Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (1)
Matashiya Idan masu karatu ba su manta ba, a baya mun fara bayani kan tekunan duniya da irin abubuwan da ke cikinsu (ko karkashinsu), inda muka yi bayani kan tekun Pacific, wanda shi ne babba, mafi fadi da girma a duniya. Bayan tekun Pacific mun fara bayanai kan teku na biyu da ke biye da […]
Matashiya
Idan masu karatu ba su manta ba, a baya mun fara bayani kan tekunan duniya da irin abubuwan da ke cikinsu (ko karkashinsu), inda muka yi bayani kan tekun Pacific, wanda shi ne babba, mafi fadi da girma a duniya. Bayan tekun Pacific mun fara bayanai kan teku na biyu da ke biye da shi, wato tekun Atlantika, ko “Tekun Legas,” kamar yadda muka saba kiransu a Najeriya. A karkashin wannan gaba dai mun gabatar da kasidu guda biyu.
Na farko kan asali da samuwar tekun Atlantika, inda muka duba bangaren tarihi da kuma bagiren da wannan teku yake a duniya. Sannan a karshe muka sanar da mai karatu cewa Turawa sun dade suna gudanar da bincike na kimiyya kan sha’anin teku a wannan bagire tun sama da shekaru dari da suka gabata. A kasida ta biyu kuma mun jero bayanai ne kan tarihin tafiye-tafiyen bude ido da burgewa da Turawa suka yi ta yi, har zuwa wannan karni da muke ciki. A yau cikin yardar Allah, ga shi mun dawo don ci gaba da bayani kan tekun Atlantika. Za kuma mu dubi tasirin wannan teku ne wajen ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya da kuma sadarwa.
Tasiri Wajen Tattalin Arzikin kasa
Kamar yadda bayanai suka gabata, tekun Atlantika babban teku ne. Shi ne na biyu a duniya, sannan ya hada alaka tsakanin manyan nahiyoyin duniya guda uku; nahiyar Amurka (Kudanci da Yammaci) ta bangaren yammacinsa. Sai nahiyar Afirka daga bangaren Arewaci. Nahiyar Afirka na daga cikin nahiyoyin da suka fi yawan jama’a a duniya. Sai kuma nahiyar Asiya ta gabashinsa, inda ya jonu da tekun Indiya (Bahar Maliya) daga gabas, ya nausa can don hadewa da shi.
Wannan gamayyar manyan nahiyoyin duniya da tekun Atlantika ya hada ya taimaka wajen saukake hanyoyin kasuwanci a tsakanin kasashen duniya. Tekun Atlantika wani babban titi ne na kasuwanci, inda manyan jiragen ruwa ke dauko dukiyoyin kasuwanci da hajoji nau’uka daban-daban daga nahiyar Amurka zuwa Afirka. Haka ma sukan dauko kayayyaki daga nahiyar Amurka zuwa nahiyar Asiya, kai tsaye ko ta hanyar yin Zango a nahiyar Afirka. Bayan wannan, har wa yau jiragen kasuwanci kan taso daga nahiyar Amurkan dai zuwa nahiyar Turai; musamman masu tasowa daga bangaren Latin Amerika (Kudancin Amurka – South America).
A daya bangaren kuma, jiragen ruwan kasuwanci kan nausa daga nahiyar Afirka zuwa nahiyar Asiya, daga can kusa karasa Turai, ta hanyar maliya da ke sada su da tekun Pacific. A wasu lokuta kuma akwai masu tashi daga Afirka zuwa nahiyar Amurka kai tsaye, don kaiwa da daukowa ko kaiwa da dawowa; ya danganci abin da ya sawwaka.
Wannan jele da jiragen ruwan kasuwanci ke yi tsakanin wadannan nahiyoyin duniya ta cikin tekun Atlantika ya taimaka gaya wajen habaka dangantakar kasuwanci tsakanin ma’abota wadannan wurare. Wannan kuma, a Turance, shi ake kira: “Transatlantic Trade,” a zamanin yau. Akwai tashoshin jiragen ruwa a dukkan kasashen da ke gaba da wannan teku a duniya baki daya; tsakanin Afirka, da Asiya, da kuma nahiyar Amurka.
