Tsarin sadarwar wayar iska (Wireless Communication) (2)
Tasirin Tsarin “GSM”Tasirin fasahar sadarwa ta “GSM” a wannan kasa tamu abu ne da kowa ke iya sheda shi. Gamammiyar tasirin wannan fasaha na kunshe ne cikin sadarwa, wanda ya kunshi dalilai da hanyoyi daban-daban. Sadar da zumunci tsakanin mutane ya yawaita, wanda samuwar wannan a cikin kowace al’umma, alheri ne. Mutane da dama sun […]
Tasirin Tsarin “GSM”
Tasirin fasahar sadarwa ta “GSM” a wannan kasa tamu abu ne da kowa ke iya sheda shi. Gamammiyar tasirin wannan fasaha na kunshe ne cikin sadarwa, wanda ya kunshi dalilai da hanyoyi daban-daban. Sadar da zumunci tsakanin mutane ya yawaita, wanda samuwar wannan a cikin kowace al’umma, alheri ne. Mutane da dama sun samu hanyar mika gaishe-gaishensu ga ‘yan uwa da abokan arzuka dake nesa, wanda wannan bai samuwa ta dadi kafin zuwan wannan tsari, sam ko kadan. Har wa yau, samuwar wannan fasaha ta “GSM” ta taimaka ma masu kasuwanci ta hanyoyi da dama. Wasu ma ba su da ofis, sam, ta hanyar lambar wayarsu za ka same su, ku yi magana, har ku hadu su maka abin da kake son a yi maka. Ga wasu kuma wannan fasaha ta samar musu sana’a tsayayye, wanda kafin zuwansa ba su taba mafarkinsa ba. Za ka samu mutum ya gama makaranta, ga shedar karatun ga komai, amma ba shi da aiki. Zuwan tsarin “GSM” ke da wuya sai sana’a ta samu. Idan muka koma kan addini, sai mu ga kusan kowa (musulmai musamman) ya zama mai da’awa, musamman ma cikin watan azumi. Wannan ya fi yaduwa ta hanyar sakonnin tes, kuma hakan abu ne mai kyau, don ya takaita wa malamai aiki sosai, ta wani bangaren fa amma. Wasu kuma hanyar yada manufa da furofaganda kawai suka samu. Idan ana son aibanta wani ko wata al’umma ko wani, sai kawai a tsara sakon tes mai zaki ko daci, iya gwargwadon batanci ko tallan da ake son yi, a ci gaba da yadawa. Ana cikin haka kuma sai ga wayoyin salula na zamani masu suna: “Smartphone,” masu dauke da manhajojin sadarwa na sada zumunta bila-adadin. Masarrafai irin su: Facebook, da Whatsapp, da Hulu, da Instagram, da Twitter, duk sun dada taimakawa wajen kara samar da sanayya da wayewa da birgewa da kuma botsarewa ta wata hanyar.
Wannan hanya na da tasiri sosai, domin ba sai ka kira mutum ba, balle ya ki amsa kiranka; da zarar sakon ya iso wayarsa shikenan, sai in gogewa zai yi, wanda kuma dole ne ya bude ya karanta abin dake ciki.
Ga wasu kuma wannan hanya ta sawwake musu hanyar karfafa sana’ar samartakan dake tsakaninsu da ‘yan matansu. Wasu sun yi ‘yan mata ta wannan hanya, wasu sun karfafa alakarsu da mata ko ’yan matansu, musamman ma ta hanyar tsarin dtracool da kamfanin MTN ke bayarwa cikin dare. Sauran kamfanonin waya su ma suka bi sahu: Glo da nata tsarin; Airtel da nata tsarin; Etisalat ma haka. Kowa na kokarin burge masu hulda da shi. Da abin ya yi nisa ma, har kyautar “Data” ma ake bayarwa, da kyautar katin waya. Abin mamaki!
