Tsarin Ma’adanar Bayanai a Kimiyyance (7)
Na’urar Sarrafa Faifan DBD Faifan DBD da CD da ma na garmaho da bayanansu suka gabata a makonnin baya, suna dauke ne da rubutattun bayanai ko sauti ko hotuna daskararru (Still Images), ko kuma hotuna masu motsi, wato bidiyo ke nan. Wadannan bayanan dai ba a iya ganinsu sai an tsofa faifan a cikin wata […]
- Na’urar Sarrafa Faifan DBD
Faifan DBD da CD da ma na garmaho da bayanansu suka gabata a makonnin baya, suna dauke ne da rubutattun bayanai ko sauti ko hotuna daskararru (Still Images), ko kuma hotuna masu motsi, wato bidiyo ke nan. Wadannan bayanan dai ba a iya ganinsu sai an tsofa faifan a cikin wata na’ura wacce ke sarrafa su don su bayyana ga mai kallo ko mu’amala da su ya gan su, ko ya samu damar yin mu’amala da su. Na’urar da ke da alhakin sarrafawa tare da bayyana wadannan bayanai na CD da DBD dai ita ake kira: “CD Player” idan na faifan CD ce, ko kuma “DBD Player,” idan na faifan DBD ce. Kowanne daga cikin wadannan aikinsa daban, duk da cewa na’urar CD Player aka fara qirqira a farko.
Kafin nan, yana da kyau mai karatu ya fahimci cewa ita fasahar Faifan DBD, kamar yadda qasidar makon jiya da na shekaranjiya suka tabbatar, mizaninta ya dara na fasahar faifan CD wajen girma da armashi da kuma yalwa wajen sarrafa bayanai. Kowane faifan DBD na taskance bayanai ne a wasu ramuka ko koguna da suke fuskar faifan, qanana, wadanda na’urar sarrafa faifan ce kadai ke iya hanga da riskar abin da ke dauke cikinsu. Wadannan ramuk ko koguna su ake kira: “Tracks” a harshen fasahar sadarwa na zamani. Fuskar faifan DBD na dauke da wadannan ramuka ne masu dimbin yawa, iya gwargwadon girma da mizanin faifan. Kowane rami ko kogo daga cikin wadannan ramuka na iya daukar bayanai miliyan biyu ne da dubu dari hudu da goma sha takwas, wato: (2,418 bytes, ko 2.4MB ke nan). Da zarar wannan rami ko kogo ya toshe sanadiyyar qura ko datti ko wani karta da ta samu faifan, to, na’urar ba ta iya sarrafa bayanan da ke wannan kogo. Shi ya sa za ka hotuna ko sautin na kakkaryewa, ba sa bayyana daidai, wato: “Cracking” ke nan.
A jumlace dai, an qirqiri na’urar sarrafa faifan CD da DBD nau’i biyu ne, kuma kowanne daga cikin wadannan nau’o’i na da wasu nau’o’i na musamman da ake amfani da su ta wasu na’urorin sadarwa daban. Ga taqaitaccen bayani nan kan kowanne daga cikinsu.
Na’urar CD Player
Ta farko daga cikin nau’ukan na’urar da ke sarrafa wadannan fasahohi dai ita ce ake kira: “CD Player.” Wannan na’ura ce aka qirqira tun farkon bayyanar fasahar CD, don sarrafawa da kuma bayyana bayanan da ke dauke cikin faifan, ga masuamfani da shi. Na’urar CD Player na’ura ce ta musamman da aka qera, wato: “Standalone Debice,” kuma ake sayarwa ga masu buqatar mu’amala da faifan CD a wancan lokaci. Kuma kamfanoni da dama sun qera wannan na’urar, musamman kamfanonin da ke da ruwa-da-tsaki wajen samar da asalin fasahar CD din, irin su: Toshiba da Sony da Philips da ma wasu kamfanoni da suka shiga harkar daga baya.
Na’urar sarrafa faifan CD dai ta kasu kashi-kashi, ta la’akari da inda ake amfani da ita. Kamar yadda bayani ya gabata a sama, ta farko ita ce wacce aka qera mai zaman kanta, wacce za ka je kasuwa ka saya, don amfani da ita kai -tsaye a jikin talabijin dinka. Sai nau’i na biyu wacce ke zuwa a jikin kwamfuta. Wannan ita ake kira: “CD ROM.” Ita kam ko ka saya, muddin ba a kwamfuta ka sanya ba, ba ka iya amfani da ita. A taqaice dai, ta kebanci kwamfuta ce kadai. Akwai kafa ta musamman da aka tanada a jikin kwamfuta, wadda a nan ake tsoka ta. Wannan nau’i na na’urar CD dai ta sha bamban da ta asalin, domin fasaharta daban take. Bayan nuna bidiyo da sarrafa sauti, na’urar CD ROM tana iya sarrafa hotuna da rubutattun bayanai da kuma manhajar kwamfuta. Amma na’urar CD da za ka iya saya a kasuwa ka jona da talabijin din gidanka ba ta iya sarrafa faifan CD mai dauke da rubutattun bayanai ko manhajar kwamfuta.
Sai nau’in na’urar CD da ke zuwa a jikin mota, ita ma dai kamar ta asalin na’urar CD ce; tana iya sarrafa sauti ne da bidiyo, amma ba ta iya sarrafa faifan CD mai dauke da rubutattun bayanai ko manhajar kwamfuta. Wannan na’ura dai an girka ta ce a jikin motocin da aka qera a lokacin da wannan fasaha ta faifan CD ke yayi. Don haka, ko da ka je kasuwa ka sayo, idan ba a mota ka dora ba, ba a iya amfani da ita a talabijin.
Sai nau’in na’urar CD na qarshe wacce ita ma mai zaman kanta ce, amma ta sha bamban da asalin na’urar da aka fara qerawa. Wannan na’urar dai tana dauke ne da muhallin dora faifan CD da kuma wasu ’yan qare-qare masu qayatarwa, irin su rediyo da sauransu. Duk da cewa ba ta shahara ba sosai a wannan bangare na qasashenmu ba, amma tana cikin jerin nau’o’in na’urar da suka shahara a qasashen Turai da Amurka. Kuma ita ake kira: “Portable CD Player.” Kamfanoni da yawa sun qera wannan nau’i na na’urar CD sosai, kuma har yanzu ana amfani da su. Ba su da girma sosai; kana iya sanya su cikin jaka, kuma suna dauke da talabijin dinsu (Display Screen), wanda hakan ke nufin ba ka buqatar talabijin don amfani da su. Sai dai su ma, kamar nau’in na’urar CD ta mota ce, sauti da bidiyo kadai suke iya sarrafawa, ban da rubutattun bayanai da manhajar kwamfuta.