A karkashin wannan teku mai albarka, akwai tarin albarkatun kasa irin su Man Fetur da ke makare cikin curarrun duwatsun da ke karkashin tekun. Akwai sinadaran Gas, da duwatsun gini da kuma duwatsun alfarma a jibge a karkashin wannan muhalli. Bayan wadannan, an gano tarin duwatsun zinare a nisan zurfin da bai shige mil daya ba, a karkashin tekun. Bincike ya nuna cewa, gano hanyoyin zakulo wadannan duwatsun zinare a halin yanzu ba abu ba ne mai sauki, idan an yi la’akari da yanayin muhallin. Sai dai nan gaba.
Bayan haka, tekun Atlantika ne ke dauke da albarkatun kifi mafi girma a duniya; fiye da tekun Pacific ma. Wuraren da suka fi kowane tarin wannan nau’in albarkar kifaye su ne: bakin tsibirin Newfoundland da Dogger Bank da ke kasar Scotland, sai Georges Bank na kasar Amurka, da kuma tsibirin Bahamas.
Tasiri Wajen Sadarwa
Masu karatu za su yi mamakin jin cewa tekun Atlantika wata matattara ce da ke dauke da hanyoyin sadarwa. Kusan dukkan manyan kamfanonin sadarwa na duniya, da gidajen yanar sadarwa na duniya, da gwamnatocin kasashe daban-daban (ta hanyar kamfanoni hukumominsu), sun binne wayoyin sadarwa nau’in “Fiber Optics,” wanda hadakar waya ce, amma a yanayin gilashi, mai daukar siginar bayanan sadarwa na zamani cikin mafi saurin yanayi da girma.
A halin yanzu an kiyasta cewa, kashi 95 cikin 100 na a kalla na hanyoyin sadarwa na zamani suna amfani ne da wayoyin sadarwa na “Fiber Optics” ta karkashin teku, don aiwatar da sadarwa. A yayin da ragowar ke amfani da tsarin sadarwa ta wayar-iska (Wireless). Wannan ya faru ne saboda ingancinsa da kuma sauri wajen aikawa da sakonnin bayanai na zamani. A yayin tsarin hanyar aikawa da sakonni ta wayar-iska ke daukar mizanin bayanai biliyan daya cikin dakika guda (1GB per second), tsarin aikawa da sakonni ta wayar “Fiber Optics” na daukar mizani tiriliyon daya ne a duk dakika guda (1Terabyte per second). Wacce alakar ce wannan da tekun Atlantika?
Alakar ta samo asali ne saboda mahalli. Ma’ana, kusan dukkan madaukan wadannan bayanai suna biyowa ta cikin wasu wayoyi na sadarwa da aka shimfide su a karkashin tekunan duniya, ciki har da tekun Atlantika. Sai dai ba yau abin ya fara ba.
Yunkurin farko da aka fara yi wajen shimfide wayoyin sadarwa a karkashin teku dai ya faro ne tun cikin shekarar 1850s. Malaman tarihi suka ce a lokacin ne aka fara shimfida wayoyi masu dauke da siginar sadarwa don amfani da na’urar “Telegraph.” Hakan ne ya saukake tare da bayar da damar karba da iya aika sakonni tsakanin nahiyoyin duniya masu dauke da wannan na’ura. Duk da cewa a lokacin kusan kasashen yammacin duniya ne kadai ke mallakar wannan na’ura ta “Telegraph,” to amma ganin cewa suna mulkin mallaka a lokacin, kuma hukumominsu sun yadu tsakanin tsakiya zuwa gabashin duniya da kuma nahiyar Afirka, sai suka yi wannan kokari don samun damar aikawa da sakonni cikin gaggawa daga kasashensu zuwa inda suke mulkin mallaka ko akasin hakan.
Sai yunkuri na biyu, wanda ya samu bayan gushewar na’urar “Telegraph,” sanadiyyar samuwar na’urar wayar tangaraho. Shi ma ya haddasa shimfide wayoyin sadarwa masu dauke da siginar rediyo don daukar murya daga wata nahiya zuwa wata. Daidai wannan lokaci dai duniyar ta fara gamewa a fannin sadarwa, sanadiyyar yaduwar wayoyin tangaraho irin na zaman baya (Analog).