Ga wasu kuma, kwarewa suka samu wajen fasahar gyaran wayar salula, cikin sauki. Da dama sun dauki wannan a matsayin sana’a ce da suke cin abinci ta hanyarta. Akwai wasu hanyoyi har wa yau da wasu suka kirkira wajen caja wayoyinsu, musamman fulanin dake rugage, kuma masu amfani da wayar salula. Cikin shekarar 2007 wani abokina ke ba ni labari cewa kasancewar ba su da wutar lantarki, sai su samu fitilar hannu (torchlight), masu batura bibbiyu, guda biyu, sai su cire kawunansu duka, su sanya wayoyi a daidai inda ake sa kwan lantarkin (globe). Daga nan sai su hade fitilun daga baya, su daure su ta yadda zai zama fitila guda, mai kawuna biyu, batura hudu. Wayoyin dake kan kowanne za su dauka su hade su biyu, don samun baki guda, wanda shi za su dofana a saman batirin wayar salula ko kuma su samu na’urar cajin waya (charger), su yanke kanta, don hadawa da kan wayar dake jikin fitilun, don caja wayar su. Wannan fasaha ce abin alfahari, wanda ke nuna kwazon dan Adam wajen samo wa kansa mafita a yayin da ya samu kansa cikin matsala ko rashi.
Kada mu shagala, daga cikin tasirin da amfani da fasahar “GSM” ta hukunta wa al’umma, akwai iya rubutu da karatu. Akwai da dama cikin mutane da na sani, wadanda ko dai ba su iya rubutu da karatu cikin harshen Hausa ko turanci ba kafin su fara mu’amala da wayar salula, ko kuma ba su iya takaita rubutu da kuma iya karanta takaitattun rubutu ba (shorthand), kafin haka. Amma a halin yanzu duk sun iya, saboda tsananin shakuwa da wannan fasaha. To duk bayan wannan, sai me?
Akasi…
Sai harkar shashanci da wasu suka mayar da wannan fasaha a matsayin wasila. Wasu kuma ba abin da ya fi musu sauki sai su sace maka wayar salularka, ko dai su sayar a arahar wulakanci, ko kuma su la’anta maka ita. Sace-sacen wayoyin salula ba wani abu ba ne boyayye. Wahalarsa kawai a ce ba ka ajiye galala ba. Yanzu sai wani ya gyara wa wayar zama, ba ruwansa. Wasu kuma zamba-cikin-aminci kawai suka iya, wato 419. Za su yi kirdadon lambobin wayoyin jama’a, idan suka dace, sai su buga maka su ce akwai wata ‘yar harkalla mai maiko. Idan ka bi tasu kuma shikenan. Wasu kuma su aiko maka da sakonnin tes, cewa ka ci gasar tambola ko kacici-kacici da aka yi lokaci kaza. Idan kana son karbar la’adarka, ka aiko da katin waya na Naira kaza, ka zo waje kaza, lokaci kaza, a rana kaza, don karba. Idan ka bi tasu, wankin hula sai ya kai ka asuba, ba ma dare ba. Cikin shekarar 2014, cikin watan azumi, na gama shiri da safe zan fita zuwa Kaduna don ziyarar aiki, sai na ji sakon tes ya shiga wayata. Ina dubawa sai na ga wani ne ya turo mini cewa, muddin ina son zaman lafiya, in tura masa katin waya na Naira dubu goma sha-hudu (N14,000), in kuwa ba haka ba, za su zo har gidana su kashe ni. Da na yi kokarin kiran layin sai na ji ba ya shiga; layi ne irin na karba da aika sakon tes kadai, ba a iya kira. Daga nan na tunkuda wa jami’an tsaro lambar; ban san yadda suka kare da su ba. A takaice dai, wannan hanya ta fasahar sadarwa ta GSM ta kawo sauyi mai dimbin yawa cikin al’umma.
Yanayin Sadarwa (Network)
Bayan samuwar hanyar dake daukar sakonni daga tashar sadarwa zuwa wata tasha, sai kuma yanayin dake bayar da wannan dama, wato Network. Wannan yanayi na samuwa ne ta hanyar kayayyakin fasahar dake sawwake wannan sadarwa, wanda ya kunshi na kamfanin sadarwa da kuma wanda mai son sadarwar ke da shi. Wadannan na’urori ko kayayyakin fasaha su za su sheda wayar salular dake neman sadarwa, su tabbatar cewa mai kyau ce, wacce aka kera da dukkan ka’idojin da aka amince da su a duniya da sauran bayanai. Kafin kowane irin nau’in sadarwa ya yiwu tsakanin mutane biyu, ko bangarori biyu, ana bukatar abubuwa kamar takwas da za su yi mu’amala da juna a lokaci guda, wajen isar da wannan sako.
Za mu cigaba