Tsarin raba tallafin N8,000 yaudara ce — Uba Sani

Idan aka tafi a kan haka, mutanen Arewa maso Yamma ba za su samu komai ba.

Tsarin raba tallafin N8,000 yaudara ce — Uba Sani

Sanata Uba Sani

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya soki tsarin raba tallafin N8,000 da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ga matalauta domin rage musu radadi.

Gwamnan ya bayyana tsarin tura wa wadanda za su ci moriyar tallafin ta asusun ajiyar banki a matsayin yaudara.

A wata hira da Gwamna Sani Uba ya yi da gidan Talabijin na Arise, ya bayyana cewa babu wani tabbataccen kundin bayanai da zai iya kayyade takaimaiman adadin ’yan Najeriyar da suka cancanci cin moriyar tallafin.

Haka kuma, gwamnan ya ce muddin aka tafi a kan wannan tsari, to kuwa kashi 70 zuwa da 75 na mutanen karkara musamman a Arewa maso Yamma sai dai su ji kawai ana yi.

“Mutanen da ba sa amfani da asusun ajiya na banki, saboda haka ta wace hanya za a tura musu kudin tallafin da ake ikirarin za a raba.”

Tuni dai Shugaba Tinubu ya jingine shirin bayar da tallafin wanda za a raba wa iyalai matalauta miliyan 12 domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Tun kafin a je ko’ina ne dai ’yan Najeriya suka soma sukar tsarin, lamarin da ya tilasta wa Shugaba Tinubu jingine shi da cewar za a yi nazari domin yi masa garambawul.

Sai dai kuma a nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce tallafin N8,000 zai biya wa iyalai da dama bukatunsu.

Da yake zantawa da Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, Gwamna Sule ya ce Naira dubu takwas kudi ne masu yawan gaske ga iyalai da dama da ba sa iya samun wannan adadi a wata guda.

Ya yi tsokaci kan yadda gwamnatin da ta shude ta rika rabawa iyalai tallafin N5,000, lamarin da ya ce yunkurin da gwamnatin yanzu ta jingine na raba N8,000 abun ma a yaba ne.

“Na yarda cewa akwai wadanda suke ganin N8,000 ba wasu kudade ba ne da suka taka kara suka karya, amma duk da haka a wurin wasu iyalan da ke cikin talauci kudin zai yi musu rana nesa ba kusa ba.”

Majalisar Tattalin Arzikin ta shimfida sabbin matakai

Majalisar Kula da Tattalin Arziki ta Najeriya (NEC) ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta dauka don samar wa ‘yan kasar saukin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a karshen taron wata-wata da ta yi a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.

Taron na tsawon kimanin sa’a shida ya fi mayar da hankali a kan batutuwa guda biyu da suka fi tasiri wajen jefa ‘yan kasar cikin mawuyacin hali — janye tallafin mai da kuma karyewar darajar naira.

Bayan tafka muhawara da musayar yawu, taron ya amince da daukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ‘yan Najeriya musamman mafi ya rauni daga cikin halin da suka shiga.

Daga ciki akwai bukatar kowacce jihar ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sauki ko dai ta hanyar raba tallafin kudi ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka ma an amince da bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin kudi a kan albashinsu, tsawon wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan basukan da suke bi.

Wadannan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar kudin da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin kudi.

Bugu da kari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya makamashin da ababen hawa suka fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in iskar gas da ake kira CNG a takaice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.

Jihohin kasar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja