adam ya nemo wasu hanyoyi masu sauki da ban mamaki da yake bi wajen taskance bayanai da kuma nemo su cikin sauki ba tare da matsala ba. Dangane da haka muke nazari na musamman kan ire-iren wadannan hanyoyi ko kayayyakin adanawa da taskance bayanai da dan Adam ya kirkira, inda za mu fara nazari kan tsari da kintsin da ke cikin Fasahar Faifan CD wato Compact Disc Technology ke nan a Ingilishi. Amma kafin mu dulmiya cikin tsarin Fasahar Faifan CD, zai dace mu yi waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira adon tafiya.
Faya-fayen Garmaho (Gramophone Records)
A tabbace yake cewa kafin bayyanar wani abu mai suna “Faifan CD” da dama cikinmu mun san cewa fasahar da ta shahara ita ce Fasahar Faifan Garmaho ko Gramophone Records, kamar yadda yake a Ingilishi. Wannan fasaha ce da ke amfani da faifai mai kama da Faifan CD da muka sani a yau, amma sai dai shi Faifan Garmaho yaf i fadi da nauyi da kuma inganci. Na san wadanda suka taba amfani da dukan biyun za su shaide ni kan haka. Faifan Garmaho ya fi tsawo da fadi da kauri da nauyi da kuma inganci. Bayan haka, na’urar da ke sarrafa faifan don jiyar da mai sauraro ma ta sha bamban da irin wacce muke amfani da ita a yau wajen sauraron Faya-Fayen CD.
Abin da Faifan Garmaho ya rasa shi ne, ba ya iya taskance hotuna masu motsi (bidiyo), sai dai sauti kadai. Sannan kasancewar ilimin fasahar da ke wancan zamani bai fadada irin na yau ba; yawan wakokin da Faifan Garmaho ke taskancewa bai kai irin na Faya-Fayen CD ba a yau. Amma duk da haka, zamanin da Faifan Garmaho ya dauka a duniya yana cin duniyarsa da tsinke, ko kadan Faifan CD bai yi ba. Domin wannan fasaha ta kwashe shekaru kusan dari tana yayi ba tare da abokiyar hamayya ba.
Wannan tsawon zamani da ta kwashe bai rasa nasaba da rashin wata fasaha da za ta iya kalubalantarta wajen inganci ne da kuma tsari da kintsi ba. Fasahar ma’adanar bayanai da ta yi kusan zamani daya da Faifan Garmaho ita ce Fasahar BHS, wato kaset din bidiyo mai amfani da na’urar Bideo Machine wajen nuna abin da ke taskance a ciki. Kuma kasancewar mahanga da kuma tsarin kowanne ya sha bamban, sai dukan fasahohin biyu suka ci gaba da rayuwa gefe-da-gefe ba tare da wata hamayya ba. Sai wajen shekarun 1970 zuwa 1980 ne aka fara samun sauyin tunani daga kamfanoni irin su Sony da Philips da ke kasar Jamus da Japan, lokacin da suka kafa kwamitoci a lokutan daban-daban, don nemo hanyar samar da wata sabuwar fasaha da ta sha bamban da Faifan Garmaho.
Cikin 1982 aka samar da Fasahar Faifan CD ta farko, wacce kamfanonin biyu suka kirkira a lokuta daban-daban, inda kuma kowanne daga cikinsu ya yi amfani da irin tasa kwarewar, ba tare da la’akari da tsarin da dan uwansa ke amfani da shi ba. Kasancewar kowanne daga cikin kamfanonin biyu yana kera na’urorin da ake amfani da su wajen sauraro ko kallo ko kuma amfana da bayanan da ke cikin ma’adanan, sai kowanne ya yi amfani da tsarin da sai na’urar da ya kera kadai za ta iya jiyarwa ko nuna hotunan da ke cikin faifan da ya kera. Wannan ya sa aka samu matsala, inda a karshe dai dole suka zauna suka kafa kwamiti na hadin-gwiwa da ya tsara ingantacciyar hanyar warware wannan matsala.
