Tsarin Ma’adanar Bayanai a Kimiyyance (8)
Matashiya A makon jiya bayani ya gabata kan nau’o’in na’urar sarrafa faifan CD, inda mai karatu ya ga bambance-bambancen da ke tsakanin wacce aka kera a farkon zamani, mai zaman kanta da wacce ke dauke kan kwamfuta da na mota, sai kuma wadanda aka kera masu tafi-da-gidanka, wadanda ba sa bukatar talabijin wajen amfani da […]
Matashiya
A makon jiya bayani ya gabata kan nau’o’in na’urar sarrafa faifan CD, inda mai karatu ya ga bambance-bambancen da ke tsakanin wacce aka kera a farkon zamani, mai zaman kanta da wacce ke dauke kan kwamfuta da na mota, sai kuma wadanda aka kera masu tafi-da-gidanka, wadanda ba sa bukatar talabijin wajen amfani da su. Duk da cewa suna sarrafa bayanan da ke dauke cikin faifan CD ne, sai dai wasunsu sun fi gamewa wajen amfaninsu; wasu kan sarrafa nau’in sauti da bidiyo ne kadai, kamar yadda bayani ya gabata. A yayin da wasu kuma ke iya sarrafa sauti da bidiyo da rubutattun bayanai da kuma manhajar kwamfuta. A wannan mako cikin dacewar Ubangiji, za mu dora daga inda muka dakata.
Na’urar “DBD Player”
Wannan ita ce na’urar da aka samar tare da fasahar DBD. Bayani ya gabata cewa fasahar DBD ta biyo bayan fasahar CD ce, wadda sanadiyyar nakasun da suka bayyana na rashin juriya da rashin karko da kuma karancin mizanin ma’adana, aka samu canji da fasahar DBD. Samar da faifan DBD ya haifar da samuwar na’urar sarrafa faifan DBD, kamar yadda samar da faifan garmaho ya haifar da samuwar na’urar sarrafa faifan garmaho (Gramophone Player), a lokuta ko zamanin baya.
Na’urar sarrafawa da bayyana bayanan da ke dauke cikin faifan DBD ita ake kira: “DBD Player”. Wannan na’ura ta dara na’urar sarrafa faifan CD, saboda bambancin nau’in bayanan da faya-fayan ke dauke da su da kuma bambancin asalin fasahohin da aka yi amfani da su wajen samar da su. Na’urar DBD Player na amfani da nau’in hasken lantarki na leza ne, wato: “Laser Light,” launin ja, wajen karba da sarrafawa da kuma bayyana bayanan da ake zuba mata a farkon lamari ko a duk sa’ar da aka tashi sabunta su, idan faifan nau’in “Re-Writable” ne, wato: DBD-WR. Wannan tsari ya dara na CD nesa ba ku sa ba. Sannan yana dauke ne da fasahar da ke iya tsallakawa daga fallen farko zuwa falle na biyu, idan faifan mai tagwayen falle ne, wato: “Double Layer DBD.”
Na’urar sarrafa DBD na zuwa nau’i-nau’i ne. Akwai nau’in gama-gari, wato na’ura ta musamman mai zaman kanta, wacce aka kera don sarrafawa da kuma kallo ko mu’amala da bayanan da ke dauke cikin faifan DBD. Wannan ita ce aka fara kerawa a farkon bayyanar faifan DBD, kuma ana jona ta da talabijin ne, don amfani da ita. Wannan nau’I tana iya sarrafa bayanan sauti ne ko bidiyon da ke dauke cikin faifan. Amma duk abin da ya shafi rubutattun bayanai ko wasu manhajoji na kwamfuta da ake iya taskance su cikin faifan DBD, wannan na’ura ba ta iya sarrafa su ko kadan. Wannan, a al’adance, idan ka ji an ce: “DBD Player”, to, ita ake nufi.
Sai nau’in na’urar sarrafa DBD da ke zuwa cikin na’urar kwamfuta. Wannan ake kira: “DBD-ROM”. Kamar “CD-ROM” da ke iya sarrafa faifan CD a kwamfuta, wannan na’ura ita ce ke iya sarrafa faifan DBD a jikin kwamfuta. Ba wai sarrafawa ma kadai ba, tana iya taskance bayanai, ko sauti ko bidiyo a kan faifan DBD sabo, wanda babu komai a cikinsa. Sannan tana iya goge bayanan da ke cikin faifan DBD-RW, wato nau’in faifan DBD da ake iya sabunta bayanai a cikinsa ke nan, sannan ta zuba wasu bayanan. Ko kuma sabunta wadanda ke ciki. Wannan na’ura ba ta tsaya wajen sarrafawa da zuba bayanan sauti da bidiyo da rubutattun bayanai kadai ba, hatta manhajar kwamfuta (Computer Applications) tana iya taskance ta a kan faifan DBD, sannan idan ma aka kawo faifan DBD mai dauke da manhajar kwamfuta, tana iya sarrafa shi don loda wa kwamfutar wannan manhaja da ke ciki. Kamar yadda bayani ya gabata, idan ka ji an ce: “DBD-ROM”, to, wannan na’ura ake nufi.
Sai nau’in na’urar saffara DBD mai zuwa cikin mota. Wannan nau’in na’ura kuma da mota kadai ta kebanta. Ba a iya amfani da ita a kan wata na’urar in dai ba mota ba ce. Sannan ba a iya jona ta da talabijin; a mota kadai ake iya amfani da ita. Kari a kan haka, bayanan sauti da bidiyo kadai take iya sarrafawa. Ba ta iya sarrafa rubutattun bayanai ko faifan DBD mai dauke da manhajar kwamfuta.
Sai na karshe da za mu dakata a kai, wato: “Portable DBD Player”. Ita kuma na’ura ce ta musamman, tafi-da-gidanka, wacce ake amfani da ita wajen sarrafa bayanan faifan DBD ba tare da an bukaci talabijin ko kwamfuta ba. Kuma kana iya sanya ta cikin jaka ka yi tafiya da ita. Bayan haka, kana iya jona mata sifika ta kunne (Earpiece), don sauraren sautin wakoki ko fim din da kake kallo, idan bidiyo ne.
Karko da tsawon rayuwar faifan DBD
A karshe dai, masana sun tabbatar da cewa faifan DBD ya dara faifan CD karko da juriya da ma tsawon rayuwa. A cikin wani bincike na musamman da aka gudanar, sakamako ya tabbatar da cewa faya-fayen DBD da DBD-R da DBD+R na daukar shekara 30 zuwa 100 ana amfani da su, wadanda suka danganci sauti da bidiyo ke nan. Ga nau’in faifan DBD-RW da DBD+RW da kuma DBD-RAM, sakamakon gwajin da aka yi ya nuna suna iya daukar shekara 30 ana amfani da su. Wannan ke tabbatar da karkonsu a kan faifan CD.
A daya bangaren kuma an tabbatar da cewa babban abin da ke dakushe karkon faifan DBD dai shi ne danshi sanadiyyar ruwa ko raba da kuma hasken rana mai kaifi, dawwamamme, wanda ke tasiri wajen rage tagomashin bayanan da ke cikinsa. Idan ka dauke wadannan dalilai, faifan DBD na iya rayuwa muddin za a samu na’urar da za ta sarrafa bayanan da ke cikinsa, ba tare da wata matsala ba.