‘Tsarin shiyya-shiyya barazana ce ga cin gashin-kan Majalisa’

Tun komawa mulkin dimokuradiyya a 1999, shugabannin tare da hadin gwiwar jam’iyyunsu na siyasa.

‘Tsarin shiyya-shiyya barazana ce ga cin gashin-kan Majalisa’

Samar da tsarin shiyya-shiyya da Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar a baya-bayan nan a shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa na ci gaba da tayar da kura duk da cewa ’yan takara da wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a na ganin cewa, an yi wa harkokin majalisar katsalandan, wanda hakan bai dace ba.

A ranar Litinin din mako jiya ne Jam’iyyar APC ta bayyana sunayen wasu ’yan takarar da ta fi so a shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai ta 10, wanda za a rantsar da su a watan gobe.

Jerin sunayen ya kunshi sunayen ’yan majalisar da aka ce zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da su.

A bisa wannan tsarin an zabi Sanata Godswill Akpabio daga Kudu maso Kudu (Akwa-Ibom) da Sanata Barau Jibrin daga Arewa maso Yamma (Kano) a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakinsa.

A Majalisar Wakilai kuma jam’iyyar ta amince da Tajuddeen Abass daga Arewa maso Yamma (Kaduna) da Benjamin Kalu daga Kudu maso Gabas (Abiya) a matsayin Shugaba da Mataimaki.

Kodayake an bayyana tsarin a matsayin shawara ce kawai, manazarta sun ce matakin na neman dora ’yan takara a majalisar da ke zaman wani bangare mai cin gashin kansa bai dace ba.

Bayyana sunayen wadannan ’yan takara an ce wani mataki ne da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka tsara, domin bukatar kansu.

Tun komawa mulkin dimokuradiyya a 1999, shugabannin tare da hadin gwiwar jam’iyyunsu na siyasa, sukan amince da zabar wasu shafaffu da mai a matsayin shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa domin tabbatar da kyakkyawar alaka a tsakanin bangarorin biyu. Shugaban Kasa kan yi amfani da ikonsa wajen tabbatar da cewa, ’yan takarar da ya fi so sun fito, kuma a mafi yawan lokuta su ne ke samun nasara.

Sai dai manazarta sun sha yin Allahwadai da irin wannan al’ada da cewa ta saba tsarin dimokuradiyya ne, kuma tana jawo matukar koma-baya ga cin gashin-kan majalisar.

Ba dimokuradiyya ba ce – Kalu, Yari ’Yan takarar shugabancin Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu da Abdul’aziz Yari da Sanata Sani Musa, sun nuna rashin amincewa da tsarin rabon, inda suka bayyana matakin da jam’iyyar ta dauka a matsayin wanda bai dace da dimokuradiyya ba.

Kalu, wanda shi ne Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa ya ce ba zai amince da matakin da jam’iyyar ta dauka ba. Kalu ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, inda ya ce tsarin da jam’iyyar ta dauka na sanya sunayen ’yan majalisar da ta fi so a matsayin shugabannin jam’iyyar ya saba wa tsarin mulkin kasa, kuma bai dace da tsarin dimokuradiyya ba.

A nasa bangaren, Yari ya bukaci jam’iyyar ta sake duba hukuncin da kuma gyara kurakuran da aka yi tun kafin zaben 2027.

Zababbun sanatoci daga Arewa ta Tsakiya a wata budaddiyar wasika da suka aike wa Shugaban Jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Adamu sun yi watsi da cire shiyyarsu daga cikin tsarin da aka yi a yanzu duk da gudunmawar da suka ba jam’iyyar a lokacin zaben Shugaban Kasa.

“Mu a matsayinmu na jiga-jigan jam’iyyar muna kira ga Jam’iyyar APC ta gaggauta janye hukuncin da ta yanke a baya, wanda ya fitar da shiryarmu daga tsarin raba madafun iko a kasar nan, tare da mika mukamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ga shiyyar Arewa ta Tsakiya domin tabbatar da adalci.

Za mu yi watsi da tsarin – Kawu Zababben Sanatan Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar NNPP, Alhaji Kawu Sumaila ya ba da tabbacin cewa abokan aikinsa za su bijire wa dora ’yan takara a kan ’yan majalisar.

Ya yi nuni da cewa, majalisar a matsayinta na wani bangaren gwamnati mai cin gashin kai, kamata ya yi ta kasance mai cin gashin kanta ta kuma kubuta daga hannun Bangaren Zartarwa.

Kokari ne na mai da majalisar ’yar amshin Shata – Kungiyoyi Wasu kungiyoyin fararen hula sun bukaci zababbun ’yan Majalisar Dokokin su tabbatar da ’yancin kansu a matsayinsu na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa don kauce wa zama ’yan amshin Shata kawai.

Malam Auwal Musa Rafsanjani, Babban Daraktan Cibiyar Bayar da Shawarwari ta CISLAC ya ce, matakin da zababben Shugaban Kasa da Jam’iyyar APC suka dauka na dora wa ’yan majalisar shugabannni wani yunkuri ne na jefa majalisar a aljihunsu.

A hirarsa da Aminiya, Malam Auwal ya ce, wannan dabi’a ta rashin bin tsarin dimokuradiyya ta dora dan takara na da illoli da dama.

Daraktan Cibiyar Kula da Dokoki ta Afirka, Dokta Sam Oguche ya ce, ya kamata a bar Majalisar Dokoki ta Kasa a matsayinta na bangare mai cin gashinkansa ta yanke shawara kan harkokinta ba tare da katsalandan ba.

Ya bukaci ’yan majalisar da aka zaba su tabbatar da ’yancin kansu su yi abin da ya dace.

Cibiyar Tabbatar da Gaskiya da Wayar da Kan Jama’a ta bukaci zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da Jam’iyyar APC su daina tsoma baki a harkokin shugabancin Majalisar ta 10.

Shugaban Cibiyar, Dokta Nwambu Gabriel ya yi Allah-wadai da matakin da Jam’iyyar APC da wasu masu ruwa-datsaki suka dauka na kakaba shugabanni a kan Majalisar ta 10.

Sai dai Shugaban Jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya ce, jam’iyyar na son a gudanar da zaben shugabannin Majalisar ta 10 mai zuwa ba tare da magudi ba, yana mai bayanin cewa duk da amincewar kowane dan takara dole ne a gudanar da zabe, domin ’yan majalisar su yanke wa kansu shawara.

Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne lokacin da ’yan takarar shugabancin majalisar da jam’iyyar ta nuna tana so, Godswill Akpabio da Mataimakinsa Barau Jibrin suka kai masa ziyara a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya gargadi ’yan majalisar na Jam’iyyar APC da kada su kuskura su zo zauren majalisar a makare a ranar gudanar da zaben shugabannin majalisar, domin su samu damar fitowa su kada kur’arsu, don gudun kauce wa maimaita irin abin da ya faru a baya.

Sanata Adamu ya ce, “Za mu jira har zuwa ranar 3 ga Yuni, inda za mu hadu a zauren majalisar. Ina so a yi zabe ba tare da magudi ba, domin koda kowa ya ce Akpabio ne ko Y ko Z dokar ita ce dole ne a yi zabe.

“Wadanda ke Majalisar Dattawa sun san ka’idojin. A wannan ranar ce Shugaba da Akawun Majalisa za su shelanta yin zabe.

Don haka, ina fata tare da yin addu’ar mu ne da nasara a wannan rana kuma za mu yi nasara.

Amma bari in yi muku gargadi, kada ku sake ku makara wajen shigowa majalisa a kan lokaci, domin muhimmancin wannan rana.

Ina fata na isar da sako,” in ji Sanata Adamu A makon jiya ne Alhaji Abdullahi Adamu ya karbi bakunci ’yan takarar shugabancin Majalisar Dattawa da ta Wakilai, wadanda suka ziyarci Sakatariyar Jam’iyyar ta Kasa a ranaku daban-daban domin gabatar da korafe-korafensu kan tsarin da jam’iyyar ta yi na raba mukaman manyan ofisoshin Majalisa ta 10 ga shiyya-shiyya.