Wannan kwamiti ne ya fitar da wasu tsare-tsare cikin wani littafi ko rahoto da ya kira “The Red Book” wanda kuma tsare-tsaren ne suka samar da irin Faya-Fayen CD da muke amfani da su a yau. Ko shakka babu, bayyanar Fasahar Faifan CD ne ya kashe wa Faifan Garmaho kasuwa gaba daya. To yaya tsarin Faifan CD yake? Kuma me ya ba shi irin wannan tasiri a kan Faifan Garmaho?
Ma’anar Faifan CD
Da farko dai, Faifan CD, ko Compact Disc a Ingilishi, faifai ne mai amfani da kyallin idon lantarki (Optical Light) don taskance bayanai a tsarin sarrafa bayanai na zamani (digital format). Bayan ya taskance, akan yi amfani da na’urar CD Player wajen kallo ko sauraron bayanan da ya taskance a wannan tsari. Faya-Fayen CD na asali an kera su ne don taskancewa da kuma jiyar da sauti ko murya na wakoki ko laccoci kadai (Audio CDs) kuma sun samo asali ne tun 1982, kamar yadda bayanai suka gabata a baya. Girman Faifan CD duk bai wuce milimita dari da ashirin (120mm) ba, kuma kana iya sauraren wakoki ko kallon bidiyo na tsawon minti tamanin (80mins), ko zuba tsantsar bayanai (kamar kasidu ko makaloli) da mizaninsu ya kai miliyan dari bakwai, wato 700MB ke nan a mizani ko ma’aunin adana bayanai na kwamfuta.
Da tafiya ta yi nisa sai aka sauya girma da tsarinsu, inda aka kera kanana masu daukar wakokin tsawon minti ashirin da hudu (24mins), masu girman milimita tamanin (80mm). Wadannan su ake kira Mini CDs. Na farkon kuma su ake kira Standard CDs. Da zamani ya kara nisa, ilimin fasahar sadarwa ya kara fadi, harkar kade-kade da wake-wake ta bunkasa, harkar fina-finai ta tumbatsa, sai kamfanonin kera faya-fayen CD suka fara yawaita. Wannan ya haifar da samuwar nau’ukan faya-fayen CD masu tsari daban-daban.
Kamar yadda bayani ya gabata a baya, Faifan CD na farko an yi shi ne don taskancewa da kuma sauraron wakoki kadai. Amma bunkasar ilimin sadarwa da kere-kere ya sa an samu wasu nau’uka irin su Faya-fayen CD masu dauke da manhajar kwamfuta, wato CD-ROM, wadanda kuma sai a kwamfuta kadai ake iya amfani da su. Akwai kuma nau’in CD-R, wato CD Recordable, wanda ake iya taskance bayanai a ciki sau daya. Su kuma ana iya sanya kowane nau’in bayanai ne a cikinsu. Abin da aka zuba a ciki na bayani, shi ke iya bayar da damar sanin irin na’urar da za a yi amfani da ita wajen nunawa ko sauraro ko kuma amfani da nau’in abin da aka zuba. Akwai kuma CD-RW, wato CD Re-writable, wadanda kana iya zuba bayanai a ciki sama da sau daya, ka goge, ka sake zubawa. Amma tsarin CD-R da zarar ka sanya a karo na farko shi ke nan.
Sai kuma tsarin BCD, wato Bideo CD ke nan, wadanda ke dauke da hotuna masu motsi, wato bidiyo. Nau’i na karshe da za mu kawo shi ne nau’in CD da ke taskance hotuna. Su wadannan musamman wasu kamfanoni ke kera su don zuba hotuna a ciki; kamar dai album ke nan. Wadannan nau’in su ake kira Photo CD. Samuwar wadannan nau’uka ko shakka babu ya kara wa Fasahar Faifan CD shahara nesa ba kusa ba, inda a shekarar 2004 aka kiyasta cewa an sayar da Faya-Fayen CD masu dauke da wakoki, har sama da biliyan talatin. A shekarar 2007 kuma wannan adadi ya karu, inda kamfanonin da ke wannan sana’a suka ce an sayar da akalla faya-fayen har guda biliyan dari biyu.
Duk da cewa faya-fayen CD sun shahara a hannun mutane a duniya baki daya a lokacin da suke tashe, ba dukan masu amfani da wannan fasaha suka san hakikaninsa ba. Da me aka kera Faifan CD? Ba kowa zai ba ka wannan amsa ba. Muna dai amfani da shi ne a tsarin nan na Black Bod kawai; wato “A ci baure, amma ban da tona cikinsa.” Amma kuma duk da cewa lokaci ko zamanin Faifan CD ya kusan wucewa, sanin tsari da kintsin wannan fasaha zai kayatar da mai karatu sosai. Akwai abin al’ajabi sosai, musamman kan abin da ya shafi ilimin da aka yi amfani da shi wajen kerawa da kuma tsara wannan fasaha shahararriya. Har wa yau, sanin tsari da kintsin wannan fasaha na Faifan CD zai rage wa mai karatu zangon karatu, idan muka zo yin bayani kan tsarin Faya-fayen DBD nan gaba in Allah Ya so. A yanzu ga takaitattun bayanai kan yadda tsari da kuma kintsin Faifan CD yake.
Tsari da kintsin Faya-Fayen CD
Kowanne daga cikin nau’ukan Faifan CD da bayaninsu ya gabata a sama, ana kera su ne daga gasasshen roba nau’in Ploycarbonate, kuma nauyin kowanne daga cikinsu giram goma sha shida ne (16g), mai kuma kaurin milimita daya da digo biyu (1.2mm). Idan ka yi rigingine da Faifan CD daidai fuskar da ke kyalli, za ka samu bangarori guda shida da yake takama da su. Wadannan bangarori sun faro ne daga ramin da ke tsakiyarsa, zuwa bangaren karshe mai kyalli da ke gefen kowane CD. Bangaren farko shi ne ramin da ke tsakiyarsa, wanda a harshen Turanci ake kira Spindle. Wannan rami shi ne ke rike sandar na’urar da ke sarrafa faifan a lokacin da ake kallo ko sauraron abin da Faifan ke watsawa na sauti ko hotuna masu motsi da yake nunawa. Sai kuma bangare na biyu da ke farfajiyar ramin, mai kama da gilashi. Wannan shi ake kira Clamping Ring. Kamar yadda mai karatu ya sani kuma ya gani, wannan gilashi na gewaye ne da ramin da ke rike sandar na’urar CD Player.
Sai bangare na uku dake biye da shi, wato Stacking Ring, wanda shi ma a gewaye yake. Sai kuma bangare na hudu mai suna Mirror Band, wato da’irar da ke biye da bangare na uku ke nan, mai kama da madubi, mai daukar ido. Daga shi kuma sai bangare na biyar, wato bangare mafi fadi ke nan, kuma wanda ke taskance bayanan da ake zubawa a cikin Faifan. Wannan bangare kuwa shi ake kira Data, kuma shi ne ya faro daga jikin Mirror Band, har zuwa gab da karshe ko gefen Faifan. A karshe kuma sai bangare na shida, wanda shi ne layin da mai karatu ke gani a gefen Faifan CD mai kyalli, siriri, mai kaifi. Wannan shi ake kira Rim a turance.
Wadannan su ne bangarori guda shida da kowane Faifan CD ke dauke da su, kuma su ne kayan aikinsa. Bayan haka, idan ka juya Faifan kowane CD, za ka samu tambari ko wata alama ko rubutu da ke dauke da suna ko tambarin kamfanin da ya sana’anta ko kera shi. Kafin a buga wannan tambari ko rubuta duk abin da aka rubuta a bangon kowane CD, sai an zuba ruwan tagulla (aluminium) mai kyalli, da kuma sinadaran kimiyya nau’in Lackuer, mai daukar ido, sannan a maka tambarin a samansa. Wannan bai tsaya kan Faya-Fayen CD da ke zuwa dauke da bayanai kai tsaye daga kamfanonin da suka kera kadai ba, a a, hatta sababbi wadanda babu komai a cikinsu. Duk suna dauke ne da wadannan sinadarai da bayaninsu ya gabata.