Tsarin Sufuri: Gwamnatin Kano da kamfanin Stata sun ƙulla yarjejeniya
Kamfanin ya shirya samar da tashoshin CNG guda shida a Kano.

Gwamnatin Jihar Kano, ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Stata Logistics Limited domin kafa sabon tsarin sufuri na zamani da za a dogara da amfani da CNG (Compressed Natural Gas) a jihar.
A taron da aka gudanar a Ma’aikatar Sufuri ta Kano, Daraktan Kamfanin Stata Logistics, Chuks Nwani, ya bayyana cewa shirin zai rage cunkoson ababen hawa a titunan Kano.
- Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6
- An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna
Hakan zai samu ne ta hanyar maye gurbin ƙananan motoci da sabbin bas-bas na zamani masu amfani da CNG.
Waɗannan bas-bas za su iya ɗaukar fasinjoji da kashi 120 sama da motocin sufuri na yanzu, wanda zai samar da tafiya mai sauƙi, aminci, da arha ga al’ummar Kano.
“Burinmu shi ne inganta sufuri a Kano ta hanyar amfani da CNG, wanda zai rage tsadar tafiye-tafiye da kuma saurin isa inda ake so idan aka kwatanta da tsarin yanzu,” in ji Nwani.
Sabbin Bas-Bas da Sabbin Tashoshin CNG
A wani ɓangare na shirin, kamfanin Stata Logistics zai gina tashoshin CNG guda shida a Kano don tabbatar da wadataccen gas ga motocin sufuri.
Haka nan, za a fara da saka jarin bas-bas 135, kowane na da darajar kusan dala 140,000, wanda gaba ɗaya zai kai dala miliyan 25.
“Muna buƙatar goyon bayan gwamnati ta hanyar samar da manufofin da za su tabbatar da nasarar wannan shiri, domin al’umma su amfana da tsarin sufuri na zamani,” in ji Nwani.
Goyon Bayan Gwamnatin Kano
Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yaba da shirin, wanda ya dace da sabuwar dokar Kano Metropolitan Agency (KAMATA), wacce aka kafa domin tsara sufuri a Kano.
“Sun gabatar da kyakkyawan shiri don inganta sufuri a Kano, kuma mun ba su damar ci gaba da shirye-shiryen da suka dace.
“Bayan sun kammala, za mu gabatar da shirin ga Mai Girma Gwamna domin tantancewa,” in ji Namadi.
Ya ƙara da cewa yana da yaƙinin cewa wannan tsarin zai kawo ci gaba mai yawa, inda ya kafa misali da Jihar Legas a matsayin abin koyi a fannin gyaran tsarin sufuri na birane.
“Wannan ci gaba ne mai muhimmanci. Idan aka aiwatar da shi cikin nasara, Kano za ta zama birni na biyu mafi girma a Najeriya da ke da irin wannan tsarin sufuri na zamani,” in ji shi.