Tsarin siyasar Amurka ya yi wa Najeriya muguwar tsada – Bisi Akande
Tsohon Shugaban riko na Jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande ya ce tsarin Shugaba Mai cikakken Iko da Najeriya take gudanarwa ba zai iya kawo mata ci gaba ko bunkasa ba. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Bisi Akande yana fadin haka ne a lokacin da yake jawabi ga taron manema a garinsu Ila […]

Tsohon Shugaban riko na Jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande ya ce tsarin Shugaba Mai cikakken Iko da Najeriya take gudanarwa ba zai iya kawo mata ci gaba ko bunkasa ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Bisi Akande yana fadin haka ne a lokacin da yake jawabi ga taron manema a garinsu Ila da ke Jihar Osun a wani bangare na bikin cikarsa shekara 79 a duniya.
Ya ce, tsarin dimokuradiyyar na majalisa mai dauke da jam’iyyu irin na Ingila ne ya fi dacewa da tafiyar da Najeriya, idan tana so ta kamo sauran kasashen da suka ci gaba.
Cif Akande, wanda tsohon Gwamna ne, ya ce dimokuradiyyar Amurka na jam’iyyu da dama da Shugaban kasa mai cikakken iko tana cike da matsaloli da kuma muguwar tsada ga kasa mai cike da mutanen da suke fama da talauci da rashin ilimi irin Najeriya.
Ya ce, Najeriya a matsayinta ta kasa a yanzu haka tana tafiyar da gwamnatin mai wahala a karkashin wani tsari marar aiki.
“Shugaban kasa Buhari abokina ne, kuma ina fatan ya samu nasara, amma yana tafiyar da wani tsarin gwamnatin mai wahalar sha’ani. Dimokuradiyyar Najeriya wata dimokuradiyya ce ta sojoji ta rabon mukamai, kuma idan muka ci gaba a irin haka babu ta yadda za a yi mu samu nasara,” inji Akande.
Ya kara da cewa: “Har zuwa wannan lokaci, shaidun da suka ginu a kan nazari sun nuna tsarin dimokuradiyya na majalisa irin na Ingila shi ne tsarin gwamnatin da ya fi tabbatar da gaskiya da rikon amana a daukacin duniya.”
Ya ce tsarin dimokuradiyya irin na majalisa ya taimaka wa kasashe irin su Ingila su samu wadata da daidaituwar al’amura da martaba a idanun duniya, kuma ya taimaka wa jaririyar kasa irin Isra’ila ta zama mai karfin tattalin arziki da na